RUQAYYAH*👱🏻♀
👩👧👧 *Uwar mata* 👩👧👧
📝Written by
👱🏻♀Asmeey 👱🏻♀#the real pure pinkeey 💅🏼✍
Page 5
💞
💞💞
💞💞💞
💞💞💞💞
💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞💞💞💞Dedicated to Jidda Habib, Fatima naseedy and Hauwah Cutee(my hajjaju) no need for long essay you know I heart you guys irin totally nake fad'a muku.
RUQAYYAH kam tunda taji she is pregnant hankalin ta ya k'ara tashi, jitake kamar kanta zai tarwatse " innalillahi wa'inna ilaihir raji'un " kawai take mai_mai tawa, " Ya Allah meyake shirin faruwa dani? " ta fad'a a zuciyar ta idonta kuwa tuni ya ciko da hawaye.
Maganar Aliyu ce ta dawo da ita nutsuwar ta, sai_saita kanta tayi sannan ta mik'e suka tafi.Cikeda happy ya kirawo Umar ya sanar dashi, sosai yamasa murna sannan ya tayashi da addu'ar Allah ya cika masa burinsa.
Kashe wayar yayi sannan d'auke da murmushi ya juyo ya Kalli RUQAYYAH yaiwa motan key suka tafi gida.
A b'angaren Beelkeey kuwa sun d'an tab'a hira da Hajiya sannan ta koma d'aki, wayarta ta d'auka ta shiga neman number'n k'awarta, Fatima Ado Haruna shine sunan dayai appearing a kan screen d'in wayarta ringing d'aya ta d'auka.
"Shegiyar gari, Beelkeey shuwerh Ya Akai kinsan ina lectures kika kirani? " Abinda Aka fada daga daya bangaren kenan.
"Yar duniya Hayak'in taba Maza ki fito a class dinnan Akwae bura uba a k'asa"
"Haba dai bari na fito ke kina ma gidah na tawo? Dan naji kamar gulmar tafi k'arfin waya".
"Wallahi ina Gidan su Aliy7, Dan Allah kiyi sauri wlh kika dad'e ta wuce ki"
"Aah wallahi gani nan yanxu"
"Yawwa Merhmeey ta ta kaina"
beelkeey shuwerh ta fad'a tareda yanke kiran.
Aikam Merhmeey najin Haka ta baro lecture hall din ta fito se gidan su Aliyu.
Cikin k'ank'anin lokaci ta Isa gidan Su Aliyu.
Da sallama ta shiga har ta kai falour bataga kowa ba Zama tai Akan kujera ta shiga kiran beelkeey shuwerh.
"Ke kinzo ne ko kuwa? ""Dalla gani nan a falour babu kowa"
"Aa gani nan zuwa" ta fad'a tareda yanke kiran.
Da sauri ta fito daga d'aki "tashi mu shiga ciki ai abun sirri ne"
" Allah kawata muje to"
Suna shiga d'aki merhmeey ta jefar da Jakarta da mayafin ta kan gado "ban nasha beelkeey meya faru? "
"Bara na kawo miki Abin motsa baki tukun "cewan beelkeey shuwerh.
"Ke bash shi wallahi nifa kawai gulma nake jira naji meya faru? " cewan merhmeey.
Zama beelkeey shuwerh tayi tace "ke kinsan aure na sati d'aya kuwa? "
Heart din merhmeey loosing beat tayi da k'yar ta iya furta
"Kamar ya sati d'aya ? Shi Abdul ne yace haka yakeso? "
Wani shu'umin murmushi beelkeey tayi sannan tace
" Aikin Hajiya ne, kuma kinsan maganar ta kamar dutse baka Isa ka musa ba yanxu kagane kuranka wani abun haushin ma wai danna haifa masa d'a namiji wlh dukkan su k'awata se sun ga tsiya da Rashin godiyar Allah".
Itakam Merhmeey rasa meza tace tayi Dan haryanxu Abin ya tsaya mata dakyar ta iya furta
"Wallahi kawata Abin nan dole mu bullo musu ta baya".
Da haka sukai ta kulle_kullen su Har suka gama."Assalamu Alaikum"
Wata y'ar budurwa da bazata wuce sa'ar su ba
Ta fada
A tare suka Amsa da
"Wa alaikis salam"" Allah dai ya biya Matar yaya" abun da yarinyar ta fad'a
"Ummeey kenan baki da Dama har kin dawo? "
"A na dawo little mum tana gaidaki ma Merhmeey'n beelkeey kina nan kenan"
"Ina nan Wallahi"
Ba'a ganinki se beelkeey shuwerh na waje dama Dan ita kike zuwa". Ummeey ta fad'a.
"Kema ba nema na kike ba Ai" merhmeey ta bata Amsa.
Haka suka ci gaba da hira suna tsokanar beelkeey shuwerh da Amaryar sati d'aya
*WAIWAYE ADON TAFIYA*
Wacece Hajiyan Aliyu?Hajiya Maryam Sa'id gwani Haifaffiyar Katsina ce ita ce diya ta biyu a wajen mahaifin su Sa'id gwani se yayanta Mai suna Muhammad da kanwarta Zainab.
Muhammad baida d'a ko guda daya a rayuwarsa, Maryam kuma y'ayanta biyu Aliyu da Hadiza da suke kiranta da Ummeey. Zainab kuma 'ya'yan ta uku Beelkeey shuwerh, Se mai binta Kabir da karamar su Ramlat.Hajiya Maryam ta kasance mace mai bala'in zafi babu wanda yake tab'ata ta raga masa idan Aka cire iyayenta se yayanta. Amma duk Abinta tana son y'an uwanta.
Idan ka taba nata ka tab'o wa kanka rigima.
Gashi idan ta daurawa mutum karan tsana ya shiga uku a wajenta Idan kuma tana sonka to babu ya kai a cikin heart inta.
Wata Rana a hanyar ta ta dawowa gida daga school wani saurayi ya kusa bigeta da mota Allah ya taimake shi bai bigeta ba amma didda haka seda ya fito ya bata hakuri.
Ko kallo bai ishe ta ba taci gaba da tafiya. Shima motar ya koma yai tafiyar sa inda ya nufa.......Yar gatan faty Azland ceh💃🏻💃🏻💃🏻