CHAPTER 4

25 2 0
                                    

*😭RAYUWAR KUNCII😭*

*written by MAYMOUNER2*

*CLEVERS WRITERS ASSOCIATION*

*Follow me on watpad*@*maymouner2*

*PAGE FOUR*

Bangaren hajiya bilkisu kuwa Dakyar ta tashi tayi sallah kafinan bacci yayi gaba da ita,bataji dawowar Alh ba sai kawai juyi tayi taganshi yana bacci domin lokachin dare yayi sosai, addua tayi sanan ta cigaba da yin baccinta.

Bayan tayi sallar asuba ba ita tashi ba sai wajan qarfe 11 na safe,takarda tagani ajiya gefanta tana budewa taga note ne alh ya rubuta mata murmushi tayi da ta karanta abunda ke ciki kafinan ta ajiye takarda.
sallamar hajiya ruqayya taji hakan yasa ta fito palor abinci ne ta kawo mata sanan ta dauko cup ta hada mata tea,nan tasa taci abincin sosai sanan tasha magani,Allay ya sawaqe ta mata sanan ta fita ta tafi part dinta.

ganin haj ruqayya ke dawainiya sosai da haj bikisu yasa alh ya yanke shawarar dauko mai aiki don ta dinga taya ta,haka kuwa aka yi.

a kwana a tashi cikin haj bilkisu ya cika wata tara nan fa tafara nakuda ba shiri suka kama hanyar asibiti,suna zuwa aka nufi labour room da ita zufa ce ta rufe ta sai nishi take ruwa aka daura mata ba a dade ba sai ga shi ta haihu hamdallah tayi tagode wa Allah sanan nurse din tayi qoqarin gyara mata babyn miqamata babyn tayi tace mata kin samu baby girl murna sosai tayi sanna aka fita da ita zuwa dakin daza ta huta kafin a sallame su tunda bata samu matsala ba

Alh ne ya tabka tagumi yana jiran yaji bikisu ta haihu aikuwa saiga haj ruqayya nan tazo tamasa da Albishir da ta haihu lafiya kuma an samu mace,sosai alhaji yaji dadi.
zuwa dakin datake yayi ya dauki jaririyar yamata khuduba sanan ya tauna dabino ya bata ya dan zuba mata zam-zam kadan tasha,sannu ya qara yiwa hajiya bilkisu sannu ya tambayi babu abinda ke damunta tace masa ehh kawai de ciwon jiki ne,basu dade ba kuwa nurse ta sallamesu suka kama hanyar gida.

ranar suna aka sawa yariya FATIMA saboda haj bilkisu na qaunar sunan amma suna ce mata zarah.

anyi shagali sosai ranar sunan nan,don duk wanda yazo yaci ya qoshi don wasu har da abinci suka tafi gidajensu dashi.
SO da qauna ba irin wanda Alh baya nuna wa diyarsa wato fatima don wataran har qin fita wajan aiki yake saboda zarah wai shi lallai shine zai dinga rainon ta
hakan baqaramin batawa haj ruqayya rai yake ba don cewa take akan wanan labibiyar yarinyar zai dinga barin akinsa yana zaman raino.

sosai zarah ta saba dashi domin da ta ganshi zata fara daga hannu alamar ya dauke ta,haka suka ci gaba da zama amma haj ruqayya tafara chanja halayenta saboda tana ganin kaman yanzu alhaji yafi son haj ruqayya saboda tana da ''ya.

haka dai suka cigaba da zaman su haj bilkusu nayiwa haj ruqayya biyayya amma tana gwasale ta bata ganin abunda take mata hakan yasa tafita daga sabgarta.

shekarar zarah hudu aka sata a farhan international school,kullum alh ne yake kaita idan lokaci tashi yayi yaje ya dauko ta waishi bai yadda driver ya dinga kaita ba.

zarah tana shekara biyar haj bilkisu ta sake haihuwa,Allah ya albarkace ta da yan biyu mace da namiji amma wanan lokacin ko kallan inda haj bilkisu take batayi ba sai cika tana batsewa da takeyi tanata surutai shikenan daga zuwanta tafara tara ''yaya duk dukiyar alh zata zama tata da yaranta to wallahi ba zai yi wuba sai nasan yadda nayi naga bayan ta

idan tabar duniyar naga ta yanda zata tara yara balle har dukiyar alh ta zama tasu.
tunda kuwa ubana ne yabawa alh jarin amma yanzu yana fin qarfin zama nawa mtsw wanan waccw irin rayuwa ce haka.

ranar suna akasa wa namiji Abubakar amma ana cemasa mufeed ita kuma ta macan khadija ana cemata mufeeda.

kyauta sosai alh yayiwa haj bilkisu itama haj ruqayya bai barta haka ba saida yayi mata kyautar,amma bawai taji dadi bane don ko godiya batayi ba.

haka suka ci gaba da zama a gidan nan haka amma alh bai fasa yimusu abunda yake musu ba.

sosai haj take kula da yayan ta don yanzu harsun fara tafiya.zarah kuwa ta qara girma,mai aiki ta nemi  da asamo mata don tadiga taya ta raino idan tana aiki haka kuwa aka samo mata wata yar matashiya don bata manyanta sosai ba.

tana da kirki saboda haka hajiya bilkisu take qaunarta.
rainon mufeed da mufeeda kawai takeyi mata se dan share-share amma duk wani sauran aiki haj bilkisu keyi kayanta

idan kuwa weekend ne babu makaranta tare suke shiga kitchen da zarah ta dinga cemata miqomin kaza bani kaza harda su barar magi take bata take yi mata

a bangaran hajiya ruqayya kuwa tunanin yadda zatayi da haj bikisu take domin idan bahaka tayi ba hankalin ta bazai kwanta ba dukiya zata zama bata ta ba.

sallamar da akayi ne ta katse mata tunanin datakeyi tana dago kai ta ga ashe wata qawar tace da suka dade basu hadu ba me suna Adama.
sosai tayi murna dazuwanta dan tasan ba qaramar makira bace yanzu zata kawo shawarar yanda zatayi ta kawar da haj bikisu batare da ta bata lokaci ba.maganar da adama tayine yasa ta dawo daga duniyar tunani

lafiya kuwa naganki duk kin fada kin rarrame ga shi na shigo naganki sai tunani kike yi haba qawata menene damuwar ki
ki fadamin ko menene anyi an gama.
kwallar munafirci ta fara sharawa kafinan tafara magana kamar hak

😍😘
please dont forget to vote and comments

*✍️edited by maman shukhrah✍️*

RAYUWAR KUNCIIOù les histoires vivent. Découvrez maintenant