Babi na bakwai

1.5K 87 1
                                    

*RIKITACCEN AL'AMARI*
~A short story~
~Inspired by true life events~

*Na Billy Ladan*

*Dedicated to Hauwa Suleiman Muhammad*


bintladan.blogspot.com

_To any Psychiatric Medicine/Nursing Freak out there like me n my Kawa Hauwa Suleiman,dis page is urs_

Murmushi Dr Abdulmajeed yayi sannan yace "toh sannu malama Juwi, inaso ki gayamin......"
Kan ma ya karasa ta daga mai hannu tareda cewa "kaga Dr waye kake da suna" "Dr Abdulmajeed" ya tayata fada, tabe baki yayi sannan yace "wateva, ni ba wani dogon surutu nake so just get me out of this stinky place"
Ajiyar zucia Dr Abdulmajeed yayi sannan yace "eh zamu cireki amma meh kika sani gameda murder cases da ake tuhumar Juwairah? "Not much" ta fada tana wani cin magani, kallon juna Shureim da Dr Abdulmajeed sukayi sannan yace "toh munaso mu san abunda kika sani" kan ta sake basu amsa sai suka ga fuskarta ya sake canjawa ya dauki wani cooler form, a hankali Dr Abdulmajeed ya kira sunan Juwairah sai gashi a hankali ta bude ido ta saukesu cikin na Dr Abdulmajeed, murmushi ta sakar mai kafun ta fara magana cikin muryanta mai sanyi "haryanxu ba ita bace ni sunana Riya" Shureim ji yayi kaman ya fice ya bar dakin dan abun ya fara tsoratasa, gashi dai kana ganin Juwairah zaune saidai yanayin fuskarta da maganarta kadai zai nuna ma ba ita bace, abun ya zamto mishi tamkar shirin film, juyowa yayi ya kalli Dr Abdulmajeed murya can kasa yace "aljanu takeda ko? Murmushi ya mishi sannan yace "dey r called *Alters* zanma bayani anjima" sannan ya juyo gun Riya yace "Riya ku nawane? " Mu biyune kawai,daga ni sai Juwi" ta mayar masa
"Ok,inaso ki gaya mun abinda kika sani gameda kisan da ake tuhumar juwairah da cewar ta aikata" ta budi baki zata mayar suka ga fuskarta ya sake canzawa, yatsina fuska tayi ko bata fada ba sun san Juwi ce dan itace meh rashin kunyar "kuna bata lokacinku ne, Riya bata san komai akan kisar nan ba, ni zaku tambaya" dan murmushi Dr yayi sannan yace "toh muna jinki Juwi" dan mika tayi tana hamma sannan ta koma ta kwanta tayi luf da idonta, kiranta Dr Abdulmajeed ya shiga yi amma shiru,kallon Shureim yayi sannan yace "sun tafi kuman bn jin zasu sake dawowa,so zan tadata, matsowa yayi kusa da Juwairah yace "Juwairah yanxu zan tadaki,zan irga from one to five at d count of five zaki farka" nan ya shiga irge har ya zo 5 sai gashi ta bude ido a hankali, kallonsu tayi sannan tace "kun sami wani abu ne? Murmushi kawai Dr Abdulmajeed yayi mata sannan yace "ki dan huta for sum minutes sai in dawo muyi magana" kai kawai ta gyada sannan ya ma Shureim ido suka fita

Suna fita suka dan nemi waje suka zauna sannan Dr Abdulmajeed ya fara magana "kamar yanda nayi suspecting case na Juwairah Psychiatric case ne, ka taba jin abunda ake kira multiple personality disorder ko split personality ko dissociative disorder? Kai Shureim ya kada alamar a'a, shiru Dr Abdulmajeed yayi dan bai san ta ina zai fara mai bayani ba, can ya dago yace "wato multiple personality disorder wani condition ne da several personalities suke taruwa a jikin mutum daya, in her case biyu take da shi but ana iya samu fiye da hakan har mai 200 personalities ma an taba samu a jikin mutum daya, yawanci yana faruwane dalilin wani trauma da ya sami mutum a kuruciyarsa, toh wannan mummunan abu da ya sami yaro a kuruciyarsa sai kaga hankali da zuciyarsa bazata iya dauka ba sabida yanada ciwo kuma yakan tada hankali, gudun haka sai yaro ya zabi ya binne wannan mummunar abu da ta samesa ta hanyar creating wani personality a jikinsa da zai tayasa mantawa da wannan event in, wannan personalities su psychiatrist ke kira *alters* ,in English in ance alter ana nufin ka canza ko ka sake, toh dts wat happen ta sake creating wani ita ajikinta dan ya tayata binne abunda ya sameta wannda ba mu san ko menene ba, but usually yana faruwa due to molestation ko kuma lost of a loved one duk kan iya jawo hakan, an ka gansu da kanka su biyune jikinta and ba lokaci daya aka haifansu ba, usually daya at a time, bayan anyi creating first one in similar trauma ya sake faruwa toh sai a sake creating wani n usually suna sanin junansu ita host ince baxata san da su ba har sai mu psychiatrist mun shigo ciki" ajiyar zuciya Shureim yayi dan jin abun yake kaman a mafarki dagowa yayi ya dubi Dr Abdulmajeed yace "Is it common? Kai ya gyada alamar eh sannan ya kara da cewa "recently an samu case na mai two personalities a Korea n i was privilege to c him" kallon dakinta Shureim yayi tareda cewa "but she seems normal" gyada kai Dr Abdulmajeed yayi sannan yace "Masu split personality seem normal har sai alter insu yayi taking ova Wanda zai iya lasting days ko sati ko wata ma sumtimes kuma host in bazai taba sani ba, shi dai zai na ji kaman ya manta wani part na rayuwarsa zai zamto kamar an mai wiping memory, bazai taba tuna abunda ya faru ba, n mostly alters suna samun sunansu ne daga sunan host in, kaga in her case Juwi/Riya= Juwairiya" tsorone ya bayyana fuskar Shureim sannan yace "kana nufin Juwairah ita tayi kisan? Shiru Dr yayi sannan yace "its inconclusive, but bazan ce ita tayi ba sai dai muce her alters did, its eida Juwi ce ta aikata ko Riya but dole mu sake ji daga garesu dan jin wa ya aikata tareda jin dalilin da yasa Juwi da Riya suka ginu a jikinta, sune kadai zasu san mummunan abunda ya sameta a kuruciyarta dan ita bazata tuna yanxu ba.

Hannu Shureim ya sa ya dafe kansa "yanxu ya zan kare wannan case a kotu, ai sai suce hauka nake kuma judge da zatayi case innan bata wasa gashi opponent ina ya san aikinsa, bai taba daukan case ya fadi ba, banji dey wil buy abunda zan fada ba" dafasa Dr Abdulmajeed yayi tareda cewa "sai kace ba Lawyer ba, kar ka karaya tun yanxu, d case is even simple, u just make an insanity plea"

Kallonsa Shureim yayi tareda sakin murmushi yace "kaga har ka fini sanin aikina, abunda zanyi kenan, zamuyi pleading not guilty sabida mental condition inta, baza mu amsa laifin ba sabida ba a cikin hayyacinta ta aikata ba" hannu ya mika mai yace "nagode Dr ds case will b in our favor insha Allah" Tashi Dr yayi yace "yanxu taso muje mu shaida mata abunda muka samu kan muje mu taro shaidu da zasu bada shaida kan wannan ciwo da ba kowa ya sanshi ba" Tashi Shureim yayi suka nufi dakin da ake tsare Juwairah, inda suka barta nan suka sameta, ko da Dr Abdulmajeed ya mata bayani kuka ta hau yi, da kyar suka samu tayi shiru ko da suka tashi tafiya cewa tayi ita su kasheta dan in basu kasheta ba ita zata kashe kanta dan gudun kar ta sake wani kisan, dole suka koma suna bata baki amma ina ita ta dage sai dai su nemo mata abunda za ta kashe kanta da shi. Ganin haka yasa Dr Abdulmajeed cewa shi zai zauna da ita, duk da Shureim bai ji dadin hakan ba dole ya koma gida tunda shi yanada family, haka ya musu sallama ya barsu akan cewa zai dawo da sassafe dan gobe za shigar da ita kotu.

Yana fita bai jimaba Bintalo suka zo dasu Inna, banda kuka ba abunda Inna da Abba keyi, cikin kuka Juwairah tace "Inna ban aikata ba" Inna na kuka tace "haba Juwairah har sai kin fada,nafi kowa sanin ba ke kikayi ba", ganin kukan yayi yawa yasa aka maidata daki su kuwa suka koma gida.

Washegari da sassafe Barrister Shureim ya fito cikin shiri,bakaken suit ne jikinsa hannunsa kuwa brief case ne sai gown na lawyers da hulansa, dakin Quraiba ya nufa yaga bata ciki, falo ya nufo ya ganta tana jera abinci a dining, ji tayi an rungumeta ta baya ta dan dago tareda juyo fuskarta, bakinsa ya kai kan nata ya danyi kissing sannan yace "mrn habibti,u r so early today kuma gashi hr kin gama brkfast" juyowa tayi tareda mai murmushi sannan tace "how do u xpct me not b up wen nasan zaka fita da wuri" jawota yayi ya rungumeta tsam a jikinsa tareda cewa "shi yasa nakesonki habibti, duk dunia bnjin akwai wanda yayi sa'an mata irina" "i luv u too habibi" ta mayar mai sannan ta zaunar da shi ta zuba mai, sai da yaci yayi nak sannan yace ta dan zuba mai a flask na mutane biyu in akwai, murmushi tayi tareda tashi tayi yanda yace, ko bai fada ba tasan wa Juwairah zai kai sai dai yanxu ta daina kishi dan tasan her time is limited kuma ko da yanason Juwairah ta san haryanxu mijinta na sonta kuma bazai taba canja mata ba. Har wajen motarsa ta rakosa tareda mai fatan samun sa'a sannan ta koma.

Yana isa station kai tsaye dakin da aka tsare Juwairah ya shiga, zaune ya sameta ita da Dr Abdulmajeed suna hirarsu Juwairah har da dariyanta, bara kace ita za a shigar kotu ba, ransa ne yaji ya sosu ganin kusancinsu gashi sai wani washe baki take, kawar da abun yayi a ransa tareda karasawa ciki, dagowa sukayi suka amsa sallamarsa a tare sannan ya aje musu containers biyu da ya zo dashi, tashi Dr Abdulmajeed yayi tareda cewa "bari inje in shirya sai mun hadu a court room" har ya kai kofa Juwairah ta kirasa cikin siririyar muryanta, juyowa yayi suka kalli juna "Kar ka jima pls,inaso ya zamto kana can time da za a shigar dani" murmushi ya mata sannan yace "u can count on me hun,i wil surely b dia" sannan ya fice. Shureim ji yayi kirjinsa ya hau bugawa da sauri sauri yayinda ya fara jin wani abu gameda Dr Abdulmajeed a ransa, kar dai zancen Quraiba ya zamto gaskia, kar dai ya fara son Juwairah, kawar da kansa yayi tareda cewa kai it cant b. Kallonta yayi tana cin abincinta cikin kwanciyar hankali ya karasa ya zauna a gefenta, gyaran murya yayi ta dago ta kallesa, sai yanxu ta tuna basu gaisa ba, cikin jin kunya ta gaishesa, tabe baki yayi yace "bazan amsa ba,sai da sabon saurayinki ya tafi zaki kulani" ya fada yana kallonta, murmushin takaici tayi sannan tace "Barrister Shureim knan, a halin da nake ciki har kana gani inada lokacin soyayyane, kawai i feel at ease when am around him,dts ol n ntn more" ajiyar zucia yayi wanda ya sa Juwairah dagowa suka hada ido, kawar da kansa yayi tareda tashi yace "bari in barki ki karasa,zamu hadu a waje, i want you to b very careful a court room innan, kar ki yadda idon mutane ko opponent ina ya baki tsoro, nasan Barrister Abbas is cunny dnt let him get to u, n bana so ki kara komai akan abunda kika gaya mun, exactly shi zaki fada a court in aka tambayek, in kinyi hakan insha Allah baza mu samu matsala a kotu ba" gyada kai yayi sannan ya sa kai zai fice "Thank You Shureim" yaji ta fada, runtse idonsa yayi jin yanda Sunansa yayi dadi a kan harshenta, sa kai yayi ya ida fita daga dakin batareda ya juyo ko ya ce mata wani abu ba.

*Billy Ladan*

Rikitaccen Al'amariWhere stories live. Discover now