A ZATONA 1

635 17 1
                                    

A ZATONA
written by
Binta Yusuf
Xarahbint ❤
And
Bilkisu Ammani
Chuchu💕

Edited by Xarahbint❤

And so, fans this is the same story you've known,
💎 A ZATONA 💎
In case you've not read it, you can as well read it.
I'm sorry but iys written in my language HAUSA.

Kawai an d'an yi editing ne, kuma an yi merging kaman chapters 3 zuwa 1, dan chapters din sun yi guntu da yawa.
Saboda dama short love story ne.

A yi mana afuwa akan 'yan errors din da aka gani. Kasancewar it was our First novel. Wannan kenan

A ZATONA 1..
Tsugunne take bakin famfo, tana wanke kwanukan da ummi ta sata, Ta zurfafa a tunanin assignment din da bata yi ba, kuma ta san lallai sai Malamin su ya zaneta.. Sauri sauri gudu gudu ta cigaba da wanke wanken...
Ji tayi an dafa ta daga bayanta, juyawanta ke da wuya suka yi ido hudu da Mustapha..

Ya mata kallon wulakanci, "ke, baki iya gaisuwa bane?"

"Na je koyo sallama"
tace masa kai tsaye ba tare da wani tsoro ba ko fargaba...
Dan dama ba yau suka fara ba, kullum dai haka suke cikin fada da tashin hankali. Wani lokacin ma har dukanta yakeyi.

"Lallai ma yarinyar nan, ni kike gayawa wa bakaken kalamai? Ai ko sai na ci ubanki"
ta tashi tsaye "ubanka dai!"..
Daga hannu yayi zai sharara mata mari, ta ruga guje dakin ummanta.

UMMA!!!.
Ta kwala mata kira tun daga bakin kofa.. Umma ta fito a rude,
"lafiya?"
"Umma mustapha ne zai bugeni!"
Tsaki ummanta ta ja ta ce

"kar ki damu 'yar nan ba abun da ya isa ya miki, kin gama wanke kwanukan??"

Gyada kai kawai tayi gami da shigewa cikin daki tayi shirin islamiya. Nan da nan ta fito tsaf abinta!

(Hmmmm Salma kenan uwar tsafta)
"umma zan wuce" ta ce wa ummanta..
"Ki yi hakuri salma yau ban da abun da zan baki amma duba kwarya zaki ga goruban da na ijiye miki"

"nagode umma" a cewarta.

Umma ta tashi ta kulle kofa gami da sa kwado. Fitarta ke da wuya suka hadu da mustapha sarkin mugunta!!!

Da alama ma ya shayo giyan sa don a buge take.. A ranta ta rinka nanata "Lnnalillahi wa inna ilayhi raji'un...."
Mai kuma zai mata yanzu???

Ya dago kai ya kalleta cikin sigar wulakanci kamar yanda ya saba.
Nan da nan dabara ya fado mata,
"Mustyn Hajjaju"
ta kirashi da sunan da ya fi so,
"kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa"
nan dai ta shiga kwararo mai kirari, don ta san ta haka kawai zata iya kubuta daga hannunshi a yau..

Nan take ya fadada murmushi har sai da fararen hakoransa suka bayyana!. Cikin murya irin ta mashaya ya ce mata
"ina zaki"
"zanje siyo tuwon madara ne"
Ta fada a tsorace dan bata so ya gano komai
"A gayas"
ya ce mata gami da matsa mata..
Ta ture labulen kofar gidan tayi ficewarta!!!
Da yamma lis! Misalin karfe 6 ta dawo gida tare da 'yan uwanta Sumayya da Saifullah wanda suke kira da saif. Saif ya rugo da gudu yana murmushi dalilin ganin Abbanshi dayayi zaune a bakin kofar daki da butarsa yana jira a kira sallah.

Nan ya shiga bashi labarin abun da ya wakana a islamiya ranar, har da dukan da aka ma ya salma sabida lattin da tayi SALAMATU!! Abba ya kira ta a fusa ce don baya so ya ji an ce tayi lattin islamiya, kuma dazu sai da ya mata gargadi da karta yi latti...

(Toh!!! Ku ba salma shawaran abun da zata gaya wa abbanta).
"Na'am!!!"
Ta amsa da karfin gaske gami da sauri don ta amsa kiran abbanta.. Ta durkusa gabanshi cikin ladabi gami da cewa "gani abba"

Tace "Abba kayi hkr aiki ne ya man yawa banyi cikin lokaci ba",
Cike da gamsuwa da uzurin da ta bada yace
"to wnan ya zama ranar ta karshe ko mike ki tafi makarantar islamiyya..
Allah muku albarka keda yan'uwanki amin"
Gwago dake zaune taja tsaki tayi gaba

Please kindly vote and comment. Thank you

Written by:
Binta Yusuf (Xarahbint)
And
Bilkisu Ammani (chuchu)
Edited by: Xarahbint

A ZATONAWhere stories live. Discover now