Goma

1.3K 167 72
                                    

Washe gari bayan shatara na arziki da aka hada ma mahaifin Rufaida, Alh Usman yace duk su shirya dasu za'ayi tafiyar. Haj Jamila kamar ta zuba ruwa a k'asa ta sha don murna, bata ko b'oye ba. Ba wanda yasan dalili amma ita Haj Jamila tunaninta Alhaji ya dauki maganarta.

Tafiyar awa takwas ya sada su da garin Gwandu daga Kaduna don ma motar gida ce. Rufaida da mahaifinta da yaran har gida garin Malisa suka isa. 

Washe gari da safe Alhaji Usman da matanshi tare da aminansa biyu suka dira gidansu Rufaida. Bayan gaisuwa da yi ma juna ta'aziyya da ban gajiyar hanya, aminin Alh Usman, Alh Bilal Gwandu ya ce, 

"Mun zo neman iri karo na biyu, wannan karan ba neman aure muke ba, rok'on arziki muka zo. Tunda kuka bamu auren Rufaida bamu taba d'aukar Rufaida a matsayin suruka ko matar d'a ba, face 'ya, munzo ne neman alfarma ka bamu Rufaida ta kasance k'ark'ashin ikonmu har mu aurar da ita ba don kun gaza ba sai don k'aunarmu gareta".

Shiru ya ratsa wajen, kafin baban Rufaida ya kirata da maminta ya maida musu abinda ya kawo su Alhaji. Sannan yace; 

"Jiya na tabbatar da Rufaida tayi dacen iyaye ba don kyautar da kukayi mata ba, sai don ina d'aki Hajiya Safiyyah tazo ta rok'i in bar mata Rufaida, har da kukanta amma nace ta bari nayi tunani akai. Yanzu kuma kun zo  da wani zancen, ko don darajar 'ya'yanta mun bar muku ita, Allah Ya baku ikon riko".

Godiya suka cigaba da yi kamar yayi musu kyautar duniya. Basu bar gidansu Rufaida ba sai bayan azahar, Hajiya Safiyyah ta saki jiki, da ita akai girkin ma. 

Washe gari, sukayi harama suka koma kaduna kowa na farinciki in banda Hajiya Jamila da ta dinga fad'in "Kun bari an asirce ku,ni wallahi kurwata kur, nama na d'aci gareshi"

Ba wanda ya tanka mata har suka isa Kaduna .

💔💔💔

Bayan sallar isha'i Hajiya Safiyyah ta dauko k'undun sirrin (diary) Umair ta fara karantawa..

Shafin   farko abinda ta fara gani shine "( Am just me, Umair bn Uthman. 

Rule 1: I don't Imitate others for no one succeed by imitation.

Rule 2: I don't envy for it leads to failure.

Rule 3: I have no enemies, I luv every one.)

Ni  din nine, Umair bn Uthman. 

Doka na d'aya; Bana kwaikwayo,  domin duk mai son cigaba bazai kwaikwayi kowa ba. (Kira ga masu yin abu don wasu sunyi, in wani yayi rawa ya sami kudi wani in yayi jibga zai sha....~Ummu abdoul)

Doka ta biyu; Bana hassada domin hassada na kaiwa ga asara.

Doka ta uku; Banda mak'iya, ni ina son kowa.

Ajiyar zuciya tayi tace

" Umair haka nan kake, baka ma sanya kai mai tsoron Allah da kiyaye dokokinsa ne ba". Ta share hawayen da ya gangaro mata sannan ta  bude shafin gaba.

Ta cigaba da karantawa wanda da harshen turanci duk yayi su.

"Duniya banda amini daga k'undin sirrina sai Jackie. Wanda muka hadu tun zamanin kwaleji.

Ina son Jackie amma yana sani aikata zunubi hawaye.

 Ban taba zina ba Alhamdulillah...

Ta tsallake wasu shafika duk zane yayi gashi da yaranshi, ga iyayenshi sun tsufa ya so musu ziyara, abin mamaki sai taga yayi ma Hajiya jamila k'aho irin na zanen shaidanu. 

Tace "Hmmmn, auta kenan uwar dakinsa ce haka?"

 Ta cigaba da kallon zanensa kasancewarsa gwani a zane yasa ta iya fahimtarsa.

YANKAR KAUNA Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz