_*DACEWA*_
_(when east meets west)__By_
_Mamuh geee_*Viawattpad@mamuhgee*
*24-25*
Tunda take arayuwarta ba'a ta6a wulaqantata kamar yauba.,Yau ita neesar da kowa ke rububice qaninta Jamaal ya wulaqnta cikin dubban mutane,
'Dagowa tayi zuciyarta kamar zata qone takalli Habib dake tsaye gefe yana sakar mata murmushin mugunta sbd buqatars data biya na yanda Jamaal yagansu.
Zeey ce ta qaraso da sauri takamata a kidime tana cewa,
Lpia neesah?
Ina motar?Har lokacin kallon Habib take sbd wata sabuwar tsanarsa da qiyayyarsa datakeji.
Kuka takeson yi sbd zuciyarta dake mata zafi sosai amma tsabar taurin rai taqiyi sbd gani take taci baya idan tayiwa Jamaal kuka.
Tsabar baqin cikin ko motar ummi daya bar mata bata kallaba ta hau drop ta nufi gida tanajin tsanarsa shima nashiga ranta.
Harta isa gida tsanar Habib da Jamaal na kai kawo cikin ranta
A harabar gidan ta tarar dashi yana waya har lokacin fuskar nasa a ha'de take.
Kai tsaye shi ta nufa itama fuska a murtuqe.
Sarai ya lura da gurinsa ta nufo ya qara ha'de fuskarsa sosai.
Zata fara mgna ya 'dora mata oily eyes 'dinsa cikin tsuke fuska yace,
What?
Rantane yakuma 6aci tama rasa abinda zatai masa sai kawai ta juya a fusace tai cikin Palo.
Siririn tsaki yaja yanajin tsantsar takaicinta tareda qyanqyaminta na shigarsa cox yanxu yafara tunanin abinda yasa aka fasa aurenta shine shi aka maqala masa,.
Motarsa yafada yafice daga gidan.Khadija dake tsaye qofar parlor tana kallonsu jitayi qirjinta yayi mata nauyi tayi 'dakinta da gudu tana danne hawayenta.
Neesah ta ganta taja tsaki tareda fadawa 'daki itama sbd kukan dake qoqarin zuwar mata itama tana dannewa.
Baki ummi dake zaune Palo tasaki tana bin qofofin 'dakunan nasu da kallo cikin mamakin abinda ke damun kowaccensu.
Tana shiga 'dakin ta sulale qasa tareda sakin kukan baqin ciki,
Tabbas yau taqara tabbatarda bazata iya Rayuwa da Jamaal ba sbd bazata iya 'daukar wulaqancinsa ba.Da safe ummi hankalinta tashi yayi matuqa sbd da wani mugun zazza6i su duka suka tashi bama kamar neesah da har lokacin bata daina tsiyayar hawaye ba.
Khadija kuwa duk zazza6in dake cinta hakanan ta shirya ta gudu school sbd ganin neesah zai iya 'Dora mata hawan jini.
Zama ummi tayi tana kallon neesah jiki asanyaye tace,
Baby kidaina kukan nan ki sanar dani matsalarki nayi alqawarin magance miki ita muddin batafi qarfina ba.
Lumshe rinanun idanuwanta tayi hawayen dake ciki suka gangaro batareda ta bu'desu ba murya a karye tace,
Ummi in gaf da rasa numfashina,
Ummi rayuwata bazan ta6a samun farin cikiba muddin ina zaune da auren Jamaal akaina,Ummi bazan iya Rayuwa da Jamaal ba sbd halayenmu sun nesa da juna,
Bu'de idanuwanta tayi ta 'dorawa ummi murya na rawa tace,
Ummi kisa araba aurena da Jamaal wlh bazan iya rayuwar aure dashiba.
Sosai jikin ummi yayi sanyi takalli neesah jikinta na tsananta sanyi tana karanto iya gskia neesah ke fadar zancen.
Baby tabbas yau da inada dama dana rabaki da Jamaal amma kasancewata mace na rasa wannan damar saidai ina miki alqawarin samun farin ciki matuqar kikayi hkr kikai biyayya.
Rintse idanuwanta tayi tareda zamewa takoma kwance.
Ummi ma jiki amace ta miqe ta fice.Jamaal kuwa a ranar ya tunkari dady da zancen auren ayeesha kai tsaye dadyn yace ba yanxu ba.
Bai tsaya 6ata time 'dinsaba ya kira abban neesah yafada masa kai tsaye,
Abban neesah kuwa babu wani shamaki ya amince tareda alqawarin zuwa wani sati sbd ganawa da iyayen ayeesha.
Mamy dataji sosai tashiga damuwa sbd sanin halin neesah na girman kai bazai ta6a bari taji 'dadin rayuwar aureba gashi har za'ayi mata kishiya da wuri haka batareda tasan wani da'din aurenba.
Abba bayan yakira dady sunyi mgn shima dadyn ya amince ummice ta tsaya tsayin daka akan bata aminceba.
Sam Jamaal yanxu baicika zama gidanba sosai sbd Fushun da ummin keyi dashi akan mgnar.
Yau zaune suke Palo ummi na lalla6a neesah akan tasha magani inna rabi kuwa sai dariyarsu take.
Khadija Ce tafito 'dakinta tazo ta zauna kusada ummi duk ta hargitse ga wata uwar rama datai.
Kallo ummi tabita dashi cikin damuwa da tausayinta zatai magana inna Rabi tarigata da fadin,
Ummi 'yayanki dai lpia tayi musu qaranci musamman ma khadija duk tabi ta rame.
Hmmmn inna Rabi wlh ita khadija nama kasa sanin damuwarta har gwara baby ita nasan matsalar aurentane da jamaal....
Wata mummunar qwarewa khadija tayi wadda ta haddasa mata wani yunqurin amai ta sbd jin maganar ummi ta qarshe wai Jamaal mijin neesah.
Ummi dake zancen Sam bata luraba sbd hankalinta nakan neesah sake shan magani taci gaba da fadin,
Sannan yanxu dan tsabar rigima yace wani auren zaiyi kafin yakom......
Kusan atare neesah da khadija suka aware gaba 'daya ruwan dake hannunta suka xube had glass cup 'din nafashewa itakuwa khadija miqewa tayi ta nufi janyar bedroom ko gani batayi sai kawai su ummi ganin sukai ta yanke jiki ta fadi asume.
Mamuh💋
🌲 *R H F W F*🐄
_Don't forget to vote, follow and comments_
YOU ARE READING
DACEWA✅
Romanceunexpected relationship last longer,,,, as east meets west in love....