A ZATONA
written by
Binta Yusuf
Xarahbint ❤
And
Bilkisu Ammani
Chuchu💕Edited by Xarahbint❤
A ZATONA 7
Da shigar ta gda tayi sallama su sumy da umma tasamu zaune se fira suke ana daria
Umma tace
"har kin dawo?"
"Eh umma na" ta ce a takaice"to maza kici abinci kafin ayi sallah magrib ko" Umma ta ce gami da nuna mata inda abincin ke ijiye.
Ta miki zuwa kitchen ta dauko
"dafa duka ce shinkafa" (rangem rangem gem)
tana ci tace
"ummah dama inaso muyi magana dake"Umma ta ce "gama ci tukunna, ba na hana ku cin abinci kuna magana ba?"
Tace "au hakane. Yi hakuri na manta ne"
Nan dai har ta gama ci, suka shiga daki atare, ta fara bata lbrn dga farko har karshe Umma ta ce
"Shine baki fada man ba, haba salma yanzu da ba bacin wnan bawan Allah ba ya zakiyi. kin ga har zuwa wurin principal da kikayi bai dace ba, laifin ki ne sbd kinje naiman alfarma wurin shi yazo miki da mgnr iskanci. wnan ya zama na farko kuma na karshe, ki tsare mutuncin ki da namu salma, ita ya mace yar kula ce shiyasa ko da yaushe muke muku fada ....wnan yaron da ya baki kudin nan fa?
Dan gdn waye??""chap, Umma wlh basa ni ba amma yace zai dawo gobe yaji idan nayi registration din"
"ok Allah kaimu lafia""amin umma na nagode!!!"
Tace cikin jin dadi.Washe gari ta je ta biya kudin a skul don bazata iya zuwa bank ba, har principal din ya dan ji kunya da ya ganta da kudin amma da shike yana jin haushinta,
se ya ce mata
"Dama chan iskanci kika zo mun dashi da kika ki kawo kudin ko, zanyi maganinki stupid kawai"
abun ya bata haushi tace"sir na kawo maka kudin, i see no reason da zaka rinka zagina.. ka sani, wallahi bazan dauka ba kuma, taimako dai na san nazo na nema amma yanzu bana bukata"
Cike da mamaki ya saki baki galala yana kallonta cikin mamaki cux he never expected that from her ta dora akan magananta da
"Ni kayi sauri ka ban receipt in fita a nan wurin mara mitunci kawai.".
Ta mishi tas! Dan ta san ba abun da zai uya fada mata.Ya rubuta receipt cikin sauri ya mika mata gami da mata wani irin kallo na jeki-kya-gani..
Ta ja tsaki ta fita...
Ta je ta shiga class aka ci gaba da karatu..
Ana tashi ta taso keyar kannenta suka dawo..Dama akwai wani shortcut me kama da lungu da suke bi zuwa gidansu suna hiransu suna tafiya kawai suka ji tattaki a bayansu..
juyawan su ke da wuya sukaga wasu hefty builded guys sun kewaye su, saif na ganin haka ya ruga aguje ya tafi..
Sumy da salma na tsaye anan jikinsu na rawa... se suka ga boss din nasu ya taho cikin fushi ya shake wuyan salma gami da watsa mata mari!!!!Tirkashi!!!
Mu hadu a na gaba!Kindly vote and comment. Thanks
#NAGODE
Written by:
Binta Yusuf (Xarahbint)
And
Bilkisu Ammani (chuchu)
Edited by: Xarahbint