*😭RAYUWAR KUNCII😭**written by MAYMOUNER2*
*CLEVERS WRITERS ASSOCIATION*
*Assalamu alikum jama'ah ga wani sabon book nazo mu ku dashi me suna ,,RAYUWAR KUNCII,, ku biyo ni danjin yanda book din zai kasance, dont forget to vote and comment love yhu all😘*
*Follow me on watpad*@*maymouner2*
*PAGE ONE*
kuka take yi me ratsa zuciyar me sauraro ganin kukan ba magani komai zai mata ta tashi tashiga toilet Alawala ta daura sannan tazo ta dauka dadduma sallah tayi raka'a biyu kafinan tayi wa mummy addu'ar allah y jiqanta y gafartama yasa mutuwa hutu ce a gareta kafin ta tashi daga kan sallayar ji tai anfara kiran sallah azahr hakan yasa ta miqe tayi sallar azahar din
tana cikin yin addua taji sallamar su mufeeda da mufeed sun dawo daga makaranta tunda ita tagama jss class yanxu jiran junior waec take ta tafi wata schl din,uniform dinsu tasa suka cire sanan ta umarce su da suyi wanka su yi sallah kafinan su ci abinci haka kuwa suka yi mufeed ne ya fito da verbal dinsa yace aunty zarah an bamu home work nan ta karba ta duba ta zauna ta koya masa yayi ya maida littafin cikin jakarsa mufeeda ma dauka nata tayi amma ita english ne haka ta koya mata sannan tace su shirya su tafi islamiyya
qofar dakinsu ta rufe sanan ta rufo qofar falon suka nufi hanyar fita.ke zahra'u ina zaku kika tusa su agaba kuka nufi hanyar qofar gida,yanda aka kira sunan nata saida duk su ukun suka tsorata juyawa sukai tace Ammi islamiyya zamuje ku kaka sani inma yawo zaku ai,dama garin tsallaka titi mota ta murqushe ku na huta gaba daya,
Allah ya karemu tafada a hankali yanda ammi bazata ji ba mufeed da mufeeda suka ce Ameen sannan suka tafi abunsa,lokacin dasukaje zasu tsallaka titin hannunsu takama sosai sai ta tabbatar babu komai kan titin kafin suka tsallaka haka suka qarasa islamiyya su mufeed suka wuce ajin su zarah ma ta tafi nata ajin,tana shiga ta ga fauza kusa da ita taje suka zauna suka fara karatu kafin mallam yazo ya karbi hadda ba su dade ba kuwa ya qaraso haka akafara karbar hadda wanda yayi daidai ya tafi wanda kuma ya kasa bulala uku (3) ce da wankin bandaki saboda haka kowa yake qoqarin bada haddar sa daida,
bayan an fito anyi sallah ankoma aji hadisi da sira aka musu lokachin tashi yayi aka tashe su fitowar su keda wuya ita da fauza saiga su mufeed sun zo qofar ajinsu suna jiran auntyn tasu wato zarah nan sukai sallama da fauza tasa su gaba suka nufi hanyar gida suna isa ana kiran magriba nan danan tayi sallah ta daura abinci jallof din macoroni ta musu kamshin duk y hade wajan saboda mummy ta koya mata girke girke tn tana jss1 shiyasa duk lokacin datayi saidai kaji qamshi na tashi,nan ta zuba musu sukaci kafinan kowa y dauka Alqur'ani ya maimaita inda aka qara musu a islamiyyar inda su mufeed suka kasa zahrah ta biya musu,
Suna cikin karatun aka kira sallahr ishaa,nan duk sukaje sukayi sallah addua suka yiwa mumynsu addua sanan suka dan yi hira zahrah ta basu labari mufeed da mufeeda ko hadda da dariya nan dai suka fara jin bacci mufeed y shimfida katifa aqasa mufeeda da zarah suka hau kan gado nan tasa kowa yai addua kafin kace me barawo bacci yai gaba dasu amma banda zarah da sai tunanin duniya take tana tunanin ya rayuwar su zata kaya su da Ammi.
dont forget to vote, comment and share it with ur frnds.......
hope you start enjoying"""""*✍️Edited by maman shukhrah✍️*
YOU ARE READING
RAYUWAR KUNCII
General FictionShow some love by commenting and voting each chapter Labarin yarinya Fatima da qannanta wanda suka tashi cikin kuncin rayuwa da gallazawa. Just follow my pen for I assure u,you are going to fall for this book