A ZATONA 3

208 7 0
                                    

A ZATONA
written by
Binta Yusuf
Xarahbint ❤
And
Bilkisu Ammani
Chuchu💕

Edited by Xarahbint❤

A ZATONA 3

Yaw Monday, ta shirya da wuri don test din da take dashi..
Ta gama shirinta tsaf ta taso kan kannenta suka wuce.. Umma tana zaune a zaure tana tankade, ta ga salma ta dawo gida..
Mamaki ya cikata..
"lafiya na ganki da rana tsaka?"
"Umma koroni sukayi, kin san an ce mu biya kudin waec tun sati 2 da suka wuce, toh shine sukace wai inje in kawo"
"toh sai ki jura abbanki ya dawo ya baki . Ga tuwo nan a tukunya"
a cewar umma..
ta ce to ta wuce ta dibi abin ci ta ci..
karasawarta ke da wuya ta jiyo sallamar Abba, ta shiga addu'an Allah ya sa ya yi ciniki a shagon don dama ya mata alkawarin jiya zai bata..

amma bata tuna masa ba don ta san Abbanta akwai cika alkawari in da hali..

Jiyo maganar su tayi sama sama suna magana akan yanda zaa samu kudin buya mata waec din....
hankalinta ya dan kwanta da ta ji ya ce ya samo kudin waec da jamb, anma be samu na neco ba..
ta shiga murna da tsalle tsallenta ita kadai a dakin..

Takun da ta jiyo kusa da kofar dakin ne ya sa ta dan tsaya cak!!!!...

Turus yayi ya tsaya yana kallonta don rawan da ya ga tanayi.. "salamatu me kikeyi haka?"

"Ba magana nake miki ba"
ya sake fada don shurun da ya ga tayi..
(ummm su salamatu ashe dai an iya rawa) ta dan wayance "Abba na dan buge kafana ne shine nake kokarin daidaitosu don ganin ya rage zugin da yake mun"

"Ummm Allah shirye ku"
ya fada gami da shigewa daki don shi ya san rawa ya kama ta tanayi...

Kashegari ya bata kudin waec da jamb din, cikin murna ta ansa ta sa a zif din jakanta gami da mishi godiya sosai..
sannan ta tasa keyar yan uwanta suka fice..

A zauren Gidan suka hadu da mustyn hajjaju, suka gaisheshi suka wuce..
Sun yi nisa a hanya sannan Sumy ta kare mata kallo sosai ta ce mata "ya Salma kin manta baki sa dankwali ba cikin hijabinki" nan ta tuna da ta barshi a kan kujeran falo..
murna ya sa ta manta.
Ta ce musu su wuce bari ta je ta dakko...

Sauri sauri, har ta isa gida..

ta tarar da musty a inda ta barshi yana faman busar sigari abinshi.. "baby ya na ga kin dawo, ko dai kina missing dina ne.. to gani ba inda na je"
tsaki ta ja, don takaici ma ta kasa cewa komi.
Ta ijiye jakanta, cikin sando ta shiga dakin don kar Abba ya jiyota, ta sanya dankwalinta ta fito
(don ita prefect ce, kuma dole su sako farin dankwalinnan ko kuma a korasu).

Fitowarta bata ga Musty ba. Bata damu ba ko kadan, asalinma ta ji sanyi har a ranta, ta je ta ansa tellern waec din a makaranta ta wuce banki don ta biya..

Ta shiga bankin ta bi layi, se da layi ya kusan zuwa kanta ta duba zif din da ta sa kudin, sukace daukammu inda kika ijiye mu!!!... Subhanallah!

Kindly vote and comment, it keeps me writing.

#NAGODE

Written by:
Binta Yusuf (Xarahbint)
And
Bilkisu Ammani (chuchu)
Edited by: Xarahbint

A ZATONAWhere stories live. Discover now