MATAR ABDALLAH 26

5.9K 512 38
                                    

💧💧 *MATAR ABDALLAH..💥*
        《Almost True Life story.》

                        💥

*©HASKE WRITER'S ASSO💡*
Home of expert & perfect writers

  *MALLAKAR: FEEDOHM💕*
      *Wattpad: Feedohm*

*26*

          **** Yar dariya kawu Dalha yayi kafin yace "Ce man zakayi masu kashe zuciya da farin cikin mai k'osae ne, Amma bawan Allah gaka da alamun mutunci a fuskar ka me ya kaika d'aukar d'iyarka ka ba mutumin da baisan darajar kanshi ba irin Abdallah? Haba kaiko wannan ai shashanci ne aura wa yarinya mutumin da baisan ya juya biyar ta zama goma ba sae dae ya mik'a hannu mace ta basa, to yanzu ai ga irinta nan anje an saka maka yarinya bala'i da kata'i.."

  "Haba kawu dalha gaskia abunda kake baka k'yautawa ko ba komae mu 'ya'yan d'an uwanka ne bai kamata ka dinga mana irin haka ba."Cewar ya salisu dake tsaye bayan Baffa tun da kawu dalha ya fara magana.

  Dalla mashi harara yayi yana fad'in "Munafuki labe ka koma kenan?

  Bai kulashi ba ya juya yana bawa Baffan hakuri sannan yace su shiga daga ciki dan Allah.

  "Babu komai ai."cewar Baffan sannan suka shiga inda suka iske Abdallah kwance idonsa a rufe sae dae da alama ba bacci yake ba.

Sallamar Baffan ya sashi bud'e ido da sauri yana k'ok'arin tashi zaune yayin da Baffan ya taimaka mashi ya zauna tare da kanga bayanshi jikin lamukekken pillow dake jingine.

Cikin kunya ya gayar da Baffan don har ga Allah baya jin zai iya had'a ido dashi.

  Kafar baffa ya k'urawa ido na d;an lokaci kafin ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Ya Salisu yace "Wane irin magana ake masa Salisu?

  "Na hausa ne Baffa. "

"An kuwa samu wanda ya iya aikin sosai kuwa?

  "Eh, Ko yau yazo ya duba shi, sae dae kamar k'ara zaganyewa take Baffa." Ya k'arashe maganar cikin rauni.

  "Allah ya kyauta."

A tare suka amsa da "Ameen."
Bayan ya mik'ene ya kuma dawowa ya tsugunna yana kallon kafar a hankali ya lumshe idonsa tare da kallon Ya Salisun yace "Ko zan iya ganin Mahaifiyarku?
 
  "Batta nan."Ya bashi amsa

"Shikenan nagode k'warae, Allah ya k'ara afuwa sae zuwa gaba idan na dawo." Daga haka ya mik'e ya fita yayin da ya Salisu ya bi bayansa, sab'anin Abdallah da ya kifa kanshi a cinyarsa ya saki kuka sosae tare da nadamar abunda ya aikata wa mutane masu karamchi da tausayi irinsu.

*BAYAN SATI BIYU*

  Shi kam tunda Abban Maryama ya saukeshi ya kasa d'aga k'afarsa daga gurin, zuwa yayi domin k'arb'owa Muhibba takardar sakinta a gurin Abdallah amma yanayin da yaga  Abdallah yayi bala'in tsaya mashi a rai hakan ma ya hana masu tambayar abubda ya kaisu, yayin da maganganun Abdallah suka dinga yawo a k'walwarsa , lumshe ido yayi tare da zama bakin dakalin gidan ya tallabe kanshi, lokaci guda tausayin Abdallah tare da son taimakonsa ya d'arsu a ransa,tabbas bazaya bari a yanke k'afar Abdallah ba dole yayi wani akai, k'aramar wayarsa ya fito a aljihu yayi dialing number wani malami amininsa da yasan yana irin wannan aikin sosai, bayan sun gaisa ne yake fad'a masa halin da Abdallah yake ciki inda ya k'ara da rok'onsa dan Allah gobe ya taimaka yaje ya gansa ko akwae taimakon da zai masa don ya fara zargin ko akwae matsalar jinnu a ciki.

  Amsa masa yayi insha Allahu goben zaizo sae su tafi tare sannan ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya shiga gidan, a tsakar gida ya sami Umman da Muhibba zaune suna fira ya samu gefen tabarmar ya zauna ya rafka uban tagumi.

MATAR ABDALLAH..Where stories live. Discover now