Sha Daya

1.1K 155 25
                                    

Tashi tayi ta ajiye kundin sirrin a cikin wardrobe. Bata tsaya ko ina ba se sashin rufaida, tana zuwa ta rungume ta, addua take mata godiya, fadi take

 "kin tseratar da d'a na daga hallaka, Allah ne kadai ze biyaki".

Kuka sukai sosai sannan su ka yi shiru, hakan ya sake tayar da shauk'in son umair a zuciyarta. Barcin da batayi ba kenan ta kwanta cikin yaranta, tana addua har sulusin dare sannan ta tashi ta yi salloli da addua.

💔💔💔

Akwana a tashi shekaran Umair biyu da Rasuwa, rabon Rufaida da farinciki tun rasuwan Umair, Alh Zunnurain ya kafa mata maaikatan Zane zane , dukiyanta kuma massallatai da rijiyoyi ta gina duk d sunan Allah ya kai Rahma zuwa ga mijinta.

Zaune take ta na Zane, ba abinda ya  fado mata a rai se  sanda take da cikin khadija. 

Ranar hana ta Zane yayi, duk motsin da tayi yana manne da ita, alkaura da kalaman soyayya da dadadan kalamai

Kuka tasaki sosai,  ji takeyi kamar lokacin ne taji sak'on rasuwar Umair. 

"Rufaida me ke faruwa ne, yanzu takwara na yazo min wai gaki can kina kuka". Alhaji Usman ne ya tambaya.

A hankali ta dago kai tana kallonsu, nan taga duk sun riked'e sun zama mata Umair, murmushi ta saki tace " Buddy dama kana raye ka barni cikin wannan hali, please ka dawo min da farinciki na".

Hankalin Alh ya tashi, ya juya yaga wa take kira da sunan da umair kawai take kira dashi, nan shima sai yaga Umair ne ke masa murmushi. Kafin ya ankara sai jin shi yayi yace "Grand PA don Allah ka lallasan mun mummy na tayi shiru, ka bata hakuri please".

Nan ya gano ashe Zunnurain ne ba Umair ba, rungumarshi yayi yana hawaye yace "Rufaida daina kuka ga farincikin ki nan a gabanki. Allah bai d'auke mana Umair ba se da ya bamu waninsa, wanda zai so ki fiye da Umair, jininki, 'Danki, farincikinki, komi naki, kinga kuwa abin ki gode Allah ne".

Ajiyan zuciya ta saki tana share hawaye. Bai bar d'akin ba se da ya sata tayi alwala ta hau kan sallaya domin yin nafiloli ko zataji sanyi.

Yana fita parlour din Haj Safiyyah ya shiga nan ya iske su biyun da yaransu mata. Haj Jamila ce mai bayani, tana ganinsa tai shiru tana dariya.

"Me kuke tattaunawa ne, ba ko gayya". Ya fad'i yana mai karasowa ciki. Duk suka yi  dariya. Yaran suka gaida shi daya bayan daya. Kasancewa ya san da zuwansu, bai tsaya tambayarsu dalilin zuwansu ba.

"Gobe inshaaAllahu zan je India, dama saura kwana hudu ne tafiyar don ganin likita, dani da takwara na zamu wannan karan". 

Sukai masa fatan dacewa da kuma k'aruwan lafiya. Wasu na mamakin zuwansa da Zunnurain. 

Haj Jamila ce ta kasa boye mamakinta se da tace " Uwar me zakaje yi da wannan yaron, ko tun yanzu zaka daura sa akan iyayensa ta hanyar fifitashi, 'ya'ya mata ma ai rahama ne, kuma ma ai ba gadonka gareshi ba illa kai da keda na..."

"Uwarki zanje yi dashi Jamila". Nan ya katseta a fusace.

"Uwata fa kace Alhaji?"

"Na fad'i ko zaki rama ne, ni  ban san mai suka tsare miki ba, wannan kiyayya har ina. Duk abinda kikai ma Umair ina sane, amma kika gwada akan zunnurain zakisha mamaki na, angirma ba'a san an girma ba". Mtswww tsaki yaja ya fita ya barsu nan.

Yana fita Aisha ta kalli mahaifiyarta tace "Mama na rasa me kika tsare ma Alhaji  ne, se ya ta wulakanta ki, ko don yaga duk mu mata ne, wallahi zamu dauki mataki fa."

"Gaskiyarki Indo, ai wannan wariya da ake nuna mana ya isa haka, ko ba komi se da kika k'are haihuwa sannan aka karo aure, ba dan ba danba ai da se muce mun haife su." Cewar maimuna, babbar 'yar  Alh Usman.

"Wai meyasa bakwa son gaskiya, idan Mama ta rik'e kanta ai duk haka baze taso ba".

Kafin ta rufe bakinta Aisha ta daka mata tsawa " Wai Salma meyasa kike sallamammiya ne? Ana wulakanta uwarki bakya gani. Allah shirye ki."

Haka suka cigaba da cecekuce tsakaninsu, Haj safiyyah da yaranta uffan basu ce ba.

💔💔💔

Karfe 8pm, agogon k'asar India, Alh Usman Gwandu da aka fi sani da Zunnurain ya isa babban asibitin birnin Bombay. Bai sha wuya ba aka sadashi da matashin likita da kusan duk duniya ake alfahari dashi. 

Ya nufo Alhaji yana mai murmushi. Bayan sun gaisa Alh ya kalle shi ya ce

" Dr Ridwan Bagudo dafatan ka gane ni?" Yayi shiru yana sauraran amsarsa.

"Ko a mafarki bazan manta fuskarka ba, tunda har na baku abu mai mahimmanci a rayuwata. Kunzo lafiya?" Cewan Dr Ridwan.

"Lafiya lau, ga d'anka Uthman, Zunnurain" Alhaji ya ce yana mai nuna masa zunnurain.

Rungumarsa yayi yana fitar da hawaye, wannan saurayi dan shekara (10) yafito daga jikin little angel d'insa.

"Ya mamanka? Tayi k'iba yanzu ko? Naga kaima ka fini k'iba".

Dariya kawai Zunnurain yai. Alhaji ne ma yai magana;

"Tayi k'iba ta k'ara kyau sosai. Cikin shekaru takwas da rabi da aurensu ta haifa masa yara hudu. 'Yan biyu Safiyyah da Uthman, Khadija da Zainab (mamienka). Cikin shekarun nan ban tsammaci akwai ranar da Rufaida tayi minti ashirin na bak'inciki. Muna godiya ga Allah Umair ya cika alkawari".

Dariya Dr yayi, kana yace " Alh nayi farinciki kwarai,amma nasan k'anwata matar alfahari ce, suruka ta gari sannan uwa ta gari ko my son?"

"She is the best mum ever, amma yanzu kullum se tayi kuka, bata dariya, in tana koya mana karatu tana kuka".

"Whaaaat!!! Alh yanzu kace min tana cikin farinciki?". Ridwan ya fadi a firgice yana duban Alhaji

"Rufaida na cikin tashin hankali, shine dalilin zuwa na ma. Rufaida ba suruka ta bace, 'ya ce da nake so fiye da wa'inda na haifa, shine nazo a matsayina na ubanta in sama mata farinciki ta wajenka. Kaine kadai zaka dawo mata da farincikinta. Allah yayi ma Umair rasuwa shekara biyu da suka wuce, duk wani tawakkali da ake son d'an musulmi dashi an samu Rufaida dashi. Amma daga bayan nan duk ta firgice, ta kasa kwantar da hankalinta. Ka taimake ni Ridwan, banson hawayen Rufaida."Alhaji ya k'arasa yana mai sheshek'a.

"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Allah ya jikan Umair, Ya kai rahma zuwa ga makwancinsa. Zan zo in bata baki, inshaAllah zata maida farincikinta."

"Aurenta nake so kayi ba kazo ka bata baki ba".

    Dr ya dauke kansa yana mai daure fuska

"A iya sanina kasan uwarmu d'aya ubanmu d'aya, kaga kenan babu aure tsakaninmu."

YANKAR KAUNA Where stories live. Discover now