A ZATONA 6

281 6 0
                                    

A ZATONA
written by
Binta Yusuf
Xarahbint ❤
And
Bilkisu Ammani
Chuchu💕

Edited by Xarahbint❤

A ZATONA 6

Ta kalleshi cikin mamakin Tambayar da ya jeho mata ta ce
"Yes gidammu ne"

se ya kara kallon labulen kofar gidan sosai don ya tabbatar da abun da ta gani.

Ashe musty ne ya gani, zaune a kasa da sigari a hannunsa, dayan hannun kuma kwalban giya ne,
ya ce
"waye wancan da ya zauna a kasa?"
cikin wani yanayi mara misaltuwa ta amsa masa da "yayana ne"
ya kalle ta ya maimaita ya ce
"Yayanki????"

Ta gyada kai, hawaye na zubowa daga idonta..
Don ta san lallai da kudinta ya je ya siyo giya don jiya ta ji goggo na masa fada, kuma ta kwace duka kudinsa kuma iya saninta dai musty baya sata, saidai in yanzu ya fara. Don ko da ta fito daga daki, daura dankwalinta ta lura, yanda ta bar jakanta ba haka ta koma ta ganshi ba, kamar an dan matsar dashi. Amma dai tunda an ce zato zunubi, se ta share.

Tabatan da yayi ne ya sa ta dawo daga duniyar tunanin da ta shiga..
Ya ce
"kanwata ina ta magana kin mun shuru"
ta ce
"Sorry ban ji bane"
yace
"ok.. nawane kudin waec din"

ta ce mishi
"Da dan yawa Fa"
ya ce mata
"Fada mun mana"

zatayi magana kenan ta ga Abba... cikin mamaki da tsoro ta fara kuka ta ce
"Shi kenan na shiga uku, Abbana ya ganni"

Cikin ikon Allah hankalin Abba bai kai wurin su ba,
ta saki ajiyar zuciya tana hamdala shi kuwa daria ta bashi yace
"naso Abba ya ganki naga dukan da zai ma kanwar tawa"
ta dan saki murmushi

Ya fido da rafar 500 ya bata ta zaro ido waje
Yace
"it's for u kije gobe ki biya kudin weac da jamb registration and keep dem safe ko ki bada a aje miki zuwa tmrw morning zan zo in d evening naga receipts din, nasan by then kin dawo gida ko.. "

Ta daga masa kai ta balla hannun kofar zata fita. Har ta fara tafiya kuma ta dawo

"Nagode Allah saka da alheri u made it possible 4 me thank you very much "
yace
"shiii u're welcome sis"
Sai tace
"yayana meye sunan ka baka fada man ba,"
"You can call me yayan ki kamar yadda kk fada but am SALIM AHMAD"
tace
"wow nice name ya salim" yayi murmushi sannan ta daga masa hannu ta wuce.

A guje ta nufi soron gidann su ta hade da musty a kwance yana maye da surutai tace
"Allah ya shurya"
Sannan ta shige ciki

Kindly vote and comment. #oneluv

#NAGODE

Written by:
Binta Yusuf (Xarahbint)
And
Bilkisu Ammani (chuchu)

Edited by: Xarahbint

A ZATONAWhere stories live. Discover now