A ZATONA 2

268 8 1
                                    

A ZATONA
written by
Binta Yusuf
Xarahbint ❤
And
Bilkisu Ammani
Chuchu💕

Edited by Xarahbint❤

A ZATONA 2

ASALIN SU

Mal. sule haifafen dan KATSINA ne !!
A ynzu hka mal sule yana kasuwanci domin Allah yasa masa nasibi sosai a hrkokin shago.
Matan sa 2 da yara 3, uwargdn sa itace gwago wadda Allah bai nufi ta da haihuwa (kasancewar haihuwa rabo ce dga Allah) take rikon dan kanwarta MUSTAPHA,
daga baya mal sule ya naima auren mahaifiyr salma (Nafisatu) soyayya ce mai karfi tsakanin Abba DA ummah.
mace ce mai ilimin addini ga tsafata inda suka sha bambam knan da gwaggo farko zaman su ba matsala sai da Ummah ta samu cikin salma aka fara kishi,
ummah ta dauke kanta ta basar da duk wani abu da gwago ke yi agidan har Allah yasa cikin ta ya isa haihuwa.

Ta haifo 'yarta kyakyawa ranar suna taci SALAMATU (Salma) bayan nan ta kara haihuwa 2 sumayya DA saif, salma da yan'uwanta sun sami tarbiyya ga ladabi da girmama manya wannan kenan.

Matsala guda ce ake samu daga gwaggo, saboda umma da yaran ta nasha wulakanci, tsangwama da zagi a wurinta....

Haka zamansu yake da ddi babu kullum ummah addu'arta Allah ya kare mata yaran ta

SALMA yarinya ce me hankali da natsuwa shekra ta 16 tana ss3 !!
Ta bangaren jikin ta kuwa, jikin fulani gareta, farace ga suma dan salma tana da gashi hr gadon baya,
yar duma-duma ce ma'ana she's extremely beautiful ga wushurya bakin ta sai dimples dinta.

yarinyar ta masifar haduwa, dama ita ba irin su Xarahbint bace 😜

kullum tana cikin hijab da yawa frnds dinta na makaranta na mata tsiyar sanya hijab wnan ra'ayinta ne, akwai chuchu frnd din ta takan ce

"Salma dani ke da rabin kyanki da an ga abubuwa, ki waye kinki kullum kanki na cikin tukunya"
tace "chuchu indai wayewar fitsarar zamani ce ba dani salma suleiman za'ayi ba"

haka dai kowa ke yabon tarbiyyar ta

Ta fita kiran saif ta hango......
Guess??? 😃

Well,
Mustyn hajajju ta hango tafe yana busa sigari a hanya ya tsaya ganin salma

"ke baby ina zaki da yamma nan"
tai fuska bata amsa shi ba, suna tsaye duk ya wanke ta da hayakin sigarin.

ya fara nuna ta da hatsa, "ba da ke nake mgn ba"
tace "ni ban da lokacin ka dan mahaifiyata ta aikeni"

"iyeee! da ni kike?"
Ta daka masa harara ta kwasa aguje yace

"zamu hade shegia dan son ki da nake da na karya ki uwar ki tayi asara"
kun ji fah mustyn hajjuju da karfin hali........

Haka ta shige gda tai sallah suka ci abinci tare da umman su, suna fira ko da ake sallah isha'i ta koma daki dan fara krtu. tana da test ranar monday !!
Nan ko samari sun kai uku suna aikowa ta ce ace tayi bacci.

Sorry for the disturbance, but I'll love it if you vote and comment. #nagode

Written by:
Binta Yusuf (Xarahbint)
And
Bilkisu Ammani (chuchu)
Edited by: Xarahbint

A ZATONAWhere stories live. Discover now