*RIKITACCEN AL'AMARI*
~A short story~
~Inspired by true life events~*Na Billy Ladan*
♻ *EXCLUSIVE WRITERS FORUM*
*Dedicated to Hauwa Suleiman Muhammad*
bintladan.blogspot.comA hankali ta bude idonta ta dubi inda take ta ga lalle cikin jirgine, runtse idonta tayi yayinda hawaye masu zafi suka fara gangarowa, Bintalo ce ta aje mujallar da ke hannunta tareda juyowa taga Juwairah na hawaye ,hannu ta sa ta dan tabata tareda fara mata magana a kasa kasa "Juwairah dan Allah ki bar kukan nan,kinga har mutane sun fara kallonmu, kiyi hakuri ki tsaida hawayenki har mu isa masaukinmu", hannu tasa ta share hawayenta yayinda take jin bakin cikin rabata da masoyinta da akayi dan taji a ranta sun rabu kenan. Jirginsu na sauka suka tari cab Bashir ya bashi address da zai kaisu, sai da suka shiga cikin gari taga posters sannan ta gane ashe Sudan suka zo. Har suka isa gidan bata tanka musu ba, akwatinta ta dauka ta wuce cikin gidan. Yanayin gidan exactly irin nasu na Nigeria ne hatta furnitures in iri daya. Sama Juwairah ta hau dan ko ba a gaya mata ba side nata kenan, tunda ta shiga ta kulle kanta a daki ta hau kuka sai da tayi mai isarta sannan ta jawo jakarta dan dauko wayarta, ganin wayan baya ciki ya sata sauka dan tambayar Bintalo, zaune ta samesu suna yar hiransu bata bi ta kan Bashir da ya kafeta da ido ba tace "Adda ina wayata? Kallon Bashir tayi ya dan kashe mata ido sannan ta maida kallonta ga Juwairah ta ce "ai garin sauri wlhy bn ma tuna na dauka miki ba", "bari yanxu in fita in nemo miki wani" cewar Bashir, "ban bukata" Juwairah ta mayar mai "kuma am not staying,am going back to Nigeria as soon as possible zan koma gun su Inna yafi mun da zaman da nake daku, u ppl r very selfish baku damu da kowa ba sai kanku kuka sani, me nayi muku da kuke son azabtar da zuciyata, kun rabani da mutanen da nakeso kun kawoni nan inda ban san kowa ba, toh wlhy ku sani bazan yi dare biyu a garinnan ba,ko kunki ko kun so am living" tana gama fadin haka ta juya ta hau sama, Bashir ne ya taso dan bin bayanta Bintalo ta rikosa tareda cewa "barta tukun, kai dai je ka nemo wayar na san meh zance mata. Tashi yayi ya fita bai jima ba sai gashi ya shigo da ledoji a hannunsa, aje mata yayi a gefenta sannan ya shige dakinsu. Bude ledan tayi taga takeaways ne da kuma waya da simcard. Takeaway daya ta dauka da drink ta haura sama da shi. Sai da tayi knocking dakin kusan sau uku sannan Juwairah ta zo ta bude mata tareda bata hanya ta shige sannan ta rufo kofar. Dan nesa da Bintalo ta zauna tareda kawar da kanta, "ga abinci da wayan na kawo miki Juwairah,nasan tabbas bamu kyauta ba but muna da dalili mai karfi na yin hakan, zamanmu a can ba karamin hatsari yake da ba dan ana farautar ran Bashir kuma hakan na nufin muma muna cikin hatsari dan kinga har gida an shigo, da ba dun Allah ya tsare ba da duk mun zama tarihi, kar ki manta halacci irin na Bashir, kiyi duba da sauyin rayuwa da kika samu a dalilinsa, da ba danshi ba da baki kai matsayin da kike a yau ba kuma yana kyautatawa iyayenki, ai ya cancanci ki sadaukar da rayuwanki na can saboda ceto rayuwarsa" ganin hawaye fuskar Juwairah ya sata murmushi dan tasan tayi nasara,tashi tayi ta dubeta tace "ki daure ki ci abincin sannan kiyi tunani akan abunda na fada, in kinga tafiyar shine yafi miki toh bazamu hanaki ba dan already ma har ya fara zancen karbo result naki ya nema miki aiki anan,so zabi na gareki" tana gama fadin hakan ta fita tareda rufo mata kofar. Tashi Juwairah tayi ta hada wayar ta sa chargi dan ta kagu taji daga Nasir da kuma Meelat. Abincin ta jawo ta fara ci,sai da tayi nak sannan ta rufe sauran ta sauko dan shan ruwa.
Bintalo na ganinta tama Bashir ido suka bar hirar da suke, wucewa tayi ta bude fridge dake gefen dining na palon ta sha ruwa sannan ta dawo parlor inda suke zaune itama ta nemi waje a kasa ta zauna.
Shiru duka sukayi sai can Juwairah ta dago tace "uncle pls kayi hakuri a bisa abunda ya faru, insha Allah bazai sake faruwa ba" murmushi yayi sannan yace "bakomai Juwairah,kuma insha Allah muddun komai yayi normal zamu koma gida but for d mean time zamu zauna nan, zanyi magana da H.O.D inku ya turo mun to whom it may concern naki sai in nema miki aiki anan" godia tayi sannan ta tashi ta shige ciki yayinda Bashir da Bintalo suka kalli juna suka sakewa juna murmushi, ko me murmushin ke nufi oho.

YOU ARE READING
Rikitaccen Al'amari
Paranormallabari akan yadda abun son dunia yasa yaya ta salwantar da rayuwar kanwarta