Karshe

2.3K 118 10
                                        

*RIKITACCEN AL'AMARI*
~A short story~
~Inspired by true life events~

*Na Billy Ladan*

*END*

*Dedicated to Hauwa Suleiman Muhammad*

bintladan.blogspot.com

Kusan Minti biyar kenan Judge Sharifa na dafe da kanta tana tunanin yanda zata bullowa wannan *Rikitaccen Al'amarin* can ta sauke wani ajiyar zucia tareda dagowa, gyaran murya tayi sannan tace "koh Bintalo da Bashir na cikin wannan kotu? Kai kawai Barrister Shureim ya gyada hakan yasa tace "toh kotu na bukatar su fito gaban kotu yanxun nan".
A take aka fito dasu suka tsaya wajen amsa tambaya, Qur'ani aka miko wa Bintalo amma ko kallonsa batayi ba, dagowa tayi ta dubi Sharifa tace "ba sai na rantse ba wlhy zan fadi gaskia ko dan samu amun sassaucin shari'a, murmushi kawai shari'a ta mata, kallon Bashir tayi da yake ta mata idanu alamar kar ta fada amma sai ma wani harara da ta watsa mai ta juyo ta fara bayani dan ita bata ji zata iya shiga prison ba "wato ya mai girma mai shari'a wannan abu ya fara ne tun bayan aurena da Bashir da yan watanni inda yake shaida mun ana son kara mai matsayi a gun aiki sai dai malaminsa yace zai iya rasa wannan matsayi da har ma aikinsa baki daya, jin haka ya tada hankalina dan na kasance mai son abin dunia dan yana daya daga cikin dalilan da yasa na auri Bashir dama bawai sonsa nake ba, nan na shiga tambayarsa koh akwai abinda zamu iya yi dan ganin bai rasa aikinsa ba inda yake shaida mun cewar malaminsa yace lallai sai ya sadu da yarinya karama wanda kuma ya tabbatar bayan ita ba mai kusantarta, nan na bazama neman yarinya karama wanda zan dauko a matsayin yar aiki daga nan mu aikata mugun nufin mu a kanta amma hakan ya gagara. Kwatsam watarana yace in shirya muje Kauyenmu dan yana so yaga malaminsa nikuma sai na duba gida,isarmu ko gida bnje ba na bisa wajen malamin nasa inda a gabana yace dole yarinyar da zai kusanta ta zamto jininace ita ko nasa, nan ya nuna cewa shi kaf danginsu ba yar yarinya mai shekarun da ake bukata, ko kadan bn kawo Juwairah a raina ba amma jin abunda Malamin ne ke ambata akan cewa zamu samu in har wannan aiki yayi kyau nan na yanke hukuncin dauko Juwairah in zan bar kauyen, ko da na tashi tafia gida bn yadda munje da Bashir ba gudun kar a zargi wani abun, ko da nayi wa inna maganar tafia da Juwairah sam bata yadda ba hakan yasa na kira Bashir na gaya masa wanda a take yasa malaminsa ya mana aiki da ya sa dole su Inna suka bamu ita, satinta daya da fara zamanta da mu na biyewa mijina ya raba kanwata da budurcinta saboda son abin dunia da yayi mun yawa, a farko abun ya so ya dameni amma ganin yanda kudade ke shigowa ya sa na manta da komai muka cigaba da aikatar da mugun nufinmu akanta,wannan shine gaskiyar al'amarin da fatan baza a yanke mun hukunci mai tsauri ba,wlhy na tuba, sharrin zucia ne da kuma munafurcin mijina shi ya zugani, a taimaka kar a kaini prison" ta karashe tana goge dan guntun hawayenta.

Bashir kam duk jikinsa yayi sanyi dan ya kasa dago kansa,ko da Sharifa ta fara tambayarsa kansa a kasa yake amsa mata, ba musu ya amsa laifinsa. Suna tsaye awajen har Judge Sharifa ta gama yar rubuce rubucenta ta dago tace "bisa kwakwarran shaidu da dalilai wannan kotu mai adalci ta wanke Juwairah daga tuhumar kisa da ake mata dan ta yisu ne yayinda bata cikin hayyacinta a dalilin mental condition da ke damunta

And according to shari'a an insane person can't be held accountable for his actions, kuma na yadda da opinion in Dr Abdulmajeed and my final decision rest at Juwairah is not guilty by reason of insanity so Dr Abdulmajeed zai tafi da ita psychiatric facility dan aje a bata kulawan da ya kamata har zuwa time da zata warke. And you, ta fada tana kallon Bashir "kotu ta yanke ma hukunci dauri with hard labor har na tsawon shekaru ashirin ke kuma Bintalo bisa wasu dalilai kotu ta yanke miki shekaru 10 kema with hard labor, d court is now adjourned" ta karashe tare da tashi, kallon side na Shureim tayi ta dan yi bowing kanta tareda mouthing congratulations, murmushi shima ya mata sannan ya maida hankalinsa kan su Bintalo da aketa tsalle ana ihun an shiga uku, kwace kanta tayi ta nufi gunsu Inna ta durkusa tana neman yafiyarsu amma ba wanda ya dago ya kalleta, har aka zo aka dagata aka fice da ita. Tashi Inna sukayi suka karasa gun Juwairah, tana ganinta ta karasa ta fada jikinta tana kuka mai cin rai dan yanxu ta tuno komai she dnt hv to hold it in anymore, mutane sai tausaya mata suke yayinda ake Allah wadai da hali irin na Bintalo. Rike da hannun juna suka fito harabar kotun inda suka ga har yanxu ba a tafi da su Bintalo ba dan ta tsaya sai Allah ya isa taketa aikawa Bashir tareda cewan saiya saketa dan ko ta fito bazata jirasa ba aurenta zata yi, wani daria yayi sannan yace "wlh sai dai ki mutu dan ni da ke mutu ka raba takalmin kaza kuma jira dole kiyi in fito mu sha talaucinmu tare" yin kansa tayi kaman zata dokesa akayi saurin sa shi a mota, tana ganin su Juwairah sun fito ta yo kansu ta durkushe gabansu tareda riko kafar Inna "Inna ki dubeni da idon Rahama kar ki gujeni a halin da nake, wlh nayi nadamar abunda na aikata ku yafemun ko zanji sauki a raina" batareda ta kalleta ba tace "Bintalo kinga irin abunda muke guje miki kenan amma kika kasa gani son abun dunia ya rufe miki ido kika auri wanda baki gama sanin halinsa ba har ya kaiki ga hanyar halaka, ban taba sanin za a iya hada baki a cuci wani da ke ba sai gashi kin nuna mun akan yar uwarki wanda kuka fito ciki daya da ita, bazan taba Yafe miki ba Bintalo bisa wannan abu da kika aikata wa Juwairahta kin ha'inceta kin cutarta da ita tun bata mallaki hankalin kanta ba sabida son abun dunia naki, nida hukuncin kisa aka daura miki da yafi mun dan shine kadai nake ji zai yaye mun bakin cikinki a raina, amma duk da haka zaki gani dan rayuwar kurkuku kadai ya isa kiyi hankali sannan duk ranar da kika fito kar ki yadda ki dawo gida, ki nemi wasu iyayen daban amma bamu ba" Abba ma kara jaddada maganar Inna na karshe yayi sannan ya bi bayar Inna aka barta daga ita sai Juwairah, dagota tayi daga durkushen da take sannan ta dubeta tace "koh ba komai Adda kin cika mun burina na rayuwa amma hakan bazai hanani ganin illar da kikayi wa rayuwata ba, bazan ce na yafe ba kuma bazan iya cewa ban yafe ba sai dai ga shawara, a zamanki a kurkuku kiyi kokari ki gyara tsakaninki da ubangijinki, ki nemi yafiyarsa sannan ki yawaita istigfari hakan zai kawo miki saukin halin da kike ciki" tana gama fadin haka ta juya itama ta barta tsaye a wajen, sosai take son Bintalo kuma take tausayinta sai dai tayi abunda baxata iya yafe mata a yanxu ba ko ta nuna mata tausayinta da take ji, taji dadin tafiyar da zatayi da Dr Abdulmajeed dan ko ba komai zata manta wasu abubuwan.

Rikitaccen Al'amariWhere stories live. Discover now