SHURAKH

763 35 0
                                    

🏅🏅🏅🏅
🏅🏅🏅
🏅🏅
🏅

*_SHURAKH_*

_Daga alk'alamin 📝 jienie daya_

® _By_

_Sis Abeedah 😘_

*Da*

_Basira Sabo Nadabo 😘_

© *_Anielurv Group Writes_* _{AGW}_

Dedicated to my kunun tsamiya, my zobo, kunun aya, swt ginger wallah ina sonki sosai har bazan iya fadan irin kaunar da nake miki ba amma zance Allah ya had'a a gidan Aljanna My Sweet *_MAMI RUKS_* But You Know That Your Abeedah's LVSM and ICDWU Sweerat 💋

@Page Eight (8)

Wannan bakon naga yaja mota da gudu kamar zai tashi sama _Ikon Allah_ ne kawai ya kaishi gida, horn yakeyi kamar zai rabashi da motar da gudu wani dattijon tsoho ya wangale gate yana barka da zuwa ko kallo bai ishehi ba balle ya amsa masa gaisuwar da yake mishi, kara kallon wannan tsohon mukayi saida bironmu ya kusan faduwa tab Allah yana halitta iri daya don sai da muka kara mutstsike idon kodai Shurakh ce kemin giezo amma bari nayi shuru dai

Da karfi yake buga kofar dakin wata farar mata nagani ta bude kofar tare da mishi sannu da zuwa

Yauwa kawai ya iya ce mata saboda yadda zuciyar shi yake mishi zafi ya haura upstairs ya shiga dakin shi ya fada band'aki ya sakewa kanshi shawa, sautin maganar yarinyar yar kauye yake mishi amsakuwwa a kunnuwar shi ya kaima tiles din dake jikin bangon dakin duka yana cewa zan nuna miki aikin dabbobi da irin jahilcin da nakoya yayi wani mugun dariya daya fada wata magana duk sonjin gulmarmu bamuji me yake fada ba saboda na juya mishi baya ne, ya fito daure da towel da dan karamin towel a hannun sa yana goge sumar kanshi daya sha gyara har da style naga anyiwa sumar irinta zamani ko ince yan kwallo _(Footballer )_ wannan kyaukkyawar matar naga ta shigo dakin tana ta wani kwarkwasa kamar zata balle don salon tafiya

_( oh mu jienie daya muna ganin iyayi a gidajen nutane kowa da tashi salon yangar Sis nima zan koya don na farawa kaina tanaji ke Sis Basira ke dai donni banga abin kallo ga wannan matar ba hmmm sis kenan nidai babu ruwana )_

Tana cewa haba sweery ina maka sannu da zuwa kawani share ni me ya bata maka rai don _Allah_ ka fadamin ko hankalina ya kwanta kaji baby ta fada kamar zatayi kuka

Falie babu abinda yake damuna karki damu ba abinda zaki tada hankali bane ni *_ADAMS_* zanji da komai muje ki bani abinci yunwa nakeji don jina nakeyi kamar anmin satan y'ay'an hanji na Don Allah ki taso mana

Abinci kuma kaima da gangan kake tambaya ta abinci a gidan nan kasan bana abinci kuma ban san yadda akeyi ba yama zan shiga kitchen ai sai kimana ya zube duk na sukurkuce ruwan lipton kawai na iya shima don kace baza ka iya siya bane na lalubo a google

Wani ruwan lipton din da mutun yake sha duk karni gaskiya Falie ki canja halin nan saboda gaba baz......

Gaba kamarya ta katse mai magana oh kishiya zaka min ko don ban'iya girki ba to sai me don kamin kishiya inma don na dinga shiga kitchen ne wallahi ka dade baka min ba kuma bazan shiga ba ko uwar data haifeni bata sani na shiga kitchen ba sai kai to wallahi Adams kaje kayi auren taja tsaki tare da ficewa daga d'akin zuciyarta na kuna

Adams ya dafe kanshi da yake sara mishi wai da wanne zanji ne da cajin da yar kauyen can ta samin ko da rigimar Falie zanji
_(Sai kaba kanka amsa ai )_
Ya bita d'akin ta ya tarar da tana rusa kuka kamar wacce akayi wa mutuwa

Kusa da ita ya zauna yace Falie ni bance zan miki kishiya ba kuma ban miki alk'awarin bazan kara aure ba amma ke kinfi kowa sanin ni bani da ra'ayin zama da mata biyu ko fiye da haka ke kadai kin isheni rayuwar duniya to me yasa kike tada hankalin ki akan abinda kike da tabbacin shi amma kullun akan girki sai munyi fad'a yau shekara biyar (5 year's ) kenan da auren mu kullun akan girki kowa sai yaji kanmu haba Falie na

To am apologize bazan kara ba

Promise?

Ta daga hannun ta sama tace I promise
Mine

_( hmmm mata muna da babban aiki kuwa a gaban mu indai halin Falie shine zamu dauka wallahi duk son da namiji yake miki indai akan girki ne watarana kuwa abin bazaiyi kyauba Allah yasa mu gyara Amin Ya Allah )_

_{AGW}_

SHURAKH Where stories live. Discover now