Mayunwacin Zaki

2.6K 202 64
                                    

Iska ne ke kaďawa, rassan bishiyoyi na harďewa suna fitar da sauti tamkar zasu faďo. In ka saurara a fakaice sai ka rantse mota ke wucewa. Garin yayi tsit saboda sanyin hunturun da ake a birnin na Zazzau.
Afaf ce zaune da yaranta suna kallon shirin jenifer's diary a tashar NTA. Suna kyal-kyalta dariyar turancin ta da sauran shirmen da fitacciyar yar wasa Funke Akindele ke yi a matsayin ta na jenifa, inda basu fahimta ba kuwa sai su tambaye ta.

"Mimi ban ci jarabawan nan sosai bafa, kinga 50 naci a lissafi " faďin Aabidullah yana mai yamutsa fuska kamar zai ɓarke da kuka. Nan ta ankara da sam bai ce komi ba tun da aka fara wasan duk da kasancewar sa mai kaunar shirin fiye da sauran yan uwansa.

"Ta6! Aiko zaka sha masifan Abba" faďin Afreen tana dariya ciki ciki. Ganin babu wanda ya tanka mata yasa ta kara da faɗin

"Kun san ana zaune ƙalau ma Abba boss ne ballantana kuma baka ci Exams ɗinka ba, hmmm kawai se duka" hakan ya sa Aabidullah fashewa da kuka, sauran yan uwa na taya shi in ka ɗebe Afreen da ke dariya ciki ciki alamun mugunta

Cike da fargaba da tausayin kaiAfaf ta kalli Yaranta, rasa bakin lallashin su tayi sai ma ita da taji wani tukukin hawaye da ya taso mata daga kasan kirjinta, amma sam bata bari matantakanta ya sa hawayen fitowa ba balle sautin kukan, kallon yaran tayi sannan tace "yaushe zan faďa muku ku yarda? Ina so ku fahimci Abbanku na sonku fiye da komi, ku ne hasken zuciyar sa, duk wani faɗa da zai muku saboda ku yi alfahari da kawunan ku ne ba don komai ba. Ba ku ga ya kai ku The most expensive school ɓa (makaranta mafi tsada) " ta faďi tana tausasa murya.

" Amma baya mana dariya kuma... " Aaida bata karasa faɗin abin da tayi niyya ba suka ji alamun mutum a kofar.

Buďe kofar da yayi ya hana ma yaran magana, nan su kayi mutuwar zaune kamar sun hango malakul maut. Tashi tayi cikin hanzari hakan yasa yaran suka bi ta don tarbon Mahaifin su wanda hakan ne al'adansu.

"Abba sannu da dawowa" duk suka faďa har ita ďin. Tana mika hannu don amsar jakansa.

"Wai ke yaushe zaki gane ba kuďin banza gare ni ba da zaki dinga kwasan dukiyata kina Almubazaranci dashi, ni ban hana kowa zuwa gidan nan ba amma in sun ci sun sha uwar me kuma zasu tafi dashi, da za'a ishe ni da godiya" ya tare ta ba tare da ya amsa musu gaisuwan ba ko mika mata jakansa da take mika hannu. Yana kai aya ya tasa kai ya wuce ɗaki. Wanka yayi Ya sauya kaya zuwa jallabiya sannan ya fito. Abincin sa ta sa masa yana ci yana hura hanci kamar ba abincin da Yaranta suka gama ci suna santi ba.

Ganin zaman ba zai fishe su ba ta ce da yaran

"ku muje lokacin Hikayaat yayi" Ta faɗi tana kallon yaran da murmushi zahirance amma a badinance tausayin kanta da Yaranta ne fal a zuciyar ta, sannan a wani bangaren kuma tsanar mijinta da a da tafi so ne. Haka suka karasa dakin Yaranta inda suka yi wanka suka sauya kaya sannan suka koma dakin ta, ta zauna a kan babban Chinese kafet din dakin su kuma yaran suka jingina a jikin ta. Littafin HIKAYAAT AMMOU MAHMOUD ta dauko ta fara karanta musu

"KISSAN WANI ATTAJIRI MAI TAUSAYI
Can wani zamani daya wuce, akwai wani mutum attajiri sunanshi Abdurrahman kuma wannan mutum ya kasance attajiri ne wanda ya shahara kuma ya zamo yana da tausayi, yana kyautata ma talakawa da mabukata, kuma yana basu bashin duniyar da, kuma yana hakuri dasu.
Wata rana wani mutum yazo ya buga mishi kofa, ya nemi bashi a wurin sa domin yayi kasuwanci saboda duk dukiyar da ya mallaka sun kare gaba daya. Abdurrahman ya bashi dukiya haɗe da sanya lokacin da zai dawo masa da kudinsa. Wani ma ya sake zuwa ya amshi bashi don yayi aure shima ya bashi tare da sa masa lokacin amsa.
Mutum na uku ya zo, ya nemi bashi domin ya biya ma mahaifiyarsa kudin magani, sai a duniya bada kudin da ya bukata kuma sanya lokacin da zai dawo masa dashi. Mutane da dama sun zo neman bashi wurin sa kuma ya basu tare da lokacin, da zasu dawo dashi.
Lokacin biyan bashi yayi, sai Abdurrahman ya aika yaransa domin su amso masa basusuka da ya ke bi, amma yai ma yaran wasiyya cewa "idan Kunga wanda bai da shi kada ku matsa masa"

GIDAN AURENA Where stories live. Discover now