CHAPTER 9

14 2 4
                                    

*RAYUWAR KUNCII😭*



*written by*
*MAYMOUNER2*

*CLEVERS*
*WRITERS*
*ASSOCIATION*

*Follow me on watpad*@*maymouner2



*PAGE NINE*

*Godiya marar adadi gareki maman shukurah,,,ngode sosai da irin gudumuwar da kike bani.Allah yasaka da alkhairi ameen*

Zarah na shiga parlour ta saki wasu zazzafan hawaye,
tayi kuka me isarta dan xuciyarta tae sanyii sanan ta tashi ta wanke fuskar ta,
taje gaban mudubi ta duba fuskar ta
taga fuskar tayi tayi jah ga shatun hannu a kwance kan kumatun tah,wasu sababbin hawayen ne suka sake zirarowa daga idunuwan tah,
Se tinanin mahaifiyarta ya taso mata tunda take mummy bata taba Marin ta bah,Abba mah haka,amma AMMI ta maida fuskar ta kamar ba komai bah,bbu abinda yafi mata dadi kamar ta mare ta seta sake fashewa da kuka da ta tina yadda sukeyin rayuwuwarsu wani sabon kuka take tana shiasshika se da tafi minti 40 tana abu daya,
kanta taji ya daure ya fara wani zazzafan ciwo,da kyar ta tashi taje ta wanke fuskarta,
man zaitun ta shafa a fuskar yanda shatun
yatsun ze baje kar su Mufeeda idan sun dawo sugani,
tana gama shafawa kwanciya tayi wani wahalallan bacci yai gaba da ita.

Su Mufeed ne suka shigo da gudu suna dariya,ko sallama basuyi bah,shiru basuga auntyn tah su ba, suna shiga daki suka ganta tanata bacci,Mufeeda CE taje zata tasheta,tana tabata kuwa taji jikinta zafi kau,
Mufeed zo kaji jikin aunty Zarah zafi,
yana tabawa yaji zafi sosai,
juyi Zarah zatayi tana bude ido tagansu kanta jungum jungum,
murmushin dole ta qaqaro Wanda yafi kuka ciwo,tace twins din mu yaushe kuka dawo, inata bacci banji shigowar Ku bah,
kanta ne yai wani irin sarawa,riqe kan tayi tace ya Allah,
Mufeed ne yace bakida lafiya koh aunty,
jikinki zafi,Mufeeda tace face dinki mah duk tayi wani iri,yar karamar dariya,Zarah tayi wadda bataje ciki bah,tace musu lafiya tah qlau,
kaina ne yakeson yimin ciwo,
amma da munci abnci zansha magani se kuga ya dena ciwon,
to sannu,
Allah ya sawwake suka hada baki suka fada,
tace amin,
tunowa tayi bata qarasa wanke wanken da takeyi bah,tashi tayi zataje ta qarasa Mufeeda tace ki kwanta ki huta mana,
dariya tayi tace ai basu da yawa yanzu zanje na qarasa,Mufeeda tace ki bari zanyi toh,Zarah tace a'a karki jika jikinki, idan kikai wanke² haka jikinki yake jikewa kizo ki tayin mura,tashi tayi ta qarasa wanke².

Parlour suka fito suka zauna duk sunyi shiru bbu me cewa komai,Zarah CE ta tmbyesu yau bbu homework ne,Mufeed yace yayi nasa tun a schl,Mufeeda tace nikm bbu,yau auntyn mu batazo schl din ba mah.
Fridge Mufeed ya bude ze dauki drink yaga bbu,Zarah tace me kknema cikin fridge yace bbu komai,tace bakujin yunwa ne yau,banji kuna Neman abinci bah,Mufeeda tace nikam banaji ynzu de,amma idan naji zansha cornflakes anjima,Mufeed yace Nima,Zarah tace wanne irin cornflakes da ranar nan,gwara a dafa abinci kawae, haba aunty Zarah ke da kanki yake ciwo wanne Irin abinci kuma,kawai ki bari ba se kin dafa komai bah,
toh shikenan da dare an dafa wani abun ai,tashi tayi ta Shiga daki ta bar su Mufeeda parlor suna kallo,tausayin Kansu ne ya kamata,tace da mummy tananan da yanzu suna zauna hanakali kwance,ba ruwansu da AMMI balle ta dinga zalintar su,
hawaye ne ya gangaro mata
data tuna Marin da AMMI ta wanka mata dazu,hannu tasa tana share hawayen Mufeed ya shigo,sauri tayi ta juya kanta kar ya ganta,Ashe ya gani,Mufeed ne yace aunty ki dena kuka,idan kina kuka kanki ze qara yin ciwo fah,shiru tayi kamar me bacci,
ya dauki abinda yazo dauka yaje yai jugum a gefenta,yaqi komawa parlor.
Knocking din kofa, akai Mufeeda CE ta bude taga drivern su Abbane,
gaisheshi tayi,
Seya tmbyeta ina fadimatu tace tana daki kanta ke ciwo,
yace to dama kaya ne alhaji yace a kawo muku,idan nazo nayiwa fadimatu magana ta bude qofar baya a saka su cikin store,tace to bari na mata magana,shiga tayi taga Mufeed na bacci itama Zarah haka,bata tashesu bah tazo tace masa bacci takeyi,kawai a shigo dasu tanan,kayan abinci ne sosai aka siyo musu,ya gama shigowa dasu ya tafi.....
Time Mufeeda ta duba taga lokacin islamiyya yayi amma Zarah da Mufeed still basu tashi bah,sallah tayi itama ta samu waje ta kwanta abunta,se kusan biyar sanan Zarah ta tashi,tunawa tayi batayi la'asar bah,tashi tayi tai sallah,motsi taji a parlor, fitowa tayi taga Waye aikuwa taga AMMI a zaune kan kujera,AMMI barka da yamma,shiru AMMI tayi batace komai,gabanta ne yadan fadi,magana ta sake mata amma bata kula ta bah,zagyawa tayi zata wuce kitchen santsi ya kwashe se gata dum a qasa,Mufeed ne ya zabura ya fito yaga AMMI zauna ko kallon Inda Zarah take batayi bah,yai sauri ya qarasa wajan,sannu aunty Zarah,sannu kinji,garin yaya kika fadi,zafi sosai Zarah taji amma ta maxe tace santsi ya kwasheni amma ai banji ciwo bah,
AMMI tashi tayi ta fice abunta,ko kallon su Zarah batayi bah.Zarah tace Mufeed ya dauko mata mopper ta goge wajan,tana gogewa taga yauqi yauqi wajan data ke gogewa,tunanin ruwan me take chan taga "yayan kubewa a gefe,shiru tayi tana tunanin ina suka sami kubewa,itada tasan basuda ita,qarasa gogewa tayi ta qara share wajen.
Hajiya rukayya na fita tayi murmushin mugunta,banso yarinyar nan iya buguwa kawai tai bah ai,naso ace karyewa tayi naga ta munafirci,
ta kada kai tai shigewarta ciki......

Alhaji na dawowa ya nufo part din su Zarah,yana shigowa mufeed yaje da gudu ya dane shi yana masa oyoyo,Abba sannu da zuwa,INA fadimatu Abba ya tamabya,tana daki
da kansa ya shiga dakin ya ganta kwance,da aboniki kusa da ita.sauri tayi ta tashi zaune Abba sannu da zuwa,yawwa sannu fadimatu,me kullum kina cikin daki,duk idan na dawo a daki nake samunki,
Zarah murmushi tayi kawai,Mufeed ne ya shigo yace Abba yau kanta fah ciwo yaitayi,kuma dazu santsi ya kwasheta ta fadi ta bugu a qasa,ya salam,Abba ya fada,tashi muje asibiti,kanki na ciwo amma kikai shiru baki fadamn bah,Zarah tace Abba ai ya dena tunda na tashi daga bacci,kuma Inda na bugu na shafa aboniki,base munje asibiti bah,toh sannu Allah ya qara sauqi Abban ya fada.kunci abinci ne,Mufeed yace a'a,meyesa toh,kanta yake ciwo se mukace ta bari zamusha cornflakes. Abba yace lami din bata dawo bah kenan Mufeed yace ehh,
Yoghurt da hanta da ya suyo musu ya basu yace ga wannan kuje kuci toh, idan zaku kwanta kuyi addu'a....se da safe.sukace Allah ya kaimu Abba mungode,
Part din hajiya rukayya ya tafi direct,fuskarsa bbu yabo bah fallasa,be sameta a parlor,yai zamansa kan kujera,
tunanin rayuwar yaransa yakeyi, ta ydd ze samar musu saukii da hutu kmr ko wane yaro dabara CE ta fadomasa,
tashi yayi ya qarasa inda hajiya rukayya take
Aah ,Alhaji ka dawo sannu da zuwa
ta fada tanavwata kisisina yawwa kawai yace yayi shiru,Alhaji lafiya kuwa ta tmbyeshi,
lfy qlau ya fada, ya sakeyin yin shiru,
Akaro na biyu
Se itama ta kyaleshii babu Wanda ya sake wa wani magana har tsahon mintuna,
hajiya CE tace nifa banson Irin wannan alhaji,idan wani abunne kawai ka fada,idan bakajin dadi ne mah toh ka fada anemii solution kawae kaxo kasanii agaba kayii jugum
Yanajinta yakii mata magana
Ganin hkn yasa ta tashi ta dauko masa ruwa,ta kawo masa
Ta koma ta kawo masa abinci,
Ya kalli abincin shekeke yace ya qoshi,
haba aalhaji wai meke faruwa ne,
Se kuma tae shiru a zuciyarta tace ko de Zarah CE ta fadamasa abinda ya faru dazu,
katse mata tunanin yayi wajan tmbyrta meya hana lami bata dawo bah,au dama alhaji saboda hakane har kaqi cin abinci kk shareni,ehh ya fada,
tace habaa alhaji ai ba'asi zaka fara ji tukun ba daure fuska bah,to naji,me ya hanata,tace ai lami aure za'a mata kwanan nan,tace gsky ayi haquri bazata dawo bah. Toh shknn alhaji ya fada.
Shiru suka sakeyi na wasu mintuna kafin Alhaji yace to hajiya ina son sanar dake akan zan QARA WANI AUREN saboda na samu me kulamin da "yaya nah,Dan kuwa ni ba mazaunin gida bane,
fadimatu ita kadae bazata iya kula da Kansu da tarbiyyarsu bah,tunda ke kinqi toh gwara na samo wadda zata kulamun da rayuwarsu kome nawa da nake nema dan rayuwarsu ta inganta ne ......DUM-DUM gaban hajiya Rukayya ya fadi.....

*✍️Edited by Maman shukhrah✍️*

RAYUWAR KUNCIIWhere stories live. Discover now