A ZATONA
written by
Binta Yusuf
Xarahbint ❤
And
Bilkisu Ammani
Chuchu💕Edited by Xarahbint❤
A ZATONA 8
Sumy kuwa, ganin an mari yayarta yasa ta kwalla kara sosai tana fadin
"Dan Allah ku kyale man yar'uwa ta Mai tai muku"
Kuka take sosae, can bangaren saif ne ya isa gda a guje dan kiran Abba da zuwan sa kofar gda.
Musty na iso wa ya ganshi a rude yake tambayr shi me ke faruwa?
saif cikin kuka yake fadin"ya salma ce, an kama su kashe su zasuyi"
Habawa!
A gigice musty ya tsayar da dan achaba Ya sa Saif a gaba ya ce ya nuna mishi hanyr wajen..Da zuwan su suka iske Salma a kasa, da gani ta sha bugu.
Sumy kuma sai rawar tsoro takeyi tana shan shessheka. Fuskan nan nata Shima yayi ja, kasancewar farin fata gareta.Aikuwa musty ya taru a kan su ya rige boss din ya cigaba da naushin sa ta ko ina, se kuma ya yo kan Salma. A tsorace ta Kalle shi don tana tunanin yana daya daga cikin su ne.
Nan ta fara bashi hakuri. Ya mata murmushi ya ce
"kar ki damu I'm here"Tana shasheka se kuma sabon kuka Saif yace
"Ya salma kiyi hkr,"Nan ko Musty ya koma kansu ya shake ogan su, ya watsa mai mari. Ya ce
"wa ya aikoku, dan na san ba abun da baby ta muku"
Ko kula shi bai yi ba, nan Musty ya kara jin haushi ya yita bugun su da kafa gaba daya, kasancewar suna kwance a kasa ne.Cikin dan lokaci sun sha wahala dole suka fara bayani ashe principal ya aiko su suyi mata duka harda fyade, musty dasu sumy suka saki baki suna mamakin hakan to meya hada ta dashi kuma.
Nan Musty Ya sa Sumy ta kirawo wani dan sanda neibour din su,
Da ya fito ya ne ya gansu cirko cirko ya tambayi
"meke faruwa?"Musty ya mishi bayani aikuwa ya tura su mota se station yace abar case din hannun shi su.
Salma sukayi gda taji dadi a ranta ashe dama mustyn hajajju zai iya taimakon su ohho..Cen bangaren umma hnkalin ta ya tashi taji shiru basu dawo ba.
Kindly vote and comment. Thanks
#NAGODE
Written by:
Binta Yusuf (Xarahbint)
And
Bilkisu Ammani (chuchu)
Edited by: Xarahbint