27

5.4K 525 49
                                    

💧💧 *MATAR ABDALLAH..💥*
         Almost True Life Story

    
                        💥

© *HASKE WRITER'S ASSO💡*
Home of expert & perfect writers

 
   *MALLAKAR:- FEEDOHM💕*
   *Wattpad:- Feedohm*

      *# Ku bar ganin laifinta, KE/KAI Dae ina maku addu'ar kar Allah ya jarabceku da ciwon SO domin babu abunda baya iya faruwa.🥰*

*27*

     *Lokutta da dama na kanji rubutun online ya fice man a rai sam saboda babu komae cikinsa face cin mutunci da wulakanci hakan ke hana mani typing baki daya.. Sae dae abunda na tsinta a Shafin Facebook ya saka naji ina bukatar yin typing saboda soyayyar mutanen da bansan su ba, ban san sunayi ba haka suma basu sanni ba amma suke man So Dan Allah yayin da suke man addu'o'i da zuciya d'aya duk a tunaninsu rashin lafiya ya saka mani k'in typing, kuyi hakuri lafiyata lau kawae yanayin rayuwar ne ba dad'i amma daga yau indae ba wani abu ya taso ba na maku alkawarin yi maku typing kullun kullun ba zan kuma maku tsallake ba❣.*

       ***Jingina kai Abdallah yayi a jikin pillown sa yana kallonta, a hankali yake lumshe idonsa tare da bud'esu bisa kanta, bazai yaudari kansa ba bazaya iya rayuwa babu Muhibba ba sae dae wannan karan babu abunda zai hanashi sadaukar da soyayyarshi gareta ba domin farin cikinta, zai hakura da farin cikinsa ya sallama mata domin taje ta auri mutumin da zai iya kula da ita ba irinsa ba mara k'afa gurgu...

  Hawaye masu zafi suka ziraro saman kuncinsa yayin da ya runtse idonsa gam na d'an lokaci, kwantar da kanshi yayi yana lek'en fuskarta daga inda take tsugunne har lokacin bata iya d'ago kanta ba ta kalleshi, a hankali yake hango hawayen ta dake d'iga bisa tabarmar dake shinfid'e tsakiyar d'akin, wani  abu mai d'aci ya tokare mashi kirjinsa yayin da ya lumshe idonsa da suka kad'a sukayi jawur, hannu ya saka ya goge hawayen dake fuskarsa tare da cije lab'b'ansa had'i da girgiza kai lokaci guda.

  Dan murmushi ya kuma saki lokaci guda wanda ya fi kuka ciwo kafin ya bud'e baki cikin sark'ewar murya ya kira sunanta " Muhibbah...!

  Karo na farko ta d'ago ta daura idonta bisa kafarsa har zuwa fuskarsa, wani a zababben kuka ya taho mata ta saka hannu ta toshe bakinta muryarta na rawa take fad'in " Muhibba is succumb (death) Ya Abdallanah."

Lumshe ido yayi a hankali yace "Weep, Weep Muhibbah.."

  Wani sabon kuka ya k'wace mata ta sakeshi a hankali ba tare da duk'ar da kanta k'asa, a hankali ta tsinkayi muryarsa yana fad'in "Kiyi kuka Muhibbah, kiyi kuka yarda kike so, Abdallah ba zai hanaki ba indae hakan zai rage maki rad'ad'in dake zuciyarki Muhibbah.."

  Kukan tacigaba da yi a hankali ba tare da ta saurara ba yayin da yake zaune yana kallonta da idanunsa da suka kad'a sukayi jawur haka lokaci guda yake goge hawayen da suka fitowa daga k'wayar idonsa.

   Baffa ya dafa kafad'arta ya mik'ar da ita tsaye sannan juyo ta ta fuskantar sa cikin sanyin murya yace "Idan kina son Abdallah ba zan raba ki dashi D'iyata, domin bazan so na k'untata maki ba akan abunda Allah ya k'adarta maki a rayuwarki."

  Girgiza kai tayi da sauri tana toshe bakinta da hannu, "Ki fad'a man gaskia Muhibba, shin har yanzu Kina son Abdallah? Shin kin shirya zaki zauna dashi domin Allah.?

  Girgiza kai tayi har lokacin hannunta yana saman bakinta, Maganganun Maryama take tunawa batta so ta karyawa k'awarta alkawarin da ta d'aukar mata haka batta so ta b'atawa Ummanta saboda soyayyarta haka shi kansa Baffa zai bar mata Abdallah ne bawae don yana buk'atar zamansu a tare ba..amma a zahirin gaskia can k'asan zuciyarta babu abunda take muradi irin Abdallanta, bata damu da yarda zai koma a nan gaba ba ita kawae Abdallanta take MURADI a duk halin da yake ciki, wasu hawaye masu zafi fiye dana d'azu suka fara gangarowa saman fuskarta tare da d'iga bisa hannun Baffanta, lumshe ido tayi tana tunani k'aryar da zata fito daga zuciyarta a hankali tace "Bana Sonsa Baffana dan girman Allah mu bar nan.."

Cikin firgici Abdallan ya kalleta lokaci guda yake hango tsabar k'aryar dake cike da k'yawawan idanunta wanda ada babu komae cikin sae tsagwaron gaskia, Sam bai so jin hakan daga bakinta ba, bai so yaji kalmar tsana daga bakin da yafi kowa sonshi fisabilillah ba shi kam ba zai iya tsayar da hawayen dake neman goce masa ba don haka ya barsu suka fara zirara daga idanunsa da babu komae yanzu sae tsagaro SO da KAUNA had'e da muradin Muhibbarsa tare da nadamar abunda ya aikata, Cikin sark'ewar murya yace "Dan Allah ki fad'awa Baffan ki gaskiya Muhibbah, Ki fad'awa Baffa Abdallanki ne Muradinki sae dae bakya buk'atar zama dashi saboda kuskuren da ya aikata maki a baya."

  Ba tare da ta kalleshi ta bud'e baki cikin sanyin murya tace "Muhibba is succumb Ya Abdallah."

  "I Know Muhibba kuma dama ban sawa kaina Muhibbata zatayi k'arko ba don banje gurinta ta sigar da ta dace ba...."

Da hannu Baffa ya dakatar dashi yana kallonta a hankali ya kuma fad'in "Kin tabbata baki sonshi.?

  Da sauri ta cigaba da gyad'a kanta tana kuka kafin ta fice daga d'akin da gudu tana toshe bakinta, bangazar mutun da tayi yasa tayi saurin tsayawa, muryar Hasna taji tana fad'in "Bak'ya gani ne.?

  Da sauri ta ware idonta tana kallonta lokacin da tayi gaba tana fad'in "Mutane kamar wasu masu k'walwar kifi sam basa ganin gabansu."

Har tayi nisa ta kuma juyowa tare da janyo wuyan hijab d'in Muhibbar tana tambayarta "Kamar daga d'akin Abdallah kika fito ko? Me kika yo a cikin? ke ni kamar ma na tab'a ganin wannan fuskar ko.?

  Fitilar wayarta ta kunna ta haske mata fuska, cikin tsawa tace "Muhibba? ke? Uban me ya kawo ki nan?

   Cikin rawar murya Muhibba tace "Sake mani Hijab."

  "Bazan saki ba sae kin fad'a man ubanda ya kawoki gurin Abdallanah."

  "Baffa ne ya kawo ni Hasna, dan Allah ki sake man hijab zan tafi" Ta fad'a a hankali tana k'ok'arin k'wace wuyan hijab d'inta

  "How Dare you." Wani Mari ta sakar mata a kuncinta na dama sae dae bata sauke hannunta ba taji nata a rabon itama a kumcinta na dama, da sauri ta haska wanda ya mareta.

  Bata saurara ba ta d'aga hannu da niyar wankawa Baffan Mari amma taji an rik'e mata hannu a zafafe, cikin sanyin muryarta take fad'in "Kuskure mafi muni kenan a rayuwarki Hasna, karkiyi k'ok'arin tab'a man fuskar mahaifi don ban had'asa da kowa ba a duniyarmu haka bazan d'auki wulakanci komi k'ank'antar sa ba indae akan Baffana nane."

  Hannun Baffa ta kama tana fad'in  "Mu tafi Baffana zan juri komae akan Abdallah amma bazan juri komae k'ank'anta abu aka maka ba, Dan Allah mu tafi Baffa."Ta k'arashe maganar idonta tab da hawaye.

Duk jarumta irin ta Baffan bai san lokacin da tausayin tilon yar'sa ya sa hawaye gangarowa daga idanunsa ba, tabbas yasan karya take babu wani da zata so sama da Abdallah haka nan tak'isa domin farin cikinsu, Juyar da kai yayi yana rok'an Allah Ubangiji ya zab'a mata abunda yafi alkhairi a rayuwarta, Tare da dunk'ule takarda da Allah ya basa ya sakata a aljihunsa na wando don baya jin zai iya fad'a mata bare har ya bata yanzu...

  Tunanin Baffa ya tsaya cak ta yarda zai dauke Muhibbar daga garin ta yarda zaiyi nisa da ita ko Allah zaisa ta manta da Rayuwar Abdallah baki d'aya tare da kwanciyar hankalinta, yanke shawara yayi ya sayar da gidan da suke ciki su tashi baki d'aya su koma k'auye da zama sannan ya kama sana'ar kiwo da noma hakan zai fi masu kwanciyar hankali baki d'aya, Sam ba zai gaza ba gurin rok'an Allah ya zab'awa Yarsa miji na gari ta sake aurenta ko ta samu kwanciyar hankali, Rungumeta yayi sosai ba tare da ya sani ba...

#Feedohm

MATAR ABDALLAH..Where stories live. Discover now