SHURAKH

895 42 2
                                    



*My dedication goes to my magarya, my zuma, my manzon kwaila, my biski Ummie Jafar, don Allah ina cigiyarki 'yar uwa in har Allah yasa kika ga page d'in nan ki tambayi ko wata writer number In Sha Allahu za ki samu.

_Wallah ina sonki my beautiful beb, my natural beauty,  ur ugly lurv u so much dear 😘

12-8-2017

Page Four (4)

Nidai ina tsugunne kaina a kasa inata godia ga Allah da ya bani cikon kuɗin nan domin da bani da shi yau sai kauyen marafa ta mana ihu amma daɗin abin duk wanda ya rike Allah wallahi Allah yana tare dashi.

"Ke bani kuɗina na ce."
       Cewar Malam Tanko sai a lokacin na buɗe hannun da Rukiee ta bani kuɗi, kuɗin da nagani ya firgita ni na kara mutstsike idona don na kara tabbatar da abinda idanuna suka nuna min tabbas shiɗin ne dai dana gani da farko to ina Rukiee ta samu wannan kudin masu yawa ni tunda nake a rayuwata ban taɓa rike wannan kuɗin ba kai ko Ummata bata taɓa rike maƙuden kuɗi nan ba duk da irin ai katau ɗin da Ummata ta yi ban taɓa ganinta da wannan kuɗin da suka kai wannan ba.

"Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un! Ina  Rukiee ta samu wannan kuɗin da ya kai naira ɗari biyar.?"

"Ke ki bani kuɗina kin rike sai faman jujjuya shi kike yi wato ga shashasha ko tun ɗazu inata magana kin maishe ni wawa ni ina zuba kamar kanyar da ba daɗi, hankalinki ma baya kaina to bani kudina ja'irar yarinya mai siffar aljanu."
       Na miƙa mishi ɗari shida sannan na ce harda kuɗin hayar wata biyu tun kafin nagama rufe bakina ya fisge kuɗin inma sata kikayi to inda nasa a aljihu na babu uban da zaisa na cire ko da kuwa hakuma ne. Nidai ina jinsa ne don bakomai nake fahimta ba na tashi haɗe da cewa.

"Sai anjima."
     Ko ta kaina bai bi ba yana ta masifa ni bata shi nake ba jefa kafata kawai nake yi hankalina ya tashi duk fadin garin nan Abban Rukiee ne kawai yake rike ɗari biyar sai ko Malam Tanko, bayan su babu mai rike irin wannan kuɗin to waye zai bata "Ya Ilahi" na faɗa a bayyane wazai ba ni amsoshi na, Rukiee ce zata iya bani amsoshin nan yanzu kuma bazan iya shiga gidan ba saboda yanzu Abba ya fito yana zaune a kofar gida kuma badon kowa yake zaune a gurin ba sai don ni,  saboda baya son gani na tare da Rukiee,  harna karaso kofar gidan yana zaune na tsugunna har kasa na ce

"Abba Ina kwana."
     wanda aka kira da Abba ko inda Shurakh take bai kallah balle yasan Allah yayi ruwan mutum agurin dama ban sa ran zai amsa min ba saboda inda sabo na saba da kyarar da Abba yake min, na tashi na shiga gida na tsaya a zaure na yi kokarin daidaita kaina bana son abin da zai tada hankalin Ummata kuma zata min faɗa inhar na ce Rukiee ce ta ba ni kuɗin da na cika kuɗin haya, da sallama na shiga tana zaune ta zabga uban tagumi gabana yayi mummunar faɗuwa to me zaisa Ummata tagumi da safen nan na ƙara yin sallama amma Ummata bata jiba na karasa da sauri na dafata idona yana shirin zubar da kwalla na ce

"Ummata me yasa me ki? Waye ya taɓa min ke Don Allah Ummata ki faɗa min.?"
     Na karasa maganar cikin kuka, ajiyar zuciya Umma ta yi.

"Bakomai Shurakh kawai ina tunanin yau sauran kwana goma sha biyar saukarku kuma babu abinda na miki ko ankon saukan baki nuna min ba sai dai gani nayi a gurin Rukiee,  kuma ga shi bani da halin yi miki amma bazan cire rai daga rahamar Ubangiji ba yana sane damu kuma shine zai kara rufa mana asiri.!"
     Umma ta goge hawayen da suka zubo mata.

"Ummata ni ban damu da ankon saukar ba ni duk wani abinda ya shafi sauka na riga da na faɗa musu babu abinda zanyi kuma Ummata lafiya yafi komai in Allah ya ƙara yarda damu ya bamu aron rai ai shine babban gata sannan Ummata ki kwantar da hankalinki babu abinda zai gagare Allah sannan yana tare damu saboda mun yi biyayya da abinda  Annabi SAW yace: kar mu yi roko don roko yana kashe zuciya, kuma kinga ai babu gun wanda muke zuwa maula gurin shi sai gurin wanda baya gajiya damu kuma nasan zai bamu don haka ki kwantar da hankalinki Ummata kuma bazamu dauwama a haka ba komai zai wuce bisa umurnin Allah,  Ummata kina yin Istigfarin da na ce ki dinga yawan yikuwa ? Istigfari yana kawo arziki da kara kusanci da Allah."

( Yar Uwa kema ki dage wallahi addu'a baya faɗuwa kasa ba tare da an amsa ba,  karkice kin gaji kina ta yi ba amsa ba dayan biyu ne ko ki tsinta a gaba ko kuma a cikin zuri'arki a samu mai wannan abinda kike nema ɗin fatan mu dai Allah yasa mu dace da rahamar Allah. Amin Ya Allah)

          Ku dai ƙara hakuri labarin ne ya zo da gajajjerun feji.

Basira Sabo Nadabo Ce.

SHURAKH Where stories live. Discover now