CHAPTER 2

221 17 1
                                    

*😭RAYUWAR KUNCII😭*

*written by MAYMOUNER2*

*CLEVERS WRITWRS ASDOCITION*

*Follow me on watpad*@*maymouner2*

*PAGE TWO*

Kiran sallah asuba ne ya tada ta Alawala tayo sanan ta tashi mufeed da mufeeda suma sukayi alwala masallaci mufeed ya nufa sukuma sukayi sallah a gida bayan an idar da sallah ne suka karanta alqur'an sanan kowa ya shafa addua shara mufeeda ta fara yi inda mufeed ya tafi ya wanke toilet sanan ya shiga wanka ita kuma zarah ta nufi kichen domin dafa musu abinda zasuci,baifi minti goma ba sai gashi ya fito daga wanka nan mufeeda ta shiga sanan suka zo suka sa uniform.
kafin qarfe bakwai na safe zarah tagama hada musu komai na breakfast don haka ta zuba musu suke ci,suna cikin ci ne dady ya shigo gaishe shi sukayi a tare sanan ya samu su Albarka nan yabawa zarah 5k yace ko zasu nemi wani abu sukuma yabawa kowa naira dari kudin break.
Nan dai dady yamusu sallama ya fita kasancewar aiyuka sun masa yawa idan ya fita wajan qarfe bakwai to sai wata bakwai da ya dawo gida.
。。。。。。。。。。。。

yau takama asabar dady yana gida bazai fita ba sai sha biyu 12am don haka yana dawo wa daga masallaci ya koma bacci Ammi ce ta zo part din su zarah to shegiya munafika me kika fadawa ubannaki har zaizo yadinga bata fuska yana min fada kamar wata 'yarsa wlh ban fada masa komai ni jiya ma bamu hadu da dady ba,kyasanta chan munafikar banza wlh koda wasa kika fadamasa na kori lami me rabani dake sai ya shirya, shiru tayi bata ce mata komai ba yi tai kaman zata doke ta sanan ta juyo tai ficewar ta daga dakin nasu.

ASALIN LABARIN
Alhaji ibrahim umar haifanfan garin dutse ne a jihar jigawa,shikadai Allah yabawa iyayensa tun cikinsa yana wata bakwai mahaifinsa ya rasu zokaga kuka wajan mamin sa,amma ba yanda ta iya sai dai idan ta tuno shi tamasa addua locakin da cikin ta yakai wata tara ne ra haifo dan ta na miji wanda ya ci sunan mahaifin ta wato ibrahim
akwana a tashi asarar mai rai har ibrahim ya soma girma mami kawai dan business dinta take yi dashi take ciyar dasu ta musu sutura ta biya masa kudin makaranta kai harma ta taimaki marasa karfi.
lokacacin da ibrahim yakai shekara goma sha 17 ne mahaifiyarsa tace ga garinku kuka kan yayi iya yinsa dan hadda suma, Bayan anyi sadakar bakwai ne wani aminin mahaifinsa me suna Alhaji yusif yazo yace masa zama shi kadai a cikin gidan nan bazai masa dadi ba don haka ya tattaro kayan sa ya koma gidan sa sai ya zauna a bq haka kuwa akayi.
Dama Alh yusuf nada yara ciki kuwa hadda sa'an sa don haka zaman gidan yake masa dadi haka duk abinda za ayiwa dan gida shima sai anyi masa ba nuna wareke a tsakaninsu
Alh yusif dan kasuwa ne babba yana da manya shaguna a kasuwar kwari dake garin kano ibrahim yanuna yansan kasuwanci hakan yasa yana gama diploma aka bude masa shago ya fara kasuwancinsa kuma Alhamdullilhi kasuwanci ya karbeshi.
ruqayya yar gidan Alhaji yusif ce itace babba a yaransa mata ganin ta dan data ne har tagama secondary schl Alhaji ya buqaci hada auranta ita da ibrahim amma yace bazai masu dole ba idan basa son junan su,lokacin da yazo wa da ummee wato matarsa labarin abunda yake shirin yi taji dadi sosai ba tare da bata lokaci ba aka sanar dasu abunda ake son yimusa dama ibrahim nasan ruqayya amma bai taba fadamata ita ma haka sun ji dadin hakan kowa cikin su yayi murna, bayan yan kwanaki kadan akasa ranar auran ibrahim da ruqayya.
yau takama Alhamis ranar akayi saku lalle na ruqayya washegari akayi shagalin biki ranar asabar aka daura aure aka kaita gidanta, Alhj yusif ne yayi komai dan shi ya gina musu gida ya zuba komai da suke buqata,ibrahim yaji dadi sosai yamasa godiya marar adadi.
soyayya sosai suke zuba wa kowa yana nuna yanda yake son dan uwansa zaman lafiya ko kaman me dan bakajin kansu ko fada sukai kamun kace me to zasu sulhunta a tsakanin su batare da wani yaji su ba.
haka suka cigaba da zaman su amma Allah ya bai bawa hajiya ruqayya haihuwa ba haryanzu gashi sun shude fin shekara goma hakane yasa suka je asibiti akan tabbatar da cewa ko lafiyar su qlau an tabbatar musu da cewa ko kwa qlau yake lokacine dai baiyi ba haka nan suka dawo kullum addua sauke Allah ya basu 'yaya.
Alhaji ibrahim ne ya zo wa da hajiya ruqayya zancan zai qara aure wani ihu tayi da kururuwa kamar wanda aka aiko mata da saqon mutuwa ita lallai ba'a isa amata kishiya ba ai munafirci ne don anga bata haihuwa, nan dai tagama masa rashin kunya yayi ficewar sa ya barmata gidan,shiryawa tayi takama hanyar gidansu domin sannar wa ummee abunda yake shirin faruwa hakuri ta bata sanan ta mata nasiha akan tayi haquri ai namiji mijin mata hudu badan ran ta yaso ba ta koma gidanta ranar.
salamu alaikum hajiya kina ciki naji kaman ba kowa a cikin gidan haka fito wa hajiya ruqayya tayi laa asabe kece a gidan nawa yau to ya mutan gidan naku, suna lafiya asabe tafada a takaice,hajiya yanaga kin dan rame kwana biyunnan haka ba dole na rame ba asabe kawai dan anga bana haihuwa shine wai Alhaji zai qara aure salati asabe ta hauyi sanan tace ta kwantar da hankalinta kar tadamu indai akwai kudi to magana ta wuce dan malamin ta babba ne idan yayi aiki to yayiwu aure kan baza ayi shi ba.
Kaman bazata yadda ba chan kuma tace to ba matsala yanzu me za'ayi kudi zaki kawo hajiya gobe da sassafe na tafi wajan malam tun kafin lokachi ya qure to shikenan bari nakawo miki shiga daki tayi batafi minti biyar sai gata sa bandir din naira 200 ta kawo mata tace kije da wannan inda wani abu da ake buqata sai kizo ki fadamin nan sukai sallama asabe ta tafi tana washa baki azuciyar ta kuma ta na tunanin anya bazata cinye kudinnan ba tace mata ananan ana yin aiki da wananan tunanin dai ta isa gida........

Dont forget to hit d orange star
comment and share it with ur love ones

*✍️Edited by maman shukrah✍️*

RAYUWAR KUNCIIWhere stories live. Discover now