A ZATONA
written by
Binta Yusuf
Xarahbint ❤
And
Bilkisu Ammani
Chuchu💕Edited by Xarahbint❤
A ZATONA 9
Suna cin abinci wani yaro ya shigo wai ana sallama a waje, gwaggo tace
"saifu je kaga ko malam ake naima ne"ya tashi da dawowar sa yace
"Ya salma ana kiran ki wani ne da big motor yazo irin wace nakeso na siyo ma abba dana girma"
Daria suka sa dukan su, gwaggo ko, tsuke baki tayi"Allah dai yasa ba fada kika dauko awaje ba salamatu"
Tace
"a’a nima basan waye me kiran nawa ba"
" uhmm"
umma tace
"jeki ki sa hijab sumy ta raka ki kuyi sauri ko dawo ciki yamma ta soma yii…"Da fitar su taga salim tsaye jikin motar shi suka gaishe shi hr kasa ya amsa da fara’arsa yace
"ya mutan gda, kowa lfy lau kanwata wnan fa itace autar umma"
" No saif ne auta"
yace
"to ai itace autar mata ko"Suka dan murmusa sumy na rufe fuska an kirata da auta..
Ya sake sakin murmushi, Salma ko a ranta ta ce "wannan ya cika murmushi"
Maganan da yake ne ya sa ta d'ago kai, sai dai bata ji farkon maganarsa ba"...wannan autar taku tana da kunya sosai, ko dai ita za’a bani"
. Salma ta ce
"idan kana so se na sa sunanka a kan layi…"Sukaita fira hadda sumy da daga baya ta dan sake ta dena dena jin kunyar shi..
Ya ce
"ehen kanwata ina receipt"
ta zaro ido waje ta ce
"yaya tun dazu nake ta nema wlh ban….."
Katseta yayi cikin sauri yace "Don’t tell me kin batar"
sumy tayi saurin cewa
"yaya ba dole ta batar ba, wacce aka kusan nakasa ta dazu"
ya zaro ido ya ce me ya faru.. Salma ta galla ma sumy harara gami da cewa "ni sumy kin cika gulma wlh,"ta ce
" toh ba gara in fada ba, ko dan kar yayi fushi,"
salma ta ce
"a’a kiyi hakuri,"
ta matso ta rada mata a kunne ta ce "pls kar ki fada mishi, me kikeso in baki,"Ita ko sumy dama da yake ba’a sirri da ita ta bude murya ta ce
"kin tuna sabon rigannan da kika siya, me shegen kyaunnan to shi zaki bani.."
Salma ta ce
"Wlh sumy ni baki hadu ba. Kayan da nake so zan baki ai kuwa zaki bushe. Abun da ba ma shigan ki zaiyi ba? "
Ita ko sumy har ta manta wai Salim na nan tsaye..
Ta ce
"yawwa Ya Salma kince zaki siyomun bireziya idan na shiga JS1 amma har yanzu shuru.."
Shi ko Salim sakin baki yayi yai ta kallonsu, dan ganin sun ma manta da shi a nan..Se da yayi gyaran murya Salma ta tuna wai akwai wani halitta ban da su anan..
Take ta ji kunya gami da zungurin sumy, ta ce
"mara kunya kawai me bakin reza.."
Shi ko dariya yai ta yi don sun burgeshi sosai.. Da sumy ta ga baza’a bata abun da ta nema ba ta ko je kusa da shi ta jingina da shi ta zayyana masa duk abun da ya faru..Ya shiga nanata
"Innalillahi wa innna ilayhi raji’un… Harda fyade????!!!!"Kindly vote and comment pls.
#NAG
Written by:
Binta Yusuf (Xarahbint)
And
Bilkisu Ammani (chuchu)
Edited by: Xarahbint