*😭RAYUWAR KUNCII😭*
*written by MAYMOUNER2*
*CLEVERS WRITERS ASSOCIATION*
*Follow me on watpad*@*maymouner2*
*PAGE THREE*
Asabe na isa gida ta fara tunanin ya zatayi da kudinan cinye wa zata yi ko kuma zuwa zata yi ayiwa hajiya aiki,kawai sai ta yanke shawarar ta tafi qauyen su tunda dama akwai bikin yarta da za ayi datake qauye inya so idan ta dawo sai tacewa hajiya ta qaro kudin, dawanan shawarar dai ta yarda tafara shirye shirye akan gobe zata wuce qauyensu.
A bangaren hajiya ruqayya kuwa tana can tanata murna tunda za'aje wajan boka a hana yi mata kishiya(ni ko nace zaki ga hana kishiya lol)tashi tayi ta nufi daki tafara bacci harda munshari.sallamar Alh ibrahim ce ta farkar da ita tashi tayi fuska ba yabo ba fallasa ta masa sannu da zuwa bayan ya huta yaci abinci, haquri ya shiga bata akan auran da zai qara cewar sa bawai dan bakya haihuwa bane zan qara auran kawai dai zanyi ne inasanki wallahi murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo sanan tace shikenan ba komai a zuciyar ta kuma tana cewa naga ta yanda za'ayi auran tunda sunayan ku yayi wajan boka,tashi yayi yai wanka sanan itama yace ta shirya don su fita shopping ba musu taje ta shirya suka tafi shopping mall siyayya sosai yamata sanan suka nufi gida suna ta hira abunsu harda dariya bakace hajiyan da taita masifa bace dazu.
yau ya rage saura kwana uku daurin auran Alh ibrahim da Amaryarsa hajiya bilkisu,shirye shiryw sosai Alh yake yi saboda auransa na farko baisan wani wahalar sa ba.
A bangaran su hajiya bilkisu kuwa yau ne za ayi kamu amarya tayi kyau sosai kamshi ta ko ina kuwa tashi yake, bayan sallah la'asar suka nufi wajan da zasuje suyi kamu,abun sai wanda yaga hall din yayi kyau sosai abun kuma ya tsaru sosai basu suka gama ba sai bayan sallar isha kowa ya nufi gida.
Ranar jumma'a akayi dinner da sauran event din baza'a rasa ba.
hajiya ruqayya hankalin ta ne ya tashi akan batajin labarin Alh ya janye maganar auran sa ba gashi har gobe daurin aure,mayafi ta zara ta nufi gidan asabe domin jin abunda yake wakana isarta keda wuya ta tarda ita bata nan gidan ma a kulle yake haushi ne da bacin rai ya kamata dole ta juyo ta dawo gidan ta fuska a daure ba annuri don bataqi taji shigowar alh yanzu ba ta ce yabata takardar ta don ita baza ta iya zama da kishiya baYau takama asabar wato ranar daurin aure Alh ibrahim banda washe baki ba abunda yake amma karkaso ganin haj ruqayya don fuskar nan ba kyan gani yanda take cika take batsewa don ko abincin safe wato breakfast bata bashi ba cewar ta wai amaryar sa ta bashi.
Hakan bai 6ata masa rai ba saboda yasan duk acikin kishi ne.
10:00am dai-dai aka dauran auran Alh ibrahim umar da haj bilkisu abubakar jama'a sun hallaci daurin aure sosai,anci abinci kala kala asha ma abunsha.
Bayan sallar isha aka kawo wa Alh amaryar sa bayan angama Allah sanyar alkhairi da zaman lafiya jama'a suka tafi gida jensu, Alh ibrahim ne ya shigo nasiha sosai yama haj bilkisu sanan yaje ya kira haj ruqayya ya tarasu a part din sa yamusu nasiha baki daya, ke haj ruqayya kece babba don haka ki riqe girmanki ke kuma bilkisu kimata biyayya don kuwa itace gaba dake ba matsala zanyi iya bakin qoqarina Alh,
To Allah yabani ikon yin Adalchi a tsakanin ku alh ibrahim ya fada ameen haj bilkisu tace amma haj ruqayya ko kala bata ce ba.Anan dai aka raba kwana akan za adinga yin kwana bibbiyu (2 days) tashi tayi tai ficewar ta bata ce musu ko qala ba.Alawa ya umarce su da suyi su sallah sanan su roqi Allah albarkar auran ya kuma kare su daga sharri dake cikinsa haka kuwa sukayi Addu'o i sosai sukai sanan sukaje suka ci abinci suka nufi bedroom.
ganin dai cika da batsewar da take bazai kaita ko ina ba ga asabe har yanzu bata dawo balle taji meke faruwa yasa ta dan sauqo suke mutunci da haj bilkisu kaman me,itama bada ganan ba biyayya sosai take mata,Alh yaji dadin hakan sosai don har kyautar motar yabawa kowacce cikinsu kuma yace idan suka cigaba da zaman lafiya haka zasu samu alheri sosai daga gareshi.
Akwana a tashi ranar hajiya bilkisu ta tashi zazzabi me zafi sai yunqurin amai datake amma ta kasa wani azbabban ciwon kai ne yake damunta haka yasan ko kofar daki bata samu ta leko ba tun safe ganin hakan ne yasa hajiya ruqayya ta leqa part dinta taga ko lafiya tunda Alh tun safe ya nufi kasuwa,tarar ta tayi a cikin barko tana barin sanyi ba shiri tace su tafi asibiti amma tunanin wanda zaiyi driven din su take yi kawai ta kira Alh ta sanar masa ba'a dade ba sai gashi ya iso Albarka clinic suka nufa suna zuwa aka karbe su hannu bibbiyu tambayoyi aka mata ta bada amsa nan akaje akayo gwaji aka tabbatar tana da juna biyu har na tsahon sati shida murna sosai Alh yayi jiyake kaman ya tashi sama don farin ciki sujjada yayi ya gode wa Allah da ya bashi.
gida suka dawo yaje ya siyo mata maganin da aka rubuta mata
kasa cin abinci tayi sai dai kawai tasha Tea sanan aka bata maganin, hajiya rukayya kuwa wucewa part dinta tayi tafara kuka tana maganganu a zuci, yanzu shikenan wadda tazo bayana ma har tasamu ciki amma ni kuma shiru yanzu kenan Alhaji zai dinga nuna wa bilkisu so fiye danni don yanzu tana dauke da cikin sa har na sati shida haka har baccin ya gaba da ita tana tunani kala kala.*✍️edited by maman shukhrah✍️*
YOU ARE READING
RAYUWAR KUNCII
General FictionShow some love by commenting and voting each chapter Labarin yarinya Fatima da qannanta wanda suka tashi cikin kuncin rayuwa da gallazawa. Just follow my pen for I assure u,you are going to fall for this book