Shimfida

6.7K 276 3
                                    

*RIKITACCEN AL'AMARI*
       ~A short story~
~Inspired by true life events~

*Na Billy Ladan*

♻ *EXCLUSIVE WRITERS FORUM*

        bintladan.blogspot.com

_Wannan littafin gaba dayansa sadaukarwane ga kawata,aminiyata *Hauwa Suleiman Muhammad*_
_U understand me moredan any1 else,uv always bn there for me. In U I find my second self. I am blessed to have u  both as my Mirror  as well as my Shadow because Mirrors dont lie n Shadows neva leave._

_Hia is a quote for u swidy_
_"A friend is someone who reaches out for your hand, and touches your heart.Thanks for touching me in more ways than one.I cherish your friendship!"_

Bintalo! Bintalo! Yarinyar da ake kira da Bintalo ta juyo a kufule tana kallon mai kiran nata, tsaki ta ja tareda cigaba da tafia. Da sauri daya yarinyar ta kamota tace "Bintalo kina jina ina kiranki amma kika wani basar dani,dadina dake dama wulakanta mutum, hararta Bintalo tayi sannan tace "ai Zulai ko meh na miki keh kika siya da kanki dan sau nawa nake cewa banson sunan nan amma kiga yanda kike wani daga murya kalan samarin anguwannan su raina ni ko? Dariya Zulai tayi sannan tace "toh meh kike so in kiraki, ni dai da Bintalo ns sanki kuma hakan zan cigaba ds kiranki" cikin bacin rai Bintalo tace "in bazaki kirani da Binta ba toh lalle baza mu shirya ba, duk sanda ki kara kirana da Bintalo wlhy bani bake" cikeda mamaki Zulai ta dubeta sannan ta dan dafata "toh naji Binta zan kiyaye" sai sannan ta dan saki ranta, karasaw sukayi bakin rafin suna yar hirarsu. Wasu 'yan samarine su biyu suka zo suka musu sallama, Zulaice kawai ta amsa yayinda Bintalo ta ja wani uban tsaki tareda kawar da kanta, daya daga cikin saurayin ne yace "Bintalo ai ko ba komai kya amsa sallamar mu ko, harara ta watso mai tareda nuna shi da dan yatsa sannan tace "Iliya wlhy ka fita harkana kaji na gayama in ba haka ba sai na ma abunda bazaka taba mantawa dani ba, wai ana soyayyar dolene, kuma anki a amsa sallamar naka sai kayi abunda zakayi" tsaki daya saurayin yaja tareda cewa "kai ma Ilu sai kace maye ka rasa wanda zaka likewa sai wannan mara kunyar, ni ban ma ga abun so a jikinta ba,yarinya in banda fitsara ba abunda ta sani" katsesa Bintalo tayi ta nunosa da yatsa shima "kaga Shamawilu ban kasa da kai sabida haka ka ja tsamin bakinka kayi shiru kafun inma rashin mutumci "nunota yayi shima da yatsa yace "ke nifa ba Ilu bane da zai juri rashin kunyarki yanxu sai in baki jikinki a nan" murguda mai baki tayi tareda harararsa sannan tace "sai kuma in tsaya ka jibgeni,kana tabani wallahi zamu kwashi yan kallo da kai" da kyar Zulai da Iliya suka shiga tsakaninsu dan dagaske Bintalo ta ci serious, in an barta hada kafada zatayi da Shamawilu, da kuwa ta kwashi na jaki dan daga gani Shamawila ba karamin kashi zai bata.

Sai da suka bar wajen Zulai ta dubeta tace "Binta kenan yanxu ke da an barki dukansa zakiyi, koh kin manta waye Shamawilun, kuma ni banga aibun Iliya ba, saurayine san kowa kin wanda ya rasa, gashi da kwazo da arziki, duk garinnan ba wanda ya kaisa noma kuma yana samu sosai, duk matan kauyen nan shi suke so amma ke da ya likewa ko kallo bai isheki ba" Tashi Bintalo tayi ta dubi Zulai tace "haba Zulai, kalleni da kyau, dubi kirar da Allah ya mun" ta fada tana jujjua jiki, "ke sai yaushe zaki gane cewa kalata sam ba na kauye bane, dirin da Allah ya mun na matan manya ne, irin Alhazawan birnin nan shi yasa kika ga ban kula kowa a kauyennan dan in kinga nayi aure toh dan birni na aura wanda zai kaini can in rayu cikin dadi, in an ganni a kauyan nan toh ziyara ta kawoni in so samu ma in tafi da su inna can mu zauna baki daya zama na har abada" cikeda mamaki Zulai ke kallonta sannan tace "lalle Binta kinyi nisa amma sai dai ki sani duk yanda kika kai da kin nan ne tushenki bakida inda ya fishi har karshen rayuwarki tarihinki a like yake da wannan rugar, kuma ma abunda kike fadi ko a mafarki bn jin zai faru, wani dan birni zai shigo wannan kauyen tamu har ya aureki,gskia da kamar wuya" duk da maganar ya batawa Bintalo rai, murmushi tayi sannan tace "Zan baki mamaki Zulai dan wlhy ko ta halin yaya sai na auri mai kudi kuma inje Birni, ni kinga tafiyata" tashi itama Zulai tayi sukayi sallama kowa ya wuce gida amma zuciyar Zulai cike yake da mamakin kawar tata.

Rikitaccen Al'amariWhere stories live. Discover now