ABU A DUHU 3

1.8K 87 0
                                    

*ABU A DUHU*
(Shaima Alhussaini)
    *3*
Soyayya ce me qarfi yashiga tsakanin bayin Allahn biyu, se de kash iyayen azra sunce bazaayi auren su yanzu ba.. dole dole se tahada degree dinta..
Haka ya haqura yace to zai jirata , dan yanzu ne ma azra take shekara na biyu a jami'a

Azra da haitham sun zama love birds shaquwa me tsanani yashiga tsakanin su.. azra ba ta da wani magana da yawuce na haitham dinta shima haitham din haka.

Kwanci tashi ba wuya inji bahaushe...

Yau gashi azra zata gama degree..
A cikin shekaru ukun nan masoya  da dama sunsha kawowa azra hari Amma azra tayi biris tace inba haitham ba ita bata ganin kowani namiji da gemu..

Ta bangaren haitham kuwa kullum yana zarya a gidansu azra, shi ke coaching dinta a karatunta, dangi duka ba Wanda baisan haitham ba, shima ta bangaren en gidansu ba Wanda baisan azra ba, da anyi masa maganar har yanzu baiyi aure ba da de uzurinsa Bai samu matar aure ba.. Amma yanzu uzurinsa daya tilo ne wato azra bata kammala karatu ba.. to gashi Alhamdulillah azra tagama karatu ta lafiya lau.. gobe iyayen haitham zasuje Nema masa auren azra..

ABU A DUHU Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ