ABU A DUHU 5

1.5K 82 0
                                    

*ABU A DUHU*
(Shaima Alhussaini)

                *5*
  Cikin sauri ya aika a kirawo masa Azra.  Sede kash an dawo masa da mummunar ansan da yaqara dagula masa lissafi.  wai Abba yahana azra fitowa..

Kan yajuya Sai ga abban nan da Kansa.. yace haitham,
Haitham ya duqa har qasa yagaidasa yace na am Abba..
Abba yace haitham ba wai na hana ka auren azra bane, Sai dai kayi hakuri dama ban ce namaka alqawarin zan baka ita bane, kayi hakuri yayana mahaifinta babba kenan ya yanke hukuncin hada auren ta da dan uwanta.. bawan Allah kayi hakuri azra ba rabonka bane.. cikin tashin hankali yayi sallama da baba yafice se de uku uku yake ganin hanya.
Ji kake rammmmmm...motarda haitham ke tuqawa ne ya bugi wani bishiya.. Sai innalillahi wa inna ilaihi rajiun mutane wasu na salati.. wasu na cewa ai dama giya yasha dole yayi irin hatsarinnan( kaji en adam Abu a DUHU basusan me musabbabinsa ba Amma har sunyi conclusion ai giya yasha.. Allah yashiryemu)..

Haka nan wasu su kadaine shi aka kaishi asbiti bangaren taimakon gaggawa.  Atake kuwa aka bashi kukawa na mussaman, yaji mummunan rauni a ka, yakuma samu Karaya a hannu..
Likiticin sunyi iya qoqarinsu sun ceto rayuwarsa Sai de har yanzu Bai farfafo yadawo hayyacinsa ba

ABU A DUHU Место, где живут истории. Откройте их для себя