🏅🏅🏅🏅
🏅🏅🏅
🏅🏅
🏅
*_SHURAKH_*_Daga alk'alamin 📝 jienie ďaya_
® _By_
_Sis Abeedah Tauhtah 😘_
*Da*
_Basira Sabo Nadabo 😘_
© *_Anielurv Group Writes_* _{AGW}_
Wattpad @ Basira_Nadabo
Sadaukarwa gare ku masoyana Allah yabar zumunci ya kara muku sona da kaunata nima naji ina sonku kamar na baku zuciyata duka ku raba wallahi ina sonku Allah ma shaida ne, wallahi jiya an nuna min cewa sa'kon dana ke son isarwa al'ummah suna fahimta don jiya na amsa wayar mutane wallahi har basa k'irguwa sun min ta'aziya da masu bina private duk nagode kuma naji daďi Allah yabar min ku, kuma Allah yabar muku ni Amin Ya Allah
_Uwar arziki alherinki a gare ni baya karewa wallahi samunki a duniyar nan sai an tona kinyiwa masoyan ki kinyiwa makiya, Allah dai ya kara kare mana ke wallahi Ina son ki, *AUNTY SIS*_
*_Sis Ayusha Iliasu_* _ke ta daban ce kin nuna min akoda yaushe muna tare nima na baki zuciya ta ke ďaya duniya ku shaida na bawa sis Ayusha Iliasu zuciyatay❤ gaba ďaya, Nagode dear kina bani kulawa yadda ya kama ina godiya sosai_ #One Lurv wallahi.
@ Page Seventeen (17)
Falie yar abokin Alh mai naira ne suma suna zaune a G.R.A. Rigasa, Falie ta taso cikin gata gashi babu kwa'ba a tare da itah duk abinda take so shine za'ayi kuma duk abinda tayi dai dai ne bata iya komai daya shafa al'amurar rayuwa ba balle ta shiga kitchen bata san ta gyara gurin kwanciyar ta ba inta tashi babu abinda take gyara mishi zama duk abinda ta ďauka to agurin zata ijiye shi ilimin addini yayi 'karanci tafi bawa boko mahimmanci, Falilah shine asalin sunan ta kuma ita ďaya ce agurin iyayen ta ta samu sunan Falie ne saboda soyayyar da iyayen nata biyu ke nuna mata, hajiya baraka itace mahaifiyar ta kuma duk sangartta a gurinta ya samo asali don itama bata iyaba balle ta koyawa yar tata, Falie ita tafara nuna soyayyar ta ga Adams da taga babu fuska ta samu daddy'nta ta mishi bayani kuma tana son ayi auren kafin azumi to kun san yar gata ce babu abinda take nema ta rasa haka ko akayi cikin kankanin lokaci dubban mutane suka shaida ďaurin auren Adams Abdullahi Mai Naira tare da amaryar sa Falilah Abbas, ďaurin auren da kunshi manyan masu kuďi da sarakuna da manyan yan kwallo wanda kasa suke alfahari dasu, anyi shagulgula kala kala amarya ta tare a gidanta lafiya anyi biki da sati biyu abokan ango sukazo domin cin abincin amarya tana ganin su ta bata rai gaisuwar ma don dole tayi mai makon a kawo musu warmers sai gani nayi an kawo musu cups da drinks shima da kyar tasa aka kawo wai za'a cinye mata abincin gida tun daga ranar Adams ya daina kawo abokanshi gashi ya lura bata iya komai ba ga ďan kwallo da cin abinci kulkun yana zarya tsakanin gidan shi da restaurant a haka kullun suke, kannen shi da yan uwa duk basa zuwa gidan saboda babu tarbar da suke samu ba sakin fuska balle su sami arzikin ruwan da zasu sha suma kannen shi sun daina zuwa gidan babu me zuwa sai yan uwanta da kawaye suma ďin ba barin su tayi ba a haka suke har yau
(hmmm Allah ya kyauta amma ai wannan ba mata bace mai gadi ce tab )
CIGABAN LABARI
Tafe yake a motarsa yar zamani a duk faďin garin kaduna babu wanda na taba gani a irinta sautin wakar Rihanna ft Drake mai taken WORK shine yake tashi sai bin wakar yakeyi kamar shine ya rera wakar badan nasan wanda sukayi wakar ba dana ce babu tantama shine yayi wakar, tafe yake yana faman rausayar kai har yayi gaba naga yaci wani uban birki saka makon abinda ya gani, yace yau da yardan Allah zan cika burina ya sauko a motar yana ta binsu har kowa ya wuce gidan ya rasa yadda zayyi yafi minti ashirin a kofar gidan sai gani yaro ya tambaye shi sunan yarinyar data shiga gidan ya faďa mishi
Yace ina baban ta yake yimin sallama dashi
Tab ai babanta ya mutu innar mu tace wai tun tana karama babanta ya rasu
To zaka iya rakani gurin mai gari
Eh muje nasan gidan
Suka kama hanya yaro sai zuba yakeyi kamar an tambaye shi Adams sai gyaďa kai yakeyi kamar mai jinjina wani al'amari a haka har suka iso gidan me gari ya sallame shi da ďari biyar (500) yaro yana ta murna yasa aka mishi sallama da mai gariMai gari ya fito har ya fara masifa sai kuma ya fara washe baki suka gaisa mai gari yayi mishi iso zuwa fada bayan sun zauna yace Alhaji ban gane ka ba
Yace daman naga wani abune a kauyen ka shine nace bari nazo nasan baifi karfin ka ba
Mai gari ya kara washe baki yace faďi komai Alhaji indai a garin nan ne kona waye zan baka, af kajika da wani zance ai cewa zakayi kana son abu kaza ni kuma nace na baka faďi kawai
Adams ya gyara zama yace daman wata yarinya nagani nake so a aura min amma ba auren daďi bane zan aure tane na gana mata azaba na wulakanta rayuwarta zan hanata jin daďin rayuwa nasa mata ciyo mai karya garkuwan jiki daga karshe na korata
Mai gari ya razana da bayanin shi saboda yaga tsantsan gaskiya a bayanin shi kuma zai aikata abinda ya faďa, yace Alhaji faďa ina jinka
Sunan ta SHURAKH
(😳😳😳 Ya Ilahi duk wannan bala'in akan baiwar Allah Shurakh )
Duk mai son auren Shurakh da Adams naga comment ďinku
Duk mai son auren ta da Kawu shima naga comment ďinku
4 ur comments 07030515774
_{AGW}_
YOU ARE READING
SHURAKH
AdventureShurakh labarin yarinya ce wanda yan uwan babanta suka b'atar da uban ta tun tans ciki, ta tashi cikin wahalar talauci babu mai taimakon su daga itah har mamanta daga karshe reshe ya juya da mujiya kudai ku biyomu don jin ya zata kaya, mun gode. Kar...