ABU A DUHU 7

2.1K 83 7
                                    

*ABU A DUHU*
(Shaima Alhussaini)
  *7*
Mun san matsalarta likita.. soyayyace Amma iyayen ta Maza sun haramta mata, ya zamuyi!
Ya zakuyi?? Inji Dr.. yazakuyi fa Kika ce? Kin gwammace kenan diyarki ta mutu? Wallahi to ni dai a shawarce nabaku Shawaran gaggauta yiwa yarinyar nan abinda takeso  in dai be sa ba Sharia ba.. mummy ta numfasa tace Dr. DanAllah kitaimakeni in Abbanta yazo kiyi masa explaining vividly, may be musami dacewa..
Dr tace inshaAllah, Amma in ba abin su bama ai an daina yayin auren dole. Allah dai yasa a gane..

Kamar yadda mummy kanemo dr. Da tayi hakan kuwa dr.rahima tayi، tasami daddy tayu convincing dinsa sossai, akan ya amince wa azra da zabin ranta, su su hakura,takuma bayyana mishi halinda Ake ciki kuma ta qara da cewa  lallai lallai in ba a barta ta auri Wanda takeso ba za a iya rasata gaba daya..
Abba ya gode yace inshaAllah zaiyi Qoqarin samun dan uwanshi su tattauna..
Abba ya Sami danuwansa Wanda suke Kira da baa kura ko alhaji babba, da wannan zancen.. se dai kash Abu baiyi dadiy ba dan wannan shine sanadiyyar fadan Alhaji babba da Abba, domin alhaji babba gani yake abba kawai ne bayason a aurad da azra ga danshi. Dama dan nashi na da matsalar shaye shaye,shine yaso ayi auren tuwona maina a rufawa juna asiri..
Abba na barin wurin Alhaji babba ba inda ya nufa se gidansu haitham.. sun masa tarba na mutunci in da yake shaida musu cewa yazo ne yabasu hakuri kuma ya amince ayi auren wadannan masoya guda biyu nan da sati daya..

Cikin Mamaki haitham ya tashi yayi sujadar godiya, yakuma godewa Abba. Tuni ya mance da ciwon da yake yi,  dama har an ware hannunsa..

Kowa na farinciki da walwala a gidan dan Basu da farincikin da ya wuce suga haitham na walwala..kasancewarsa mutum ne me barkwanci da raha ga kirki ga son jama'a..

Bari mudawo ga azra..

Ita kuma azra labari na isowa gareta se miqewa tayi tsam.. ji take ciwon da take ji a zuciyarta kaman an wanke mata shi TAs.. se tafaara kuka farin ciki a take kuma ta rufe fuskarta wai kunya(nace bayan me..lol).. ta qara kwana biyu a asbitin har se da aka tabbatar ta wartsake aka sallameta tare da bata shawarwari masu amfani Wanda ciki harda tarage sa damuwa a ranta..  biki saura kwana 5 inshaAllah .. shiri akeyi ba kama hanyun yaro. Mummy zata aurad da er tilon diyarta me hazaqa tarbiyya kyau da nutsuwa...
Anshirya yin
events kala kala abin ba a cewa komai

ABU A DUHU Où les histoires vivent. Découvrez maintenant