Assalamu Alaikum warahmatullah. Yan uwa am back again. It's complete ready to be published but I will have to make some additions and Editions. But will unpublish it imidiately I post the last chapter.
Any way Ummu-Abdoul loves u loads. Will update everyday if I will get maximum votes nd comments. Ejor, pls don Allah banda laɓe. Aswear I love u dearly for d sake of Allah.
✏📖
®
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION.🏡 GIDAN AURENA 🏡
(Ummu Abdoul July 2016)Sadaukarwa
Ni safiyyah Ummu Abdoul na sadaukar da labarinnan ga ďaukacin mata musulmai da ke samun matsaloli a gidajen aurensu. Da kuma Inyamurai Musulmai (Igbo Muslims) wa'inda aka maida su jemagu karfi da yaji. Musulmai na kyamatarsu arna na hantararsu. Allah ya kara daukaka musulunci da musulmai. AameenMATASHIYA
Zaune take a doguwar kujera hannunta rike da Mujallar 'Fikra' tana karanta daďaďan labarai da ya shafi Rubutu da Marubuta Hausa.
Hankalinta ya ďauku akan hiran da akayi da Marubuciya Khadija Sidi wacce aka fi sani da Sidiya,"Soyayya ta ga mahaifiyata yasa nake amfani da sunanta a duniyar rubutu, amma asalin Sunana Salmah Ateeku " Ta karanta yafi so goma tana murmushi, " Ai duk dan da bai so uwarsa ba tabbas yayi asara." Ta faɗi a bayyane sannan ta cigaba da karatun ta, can tambayar yar jarida Sanah Matazu ya sake ɗaukan hankalinta inda ta ce
"A duniyar rubutu mai yafi baki sha'awa, kuma meyasa?"
Salmah kuma ta amsa da cewa
"FIKRA WRITER'S ASSOCIATION yafi bani sha'awa don tun kafin kafuwar ta kashi casa'in da biyar na marubutan tafiyarsu ɗaya, wato su mutane ne da ke son cigaban wasunsu fiye da kansu, sannan sun fara harkar ne don cigaban Adabin hausa ba don neman shahara ba, sannan suna tare da duk wani marubuci ko da bai kasance a cikinsu ba, dalilin hakan yasa suke ban sha'awa kuma suka kasance min madubin dubawa har ya kai ma da bazarsu na ke rawa."
"Kar dai ace kina yabon kanku ne?" Sanah ta katseta
"A'a wallahi, ai duk wani marubuci abin sha'awa ne matukar bai fake da sunan rubutu yana yaɗa alfasha ba, ni idan kika ce in faɗi marubuciyar da nafi son rubutunta zan ce miki Ayeesha Chuchu ce, kinga bata cikin kungiyar, ga su Feenat, YBK su Biebie su lubabatu mai tafsir da dai sauransu, fata dai Allah ya biya duk wani marubuci da kyakkyawar sakamako."
"(Wow Bravo alaiki!)" fadin makaranciyar.
Haka ta cigaba da karatun tana mamaki da hazak'arta da fikran da Allah Ya bata wajen sarrafa labari da isar da sak'o zuwa ga al'umma.
"Hmmm kowa da baiwarsa, ga boko ga addini ga fasahar gina labari." Ta faďi tana mai sauke da ajiyan zuciya.Matashiyar mata ce wacce bazata wuce shekaru talatin da biyar ba. Bak'a ce mai faďin fuska. Duk da zaune take hakan bazai hana maka gano kyawun surarta ba wanda shi yafi komi ďaukan hankalin mutane. Kallo ɗaya masana halayyar dan Adam zasu mata su gano tarin damuwar da ke likimo a k'ark'ashin fuskarta mai yalwar murmushi.
Sallamar da akayi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin hazika Sidiya da takeyi.
Mijinta ne ya shigo wanda a shekaru bazai wuce arba'in ba. Fari kyakyawa ajin karshe, dogo ne da tsawonsa ke yawan bayyana gajartanta.
"Sannu da zuwa." Ta faďi tana mai mika hannu don ta amshi jakar hannunsa."Wai yanzu Afaf haka zaki 6arnatar da lokutanki wanjen karance karance. Bansan ko rayuwar jiranki zaiyi ba baki da aiki sai karanta jarida da littafai." Ya faďi a tausashe yana mai shashantar da gaisuwan da tai masa a farko.
"Amma dai Affan ka amsamin gaisuwar da nai maka ko?" Ta faďa cikin sanyin murya.
"Au dama magana kikayi?" Ya tambaya yana mai kallonta cikin ido.
"A'a matattaran la66a na ne haka nan." Ta faďi tana banka masa harara tamkar idanunta zasu zazzago.
Bai amsa mata ba ya janye jikinsa zuwa ďakinsa inda wanka kawai yayi sannan ya fito.
"Za muje na zubo maka abinci ne?" Ta tambaya tana nuna masa saman teburin cin abinci.
Wani malalacin kallo ya bita dashi sannan ya juya ya fita, saidai k'arar motarsa taji.Nan wajen ta zauna daɓas, ita kuma haka rayuwarta zai kasance? Ace sam babu wani abu mai suna farin ciki a gidan aure da take ji ana faɗin daɗi ne dashi.
"Oh na shiga aljanna na kasa fita."
#fikrawriters
#StandWithSccvolunteersEhmm u will get d complete version at okada books. Just search for fikrawriters or gidanaurena
YOU ARE READING
GIDAN AURENA
General FictionCompleted on 27th October 2017 #1 in General Fiction more than 10x since 2/10/17, #2 in General fiction 12/09/17 Afaf ta kasance abar so ga kowa tun daga kakanta har zuwa iyaye da yan uwa har dangi da na nesa, nagartanta da kyawawan dabiu ya haifa...