21

2.1K 93 0
                                    

🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾

*ME KE FARUWA?*

🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾


*A TRUE LIFE EVENT*

        *WRITTEN*

              *BY*

_*BILKISU Z. YAU (🅱K )*_
_( Autar Marubuta )_

               &

_*AISHA ISA*_
_( Mummy's Friend )_


*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS*
_(Gidan zaman lafiya da amana., In Shaa Allah)🤜🤛_


*SADAUKARWA GA:*

*MAMAN SALEEM*
_( Aunty lipson )_

            &

*UMMU AKRAM*
_( Aunty Aisha )_


_When nobody understands the way you feel, remember the Almighty will make it heal. So turn to Him and fulfil your part of the deal._

_"Patience is not waiting for what you prayed for to come true. It's trusting whatever *Allahﷻ* has written for you."_


_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

_Manzon Allah S.A.W yace: mafi alkhairin musulmi shine wanda sauran musulmai suka kub'uta daga sharrin larshensa da kuma hannunsa._


*BABI NA ASHIRIN DA 'DAYA*

      Bincike daddy yasa aka masa akan Ismail, Alhamdulillah kuma duk abinda Ismail ya fada sun tabbata gaskiya. Haka ma ta bangare mummy itama ta saka Amata bincike kanshi, koda ta fadawa daddy sakamokon binciken nata duk magana kusan daya ne.  Wannan dalilin ne ya saka aka farawa sanar a dangi Amira tayi miji,  sai kash duk wanda aka sanarwa cewa ba d'an garinsu bane sai yace  ita mai yakai auren bare maimakon dan gari, wasu kuma tambaya suke ta yaya suka hadu tundai. Abin ya dade yana daure wa Amira ace wai mutum musulmi ma sai sun nuna banbanci, da cewa sukayi lallai sai banufe yanzu kuma ta samu banufen  amma duda haka basu bar wannan korafin ba. "hmm mutane baka iya masu wallahi,  saidai kayi iya yinka kabar saura".

Mummy kam ko a jikinta don inda sabo ta riga ta saba, domin itama haka ta sha fama dasu lokacin da ta aure daddy duk sabida ita 'yar garin bace. Wannan dalilin yasa suka fison aunty Amarya kasancewar ta 'yar gari.

*Bayan kwana biyu*

Kimanin wata daya kenan da daddy yace su Ismail su bashi lokaci amma  har yanzu shiru basu ji daga gareshi ba.  Wannan dalilin yasa suka dawowa a karo na biyu.  Hakuri daddy ya kuma basu tare cewa su dawo nan da wata hud'u, babu yanda basuyi ya rage tsahon kwanakin amma sam daddy bai yarda ba,  cike da mamakin wannan gaggawan tasu daddy ya yace "ai in har da rai da lafiya wata hud'u kamar yau da gobe ne ai ".

Sai a sannan ne suke sanar dashi tare da kara niman alfarma domin sunada bikin da suke son ayi ne a tare.  Lokacin ne hankalin daddy ya kwanta domin sai yanzu ya gane manufarsu,  naji taku amma kara hakuri har zuwa wannan lokacin. Haka suka hakura ba don sun so.

Bikin d'an uwan Ismail akayi sabida su bara su iya jiran har lokacin da daddy yace ba.

Ganin su Ismail sun kuma dawowa a karo na biyu daddy ya kira Bilkisu don jin ko ta tsaida mijin amma labarin duk irin ta jiya ce. Watanni  biyu daddy yabata ta fito da miji kafin lokacin da ya yankawar su Ismail tayi  don so yake ya hada su biyu domin itama Balkisu ta kammala karatun ta ko tana koyarwa be a wani makaranta private dake cikin anguwar su.

Hankalin aunty Amarya yayi matukar tashi da jin wannan hukuncin da daddy yake, yayanta ta fadawa ba wani dauki lokaci aka turo wani daga kauyen su yazo ya nima aurenta.

Bello kenan wanda a shekaru zai kai 35 zuwa 40,  yana koyar wane a wani makarantar gwamnatin dake nan cikin kauyen su.  Ya taba aure amma Allah yayiwa matar rasu ta bar 'ya'ya uku  duk mata wanda a halin yanzu biyu na gun mahaifiyarsa daya kuma na gun iyayen matar tasa.

Da farko kin amincewa Bilkisu  tayi don ita a ganinta ci bayane ace mutum na birni  amma ya koma  kauye da zama, gaskiya da sake...

_( hmmm 'yar babu yanda aure bata kai mutum, nasu gun mazaje wai don suna Maiduguri sai a daina, amma inda za'a k ban mummy's friend a 'yan rakiya😝😝😝)._


Kuyi managing wannan






*MUMMY'S FRIEND*

             &

*BK😘💋*

MEKE FARUWAWhere stories live. Discover now