9/3/2017 4:33pm *Muneerat*✍
*JININ JIKINA*
_*101-105*_
NA *NEERATLURV*😍
_based on fiction and love tale story_
_Dedicated to aunty sis_
*PERFECT WRITERS FORUM*
(P.W.F)_*A gurguje pls reders am sorry for the late post abubuwane suka shigemin gaba kuyi hakuri da yadda novel din zai kasance I love y'all *_#one love 💕
**
FARIS zaune gaban kanin mahaifinsa Usman duk ya korowa kawunsa bayanin komai game da son auren faty daya ke son yi dakuma yadda suka kaya dasu , kawu usman yaji jawabansa yakuma tambayesa kan yana son karin auren dawata manufa koko matarsa ce tamasa wani abin?,Kamar yadda yafadawa Dad yanason karin auren ne sabida cika sunnah kuma yana sha'awan yin mata Biyu haka yadafadawa Shiva kawun. Kawu yace toh masha Allah idan dai dan wannan ne zaiyiwa Dad magana,gdy FARIS yashiga jerowa kawu yasan idan dai kawu yawa dad m.agana zai iya amincewa shiko idan akamai haka angama masa komai na Rayuwa.
Kawu yace gdy ya isa ai yiwa kaine kuma FARIS ai kai dana ne kaima karkaji komai kaji. Toh yace kawune ya umarcesa da yatashi yatafi shima zasa wani gun yanxu daganan yawuce wajen dad din."
'farinciki ne ko murna duk FARIS na ciki yana driving yana..murmushi harda bude wakar backstreet boys yana marming din wakarsu ta _I want it that way_ har ya isa gida.""Faty da kawarta meemah yau sundau hanyar kauyen bebeji sabida itafa faty haka kawai take jin bata aminta da abinda FARIS ke fadamata game da maganar aurensuba gani take kamar karya yake mata idan yace wai aiki ne yawa dad yawa, shiyasa ta fadawa meemah su koma wajen boka share kukanka ko, zaisan *meke faruwa*(cute xarah ce )."
"sun shiga cikin jejin kamar yadda suka saba yau ko tsoro babu tattare da faty, karkashin bishiyan da yake bullowa suka tsaya take sukasoma babbako ashar masu zafi, wata irin iska ce ta kada tana juyawa boka na a samarta yana saukowa kasa take suka jiyo dariyar boka hahahaha yana wani mugun dariya inda iskar ta tsaya shikuma sai gashi zaune yana wannan muguwar dariyarsa hakora duk sun rine gasa baki so irritating idan kungansa fans.
"shegu, marasa imani, hatsababbu abinda boka kefadi kenan wasu faty."
"Sannunku dazuwa yanunamusu waje su zauna, ba musu suka zazzauna, boka yace."
"nasan zaku dawo basai kunfadi mai ke tafe dakuba nasani ansami matsala wajen iyayen yaron wancan karon bamusamu munyi aiki kansuba amma yanxu zamuyi, wata kwarya yaja yakawo gabansa cike da ruwa ya umarci faty da ta matso ba musu ta matso kamar yadda ya bukata wasu yarensa yasoma karantowa wadda ni neerat bansan mai yakefadaba tsiiiiii wasu kibiya biyu suka wuntsilo bakin kwarya atsorace faty ke gwalo idanu tana ganin abin al'ajabi, dariya boka ya bushe da ita yace."
"kinga wannan yanunamata cikin kwaryan waye wannan ya tambaya yana nunamata cikin kwaryan?.
"faty da tacika da mamaki tace."wannan ai mummy ce mahafiyar FARIS tafada maganar na rawa abakinta."
"wannan fa yanunamata dayan."
"Dad ne ai tafada still getting suprise."
"toh yayi kyau inji boka sa'anan yace wadannan suke kawomuku cikasss sabida a halin yanxu sun hana dansu auren ki amma yanxu zanyi maganunsu zuba ido ki gani."
"kibiyar da ya ajiyesu guda biyun yadaga yajefa cikin ruwan take dayan ya sami dad a bakin zuciyarsa dayan kuma yasami mum gefen zuciyarta amma basu kula da hakanba boka yace ."
"kinga wadannan kibiyoyin dana harba musu yasamesu toh aiki yayi yanxu bazasu bijirewa auren kuba tashi ki tafi komai yayi daidai hahhhhhh yasake barkewa da dariya."
"kudi masu yawa ta ajiyemasa cikin kwaryansa ta taso suka kama hanyan fita daga jejin da meemah."
"saida suka fita cikin daji suka shiga cikin mota sun soma shiga gari tukun faty tasoma baywa meemah lbrn abinda ya wakana."**
Dad, mum zaune a falo tare dasu fareeda sun shirya tsabb zasu dauko MUSKAN takusa sauka, suna cikin hirane lokacinda boka ya harbo kibiyoyin kirjinsa ya rike a daidai lokacinda kibiyar ta samesa, mum madai taji abu ya dan tabata amma ba kamar ta dad ba."
"ruwa dad yace humaira ta mikomasa a firij mai sanyi, saida yasha wannan ruwan yadanjin dama -dama yace su taso su tafi batare da yafadamusu abinda yaji bakin zuciyarsa."
"isarsu airport yayi daidai da saukar jirgin su MUSKAN, lokacinda ta fita a jirgin ido tarinka warowa tana dudduba su mum, can nesa ta hangosu lokacin suma sun hangota da gudu ta nufesu hugging din mum tayi tace I miss you so much my mum, I miss you to daughter mum tafada itama, murmushi dad yayi wajen dad ta koma ta kama hannunsa tace i also miss you dad, kanta yashafa yace my daughter I miss you too, ke baki ganmu bane fareeda tafada tana wurgomata harara cikin wasa, sorry my sisters tamatso wajensu hannayensu takamo dukka tace."
"You know i love you all babes kawai ganin dad da mum ne yasa nayi mantuwa ban fara hogging dinkuba, kun hakura ammatas? Murmushi sukayi tare da hugging dinta suna dariya duka."
"da kyar Dad yasasu suka shiga mota, suka kama hanyan gida."
"da isarsu.MUSKAN tawuce daki tawatsa ruwa sukuma sukaje shiryomusu abinci, bata dau lokaciba ta shirya tasamesu a falo dukkansu sukaci abincin suna hira harsuka kammala, koda suka kammala kamar rufe bakinsu dad akayi(kodashike ai rufewan akayi ) ko maganarda sukayi. Niyan sanar da ita sunkasa yi hira kawai sukayi tayi."
"sai kusan bayan sallah'n magriba kawu usman yazo shi gidansu FARIS ya tarar da Dad a gida da fara'arsu suka tarbesa, bayan sun gaggaisa hardasu MUSKAN yake tambaya dama tare suke da FARIS ne? Mum ce tace dashi ai yau tazota ita, yace toh yana da kyau, cewa su MUSKAN yayi subasu waje zasuyi magana da dad, ba musu suka mimmike suka nufi nasu dakin."
"bayan tafiyarsu ne kawu usman ya dubi yayansa da girma ya soma koramasa bayanin yadda sukayi da FARIS yakuma rokarwa FARIS dad yaje sunemasa auren faty tunda sunnah zai cika."
"Ajiyan zuciya dad ya sauke yace ba matsala gobe ma kuwa zasu yanxu zai kira daddyn faty yasanar dashi batun."
"mum dai najinsu amma itama bata jin zata iya hanasu auren, amma can kasar zuciyarta kuma tanajin zafin faruwar haka."
"Gdy kawu usman yawa dad hade da musu sallama ya tafi."
"Cikin mum da dad ba wanda ya yi yunkurin tambayan wani mai dalilin sa na barin ayi auren shiru kawai sukayi duka."
"da kyar dad yayi gaining courage ya dau waya ya kira daddyn faty yasanar dashi abinda yakeso, daddyn faty dayafi kowa murna naganin zai aurar da diyarsa yace ba matsla sai sunzo, nan sukayi sallama."
YOU ARE READING
JININ JIKINA
FanfictionYarinyace marainiya wacce iyayenta suka rasu sakamakon had'arin jirginda sukayi wato itace MUSKAN! Faris dai ya kasance matukin jirgi acan airport suka had'u da mahaifin MUSKAN, sakamakon taimakon da FARIS yawa abban MUSKAN yasa sa son yaron dakuma...