🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾
*ME KE FARUWA?*
🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾
*A TRUE LIFE EVENT*
*WRITTEN*
*BY*
_*BILKISU Z. YAU (🅱K )*_
_( Autar Marubuta )_&
_*AISHA ISA*_
_( Mummy's Friend )_*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS*
_(Gidan zaman lafiya da amana., In Shaa Allah)🤜🤛_*SADAUKARWA GA:*
*MAMAN SALEEM*
_( Aunty lipson )_&
*UMMU AKRAM*
_( Aunty Aisha )__*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
_*Manzon Allah S.A. W yace : duk wanda yabi wata hanya yana mai niman ilimi Allah zai sauk'ak'a masa hanyar shiga aljanna.*_
*BABI NA TARA*
Amira ta kasance d'aya daga cikin irin wad'anda Allah yai musu farin jinin duk inda ta shiga saita samu masoya ba mazan ba har mata sonta suke saboda akwaita da saurin sabo da shiga rai, hakan ne ma ya kasance a zamanta a gidan Auntyn ta.Wata rana tafe Amira take cikin hanyar ta na dawowa daga aiken da aunty Hauwa tayi mata cikin takunta wanda Humaira tayi wa lak'abi da yanga, wani saurayi ne ya tsaidata, sallama yayi mata sannan yace " don Allah tambaya nake. "
Amira tace " Allah yasa na sani" Amira ta fad'a a takaice don babu abinda ta tsana kamar saurayi ya tsaida ta a hanya.
" Yi hak'uri fa naga kamar ranki ya b'aci."
Murmushi tayi wanda ya k'ara wa fuskarta kyau sannan tace "lah babu komai wallahi sauri nake yi shiyasa. "
" Gidan mall. Buba mai anguwa nake nema, dan Allah ko kin san gidan?".
Amira tace "eh nima dai bak'uwa ce a unguwar amma a kusa da gidan nake ina jin sunan, ko zaka biyoni na kai ka watakil shine wanda kake nema?"
Yace " na kuwa gode " ya bita a baya suna tafiya don gidan akwai d'an tazara daga gun da suke, ganin wurin da d'an nisa kuma babu wanda ya yi wa wani magana cikinsu sai saurayin nan yace "ni suna na Mujahid."
Murmushi Amira tayi, amma still bata ce komai ba.
Mujahid yace " baki fad'a min naki sunan ba"
" Am Amira " Amira ta bashi amsa cike da nuna kosawa, daga haka babu wanda ya k'ara yiwa wani magana cikinsu, sai da Amira ta kai dai-dai bakin gate d'in gidansu ta tsaya, Hannu tai masa nuni da shi tace " gida na uku shine wanda nake tunani zaka iya tambaya watak'il a dace," bata jira ta cewarsa ba tayi shigewar ta gida.
Shi kuma gogan cike da murna ya k'ara sa gidan yana sake-sake cikin zuciyarshi, ya kuwa yi sa'a gidan da yake nema ne.
*Bayan kwana biyu*
Amira ce zaune kan kujera tana yiwa auntyn Hauwa tsifa, yaro ya shigo yace " wai ana sallama da Amira."
"Je kace bata nan" Amira ta bawa yaron amsa.
Aunty Hauwa tace "je kace tana zuwa," Shek'awa yayi a guje sannan ya samu saurayin yace "wai tana zuwa," naira d'ari ya ciro daga aljihunsa ya mik'a wa yaron.
YOU ARE READING
MEKE FARUWA
Short StoryLabarin wata budurwa ne wacce aure yayi mata wahala. Amira kenan 'yar kimanin shekara 24 da hud'u, tayi samari fiye da biyar amma dukkan su sai magana tayi nisa kwatsam sai a nime su a rasa. Amira na da kishir uwa wacce sam basu shi da ita. Ko mek...