Good morning sweethearts..
Kun tashi lafiya?
May b se late at night but if am opportuned will Holla u lunch 😁
Kada ku manta I wrote this Wen I was an amateur Ko ni ina jin sa wani haka-haka but I can't edit..
Kallonsa Alhaji yayi na d'an dak'ik'u kana yace "Haka dai kace Ridwan. Amma kaje kayi tunani zan sake dawowa nan ba da jimawa ba".Jan hannun zunnurain yayi suka tafi.
Kwanansu bakwai (7) a India suka dawo gida Nigeria, basu tsaya ko'ina ba sai garin Malisa gidansu Rufaida. Sun samu tarba na musanmman duk da ba'a san da zuwansu ba, bayan sun gaisa Alh ya kalli mahaifin Rufaida yace;
"Alhaji Nuruddeen"
Baban Rufaida yai saurin d'agowa ya kalle shi don a iya saninsa bai ta'ba jin ya ambaci sunansa ba se sannan.
"Nazo ne ina son sanin alak'arku da Ridwan"
Mahaifin Rufaida yai murmushi yace "Labari ne mai tsawo, amma bari muyi sallan la'asar sai na fada maka tarihin mu"
💔💔💔
"Sunana Nuruddeen, ni asalin garin Bagudo ne, dagani sai kanwata muka rage mai suna Fadila, iyayenmu sun rasu sakamakon gobara da ya kama bukkan mu, inda suka rasu da kanninmu biyu.
Mun fuskanci wahalhalu bayan rasuwan iyayenmu a lokacin ina da shekara tara, Fadila nada (7).
Wata shida bayan rasuwan mahaifanmu aka tura ni almajiranci a kauyen Kwasara, inda na k'arasa karatun Muhammadiyya a garin.
Sanda na cika shekara ashirin a duniya, malaminmu Alaranma Bello ya bani auran 'yarsa Zainabu. Yarinya kyakyawa da kyawun hali
Watanmu uku da aure na shirya mana zuwa Bagudo dan gaida Baffa na da sauran dangi don rabona dasu tun zuwa na almajiranci.
Munje mun iske kowa lafiya, anan na taradda Fadila ta auri d'an sarkin garin har sun haifi dansu Ridwan tana kuma da tsohon ciki
Nayi farincikin ganin Fadila domin ta k'ara kyau da wayewa, mun dad'e muna hira anan take fada min ba'a k'asar suke ba, kuma mijin na sonta har yasa ta makarantar boko.
Cikin kwana (6) mun zazzaga 'yan uwa da abokan arziki, a kwana na bakwai muka dauki hanya muka koma Kwasara.
Aurena da shekara goma sha biyu (12) muka sami Rufaida. Zainabu ta haifi yara (8) duk sun rasu, (abinda hausawa kece ma waabi).
Na aika ma mutanen Bagudo haihuwan kamar yanda na saba aika musu duk ta haihu. Ranar suna se ga su Fadila don sun zo daga k'asar da suke wato Moscow.
Nayi farincikin ganinsu don rabon da mu hadu shekaru (10) kenan. Ridwan ya girma da k'anninsa biyu Hibbatullah da Aamatullah.
Abu d'aya ya tsaya min a rai, sauyin da nagani a fuskan k'anwata da yaranta mata, sun nuna k'yamanmu suke ko ruwa bata sha ba. Ridwan ne ma ya dame ta cikin halshen fullanci akan wanene ni, tace Yayanta ne.
Bud'an bakin Hibbatullah se cewa tayi "Amma bakiyi sa'ar Yaya ba don kuwa k'azami ne talaka".
Na zuba ido inga ta kwa'be ta se naga ta rungumo ta. Da haka suka fice.
Tun daga ranar ban sake ganinta ba se da auren Hibbatullah, lokacin Rufaida nada shekara (9), na samu na halarci d'aurin auren, amma ba mu je taron bikin ba.
Bayan bikin da kwana biyu, Ridwan yazo ya same ni har gida da takardun gidan nan da muke ciki, ya rok'e ni Allah da Annabi in baro Kwasara in dawo Malisa da zama saboda ya fi ku sa da babban birnin jihar.
Da k'yar ya shawo kaina, bacin gidan nan ya sama min sana'ar yi, shi ya dauki nauyin karatun Rufaida tun daga primary, har kwalejin 'yan mata na tarayya da ke garin gwandu (FGGC GWANDU), ya sama mata jami'ar kimiyya da fasaha ta jihar Kebbi.
Duk wani hidima da uba ze ma 'yarsa Ridwan yayi ma Rufaida, akwai sanda ya ce min don Allah in bashi dama wajen zab'awa Rufaida miji, ni kuma nayi masa alkawarin shi zai bada aurenta. Nayi tunanin ko sonta yake sai kuma banji komi dangane da haka daga garesu ba.
"Dafatan ka gamsu" Ya k'arasa yana mai dariya.
Alhaji yayi dariya yace "Na gamsu kwarai. Dama a matsayi na na uban Rufaida ne nake so na aurar da ita, zamanta haka nan bai da amfani."
"Haka ne kam ni ma naso inyi magana sai nayi tunani kar nayi muku shishshigi."
{27}
Alh Usman bai bar jihar Kebbi ba sai da ya zaga aminan Rufaida wato Firyal da Naseera ya tambaye su alak'ar Rufaida da Ridwan.
Amsar duk d'aya ne "Yayanta ne bacin haka babu komi."
Ko da ya koma Kaduna baice ma kowa uffan ba akan zancen, Zunnurain ne ma yace ma Rufaida sunga wani uncle mai kama da ita, dariya kawai tayi ba tare da ta maida hankali ga zancensa ba.
YOU ARE READING
YANKAR KAUNA
General Fiction"Wanena halan?" Daya daga cikin 'yan union ya tambaya. "Alhaji Usman na hwa. Baka gani ZUNNURAIN ga jikin lambar mota nai. Ko da yake duk kuna yaka hwadi ma magana ko yak'i da jahilci baku tai ba." Daya daga cikinsu wanda dagani direba ne yake fadi...