Completed on 27th October 2017
#1 in General Fiction more than 10x since 2/10/17,
#2 in General fiction 12/09/17
Afaf ta kasance abar so ga kowa tun daga kakanta har zuwa iyaye da yan uwa har dangi da na nesa, nagartanta da kyawawan dabiu ya haifa...
Ups! Gambar ini tidak mengikuti Pedoman Konten kami. Untuk melanjutkan publikasi, hapuslah gambar ini atau unggah gambar lain.
GIDAN AURENA Kamar yanda ko wani aure kan zo da faɗi tashi haka rayuwar auren Afaf da Affan ya kasance. Sun so junan su kamar za su haɗiye juna kafin bikin su da kwanakin farko a aurensu Ranar da abin ya fara ta kammala shara kenan gashi tana laulayin cikin wata ďaya. Da kyar ta iya share gidan sai gashi. Kamar yanda ya saba ya wuce ba tare da ya kwa6e takalminsa ba. Ashe ya tako kashin shanu shi kansa bai kula ba. Ya je ya rungumeta kamar yanda ya saba sai ta hankaďe shi "Fisabilillahi yaushe zaka fara tausayi na, ji abinda ka tako da kyar fa na ke iya shara" ta faďi a fusace. Juyawa yayi yaga abinda ya tako sannan ya juyo da kallonsa zuwa gareta yace "Mami na bata ta6a ce min in nai aure ni zan dinga ma mata na shara ba, sannan ban ta6a jin inda aka ce Miji yai shara ba da zaki faďa min magana ko da nake yi miki a da ganin dama nane ko" ya faďa da murmushi sauke akan fuskarsa wanda hakan ya kara kular da ita. "Sannan kuma ba'a ce don kayi aure shike nan zaka dinga taka ko'ina da takalmi ba" ta faďi tana mai jan karamin tsaki wanda da ba don yana kallonta ba bazai ta6a ganin tayi ba. "Ina ce gida na ne, sai ki barni inyi duk abinda naso da gida na" ya karasa yana cigaba da tafiya batare da ya cire takalmin ba. *** Abin da ya kara karfin igiyar aurensu samun uwar miji mai ilimin addini da aiki da shi. Ta taimaka ma Afaf da adduoi ingantattu da kuma salo salo na samun nasara cikin sauki Don samun wannan romon Biya don karanta labarin GIDAN AURENA akan farashi N350. Labarin zai zo a cikin kwana bakwai Kawai insha Allah tsakanin 1-7 ga watan Afrilu, yana kuma shafin okada books @fikrawriters.
biya zuwa ga 0069724232 Abubakar Safiyyah jibril Sterling Bank Sai ki tura shaidan biya 07010137848