MATAR ABDALLAH 19

6K 433 31
                                    

💧💧 *MATAR ABDALLAH.!*💥
                   True Life Story.!

                              💥

*©HASKE WRITER'S ASSO.💡*
Home of expert & perfect writers

*MALLAKAR: FEEDOHM💞*
   *Wattpad:Feedohm*

*19*

  ***

Juyowa tayi tana kallonsu da idonta da suka kad'a sukayi jawur ganin Muhibbar ko numfashi bata yi amma sam hankalinsu ba gareta yake ba, nuna Abdallah tayi cikin rawar murya tace "Me ya sami K'awata Abdallah? Ka fad'a man me ya samu Muhibba? Wallahi kar ka kuskura wani abu ya sameta don bazan tab'a barinka ba Abdallah."

  Babu wanda ya bata amsa sae Abdallah da yayi kan Muhibbar yana kiran sunanta ita kam Maryama ta fice da gudu tana kiran wata nurse da ta fito daga wani d'aki opposite dasu.

  A tare suka shigo da nurse d'in yayin da ta nufi gadon Muhibbar domin dubata amma Momin Hasnar ta tsayar da ita ta hanyar d'aga mata hannu cikin tsawa take fad'in "Ya isa haka Sister Luba karki kuskura ki tab'a ta."

  Cak Sister Lubah d'in ta tsaya yayin da Maryama ta juyi a sak'wane tana kallonta mayar da kallonta tayi ga Abdallah  da yake k'ok'arin daukar Muhibbar   jin abunda momin Hasna ta fad'a

  Cikin tsawa tace yayin da idonta ya cika da k'walla "Karka kuskura ka tab'a man K'awa Abdallah.!

  Tureshi tayi da k'arfi daga kan Muhibbar ta fice da gudu sae gata ta dawo da maza guda biyu a bayanta, cikin k'yarma ta nuna masu Muhibbar yayin da sukayi kanta,  ganin suna niyyar d'aukar ta yasa Abdallah yayi kansu cikin tashin Hankali yana fad'in"Karku tab'a man Mata."

  A harzuk'e Maryama ta juyo tana fad'in "Tun daga ranar da ka soma zaluntar ta na cireka a matsayin mijinta Abdallah."

  "Wallahi ba wanda ya isa ya fitar da ita daga asibitin nan muddun baa biya mu kud'in aikin da aka mata sae dae ta mutu a nan."Muryar Hasna ta daki dodon kunnenta

  Da sassarfa ta k'arasa kusa da ita ta cire sark'ar zinarin da ke wuyanta da yan kunnen ta damk'a a hannun Hasnar ta juya a fusace tana fad'in "Banda lokacin ki yanzu Hasna amma wallahi baki sha Maryama a banza ba, sae na tabbatar maki da bunsurun da ya tara kud'in kika d'auka a k'ark'ashin tafin hannun Maryama yake."

Mazan ta kalla tace "Ku taimaka ku d'auketa mu tafi dan girman Allah."

  Suna fita Abdallah ya bi bayansu yayin Umman shi  ta janyo shi cikin kakk'ausar murya tana fad'in "Ka fad'a man wacece waccan Abdallah.?

  Cikin tashin hankali yace "Matata ce Umma."

Lafiyayyen mari ta bashi tana fadin "Gidan uwar wa ka aureta? da sanin wa ka aureta?

  "K'arya yake Umma wallahi yar aikina ce yake lalata da ita har ya mata ciki shine yace na rufa mashi asiri, har ya kawota asibiti ta haihu yaronta ya mutu, shine ya d'auke nawa ya bata, ki taimaka mani Umma." Hasnar ta fad'a tare da k'ank'ame Yaron jikinta

  "Inna lillahi wa inna ailaihir rajun Amma Allah ya isa Abdallah! Allah ya tsine maka Albarka ashe mugun halinka har ya kai ga haka? har ya kai ga kayi zina har ka samu shege? sannan ka k'wace wa matarka yaro ka bawa karuwarka? ka ci amanata ni mahaifiyarka! kaci amanar matarka wallahi bazan tab'a yafe maka ba."

Cakumar wuyanshi tayi tana fad'in "Meye ribarka Abdallah.?

  Cikin kuka Aisha tace "Me yasa zaki yarda da abunda wad'annan mugayen suka fad'a maki Umma? Me yasa shi bara ki saurareshi ba?kenan bare sun fiye maki d'anki Umma.?

  Duka ta kaiwa Aishan tana fad'in "Ki rufe man baki dan ubanki don wallahi Hasna ta fiye man Abdallah sau dubu."

Banda hawaye babu abunda ke fita daga idanunshi a hankali yake kallon Hasna dake tsaye rik'e da yaro a hannunta yayin da ya mayar da kallonshi ga Mominta tabbas ya yarda mace bala'i ce domin tana iya kaika cikin jahannama da k'afafunka.

MATAR ABDALLAH..Where stories live. Discover now