*RIKITACCEN AL'AMARI*
~A short story~
~Inspired by true life events~*Na Billy Ladan*
*Dedicated to Hauwa Suleiman Muhammad*
bintladan.blogspot.com
_Aunty *Aishat A Muh'd* wannan shafin na baki shi kyauta, u r such a nice,simple,kind and generous person, a gaskia samun irinki sai an tona, Allah ya biya miki bukatunki,ya saka miki da mafificin alkhairansa.Ina sonki har cikin raina_
Kotun cike yake makil da mutanen da suka zo jin ya case in Juwairah zata kaya, a dama Barrister Abbas ne zaune da mai tayasa defendn case insa, a hagu kuma Barrister Shureim ne zaune da Juwairah a gefensa sai kuma wani abokin aikinsa. A first row na audience na hango Inna,Abba,Bintalo da Bashir suna zaune duk damuwa rubuce a fuskarsu, sunfi minti biyar suna zaune ana jiran judge, umarni naji an basu duk aka tashi sai ga judge in ta shigo fuskan nan nata a murtuke kai kace bata taba daria ba. Sai da ta haura mazauninta ta zauna sannan kowa ya koma ya zauna. Medicated glass nata ta dauko ta maka a idonta sanna ta dan yi rubuce rubucenta, ba tareda ta dago ba tace "lawyern mai kara ur opening statement" cikin nuna isa da takama barrister Abbas ya bar mazauninsa ya zo gaba, wani kallo ya watsa wa Shureim da Juwairah sannan yace "ya mai girma mai shari'a da duk sauran mutane dake zaune a cikin kotun nan ina muku barka da warhaka, kamar yanda kuka sani ana shari'ane akan wannan gagarumar yar ta'addan da ta addabi ba nan kasarmu ba har ma da wasu kasashe" ya fada yana nuno Juwairah "she is a cold bloody murderer da ta dauki rayukan mutane uku aciki harda saurayin da zata aura, bayan ta kashesane ta gudo nan ta aikata wasu kisan kuma ta so lakaya wa mijin yayarta da ya bata dukkan wani gata amma dan butulci irin na dan Adam ta nemi lakaya masa, as we proceed zan fayyace muku daya bayan daya ta yanda zaku gamsu cewa ita tayi dukkan kisan nan" yana gama fadin haka ya danyi bowing wa Judge Sharifa tareda sake watsowa su Shureim harara sannan ya zauna. Yan rubuce rubuce Judge Sharifa tayi sannan ta ce "Lawyern wanda ake kara how do u plead?
" not guilty by reason of insanity" Shureim ya fada tareda tashi, "client ina na fama da wani condition da ake kira MPD" nan ya shiga kwararo musu bayani da Dr Abdulmajeed ya masa sannan ya kara da cewa "as d trial progress zan yi kokarin gamsar da ku akan cewa Juwairah bata yi kisan nan ba,alters nata ne sukayi kuma bata da masaniya akan hakan" yana gama fadin hakan shima ya koma ya zauna. Yan rubutu tayi sannan ta dago ta kalli barrister Abbas tace "r u ready to proceed? " yes ur honor" ya fada tareda tashi ya fito gaba ya tsaya yana kallonsu, yayi hakan na kusan minti daya sannan ya saki wani uban kara, kallonsa duk aka tsaya yayi can ya hau dariya ba kakkautawa sannan yayi shiru ya tsaya yana kallonsu, tafi yayi yace "ba dai kuna jira in baku hakuri ba, dan nima ba ni nayi ba,alter na ne yayi" "objection ur honor" Shureim ya fada "korafi bai karbu ba,barrister yusuf kana iya cigaba" yaji Judge Sharifa ta fada, wani murmushin mugunta Abbas ya watso mai, cikin sanyin jiki ya koma ya zauna sannan barrister Abbas ya karasa "ynxu zan kira mutum na farko da zai bada shaida wanda zai tabbatar muku cewa juwairah ita tayi wannan kisan, ido yayi aka shigo da wani, karasawa yayi gabansa yace "inaso ka gayawa kotu sunanka da kuma aikinka" gyaran murya wannan bawan Allahn yayi sannan yace "ni sunana agent Aaron kuma ina aiki ne a wajen tantance fingerprints" kada kai Abbas yayi sannan yace "shekaru nawa ka dauka kake aiki a can? "Kimanin shekara goma sha biyar knan yanxu" ya mayar mai, sake kada kai yayi sannan yace "na tabbata ka ci karo da finger prints da aka kawo muku na wannan murder cases in" kai ya gyada alamar eh, sake kada kai Abbas yayi alamar gamsuwa sannan yace "inaso ka fadawa ko kotu abunda ka samu akai" dan gyara zama agent Aron yayi sannan yace "eh toh bisa bincekenmu dai ya nuna wanda yayi kisan nan mutum dayane dan duk iri dayane kuma yayi pointing at Juwairah" godia yayi masa sannan ya juyo yace "ya mai girma mai shari'a wannan hujja kadai ya isa ya gamsar da kowa kan cewa Juwairah ita tayi kisan nan amma nan ba da jimawa ba zamu kawo wasu shaidun su sake gamsar daku" zama ya koma yayi sannan Judge Sharifa ta dubi Shureim tace "koh kana da tambaya? Tashi yayi tareda kada kai tareda cewa "banda tambaya ur honor, sai dai inason wannan kotu mai adalci tayi amfani da basirarta dan gano cewa bamu mutum mai hankalin da zai yi kisa sannan ya tafi batareda ya binne duk wani abu da zai sa a ganosa ba,dts ol ur honor" ya fada tareda zama, umarni aka bada aka fitar da agent Aron, bai jimaba aka shigo da wani tsohon balarabe, Barrister Abbas ya taso yace "Ur honor shaidata na biyu kenan, karasawa yayi yace "ko zaka iya gayawa kotu ko waye kai? Gyara tsayuwarsa tsohon nan yayi sannan yace " ni sunana Abdulrauf kuma mai gadine a gidan shahararran dan kasuwan nan na garin dubai wato Abdulkadir,
"Koh zaka iya gayawa kotu abunda ka sani gameda mutuwar uban gidan naka"
"Eh wata daya da ya wuce kenan wata daren lahadi uban gidan nawa ya shigo da wata yar budurwa,nidai naga shigansu tare amma fitarta ita daya nagani,toh da safe da na tashi ganin har lokacin fitansa yayi bai fito ba shine na bi bayansa inda na tarar da gawansa shine nayi wuri na kira jami'an tsaro" wani murmushi Abbas yayi sannan yace "na tabbata ka ga fuskar wannan yarinyar" "sosai naga fuskarta" ya bashi amsa "ai gidan alhaji Abdulkadir ko dare ma rana ne dan akwai wuta a ko ina wanda hakan ya bani daman ganin fuskarta" dan juyowa Barrister Abbas yayi sannan yace "mallam Abdulrauf inaso ka duba cikin kotun nan ko kaga wanda tayi kama da wannan budurwan" hannu ya daga ya nuno Juwairah wanda a take taji hawaye ya fara taruwa a idonta, "wani shu'umin murmushi barrister Abbas yayi sannan ya juyo yace " Ya mai girma mai shari'a a ranar da aka kashe wannan attajiri munada labarin cewa Juwairah taje conference dubai kuma an samu chat nasu da wannan bawan Allah sai dai ta dan canza suna dan kar a ganeta, amma bata fi karfin hukuma ba dan an gano sun jima suna tare kafun har ta samu damar kasheshi

YOU ARE READING
Rikitaccen Al'amari
Мистикаlabari akan yadda abun son dunia yasa yaya ta salwantar da rayuwar kanwarta