🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾
*ME KE FARUWA?*
🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾
*A TRUE LIFE EVENT*
*WRITTEN*
*BY*
_*BILKISU Z. YAU (🅱K )*_
_( Autar Marubuta )_&
_*AISHA ISA*_
_( Mummy's Friend )_*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS*
_(Gidan zaman lafiya da amana., In Shaa Allah)🤜🤛_*SADAUKARWA GA:*
*MAMAN SALEEM*
_( Aunty lipson )_&
*UMMU AKRAM*
_( Aunty Aisha )__*Wollah munji dadin comment dinku na jiya, don haka muma zamu cika alkawari tare da baku sadaukarwa wannan page*_
_*Wannan page dinnan sadaukarwa ce ga dukkan masoya wannan littafin*_
_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
_*Manzon S.A.W yace : Mafificin aiki shine yin sallah a cikin farkon lokaci.*_
*BABI NA GOMA SHA SHIDA*
Murmushi Amira tayi sannan tace " kamal ai ni nasan mutunci na, kuma Allah yagan niyyata taimakon nayi ba cuta ba, da sannu zai bi min hakkina tunda dai aron kace na baka ba kyauta.... "
"Dalla malama karki gayan magana kan chicken change..., next month idan na karbi albashi zan biya ki kudinki".
"Zai fiye maka.. " bata jira taji ko me zai fada ba ta kashe wayarta. Ajiyar zuciya tayi ta runtsa ido "ya ilahi see me through, wai *meke faruwa* dani ne?, me nayi wa Kamal yake son cuta dani haka?" ganin bata da amsar dukkan wannan tambayoyin yasa ta tashi ta dauki gyalenta, dakin mummy ta nufa tace "mummy don Allah ki bani kudin machine naje gidan su anty Hauwa".
"Wani abun ne ya faru?"
"A'a mommy ina dai son zuwa ne kawai".
"A'a kibari daddy ya dawo sai ki tambayeshi, in yaso gobe sai kije kinga yanzu ranar ta riga tayi zafi ko"
"Ayyah mummy don Allah ki barni in tafi, sai ki kira daddy ki shaida masa.... Kinji mummy please".
"Hmm! Toh a dawo lafiya " sannan ta fito da kudin ta bata.
Amsa tayi tare da godiya kannan ta tafi.
Sallama tayi tare da bude kofar. Kwance ta sami aunty Hauwa akan 3 seater tana kallon Indian film. Dagowa aunty Hauwa tayi jin a shigo dakin, murmushi ta saki ganin Amira tsaye, anty hauwa tace " what should I offer this surprise visit?"
Murmushi Amira tayi tace " anything sis... "
"Toh ga kitchen nan ki shiga ki dauki duk abinda kike so".
"Wallahi aunty a koshe nake, Aunty wai ina d'ana yake ne?"
"Ya tafi wasa tare da saura yara.. "
"Hhh, yaro ya fara samun freedom yanzu an daina kulle sa a daki.. "
"Yana iya ai dole na daina kulleshi kinga fa koda na rufeshi nan suke zuwa suta buga min kofa har sai na bude, shiyasa na daina wahalar da kaina".
"Ai hakan ma yafi shima zai dan saba da mutane tunda ba dan uwa gareshi ba".
Daga haka duk sukayi shiru. Amira tayi tagumi ta kurawa TV ido tana kallo amma a zahiri bashi take kallo ba.
YOU ARE READING
MEKE FARUWA
Short StoryLabarin wata budurwa ne wacce aure yayi mata wahala. Amira kenan 'yar kimanin shekara 24 da hud'u, tayi samari fiye da biyar amma dukkan su sai magana tayi nisa kwatsam sai a nime su a rasa. Amira na da kishir uwa wacce sam basu shi da ita. Ko mek...