RANAR AURENA 05

7.2K 450 20
                                    

💧💧 *MATAR ABDALLAH.!*💥
                   True Life Story.!

                              💥

*HASKE WRITER'S ASSO.💡*
Home of expert & perfect writers

*MALLAKAR: FEEDOHM💞*
   *Wattpad:Feedohm*

  *05*

     Cikin ikon Allah ranar asabar da misalin k'arfe sha d'aya da rabi na safe aka daura aurena da Abdallah akan sadaki naira dubu hamsin. Bayan an dawo ne tsegumi ya tashi wae sam auren bayyi mutane sosae ba, don duk a tunanin jama'a za'a ga manyan mutane daga jahohi daban daban amma sae aka samu akasin haka, wasu ma fad'i suke wae kamar babu yan uwan Abdallah shak'ik'ai a gurin daurin auren dan basu ga masu kama dashi ba ko ta jini daga abokai sae mutanen azik'i...

  Nikam babu abunda ya shalleni bare ya dameni, gani nake don ba'a ga mai kama dashi ba sae ace babu danginshi a ciki? koko sae ya fad'awa jama'a wannan yan'uwana ne.? A raina kam na hak'ik'ance ko da Abdallah shegene babu abunda zai ragu a cikin zuciyata..

  Maryama ta shigo ta mik'o man Peak da markad'ad'd'ar cucumber tana fad'in "Mutane munafukaine wallahi."

  Nasan itama maganar ta jiyo don haka nace "Me kuma akayi Maryama?

Boye man tayi wata k'ila bata so raina ya b'aci don haka tace "Ke ba komae, Ki had'a kisha bara naje na shigo dasu Shatu yanzu suka iso kuma basu san gidan ba."

  Hannunta na janyo ina dariya "Kisa yaro ko su Amina su shigo dasu wallahi bana son rabuwa dake."

  Tsaki ta saki tana harara tace "Ke ni bana son gulma k'ya ma fad'i wanda baki son rabuwa dashi amma bani ba."

  Dariya nayi ina fad'in "Kayyasa Maryamata akwae ki da banzar fassara."

Itama dariyar tayi ta fita tana fad'in "Ki tashi ki sake wanka k'awata."

*

  Bayan an gama daurin Aure Abdallah kam gidan Ummarshi ya nufa, Ya iske zaune tsakar gida tana wanke wanken kayan da ta gama sana'a dasu, kusa ita ya tsugunna yana nannad'e babbar rigar da ya sha..

Da murmushi ta kalleshi kafin tace "Ka ganka kuwa Abdallah kayi kyau sosai yarda kasan sabon ango."

Shima d'an murmushi yayi kafin yace "Ina Wuni Ummana?Baki san angon bane Umma, domin daga daurin auren Mahmud nake."

"Ba dai Mahmuda da na sani aka daurawa aure Abdallah? Me yasa baka fad'a man ba, ai da ko addu'a na masu ko banje wa mamarsu walima ba."

  Goro ya fiddo da dabino ya mika mata yana fad'in "Ba sae kinje ba Umma daga nan ma k'ya iya masa addu'ar samun abunda ake buk'ata."

Ba ta kawo komae ba ta k'arba  tace "Allah yasa alkhairi Abdallah, ya Albarkacesu da zuri'a d'ayyaba, yaya wajen su Hasna da fatan tana lafiya.?

  "Lafiya lau Umma." Sun d'an tab'a fira sannan ya mata bank'wana ya tashi...

  A waje ya iske Kawu dalha yana nik'a yayi bad'a bad'a da garin masara fuskarnan tayi fari tas sae idanunun da ake gani.

  A Hankali ya matsa yana fad'in "Barka da wahala Kawu dalha ka ganka kuwa? wallahi kaje kayi wanka in ba haka ba sae an bar kawo maka nik'a."

  "Barka kadae mijin hajiya, nagode Allah da gumi na ake nema ba wata ke bani ba, shege mai matattar zuciya."Ya bashi amsa ba tare da ya kalleshi ba

  Dariya yayi mai sauti ya fiddo da goro ya mika mashi yana fad'in "Haba kawu meye na fad'a kuma? Ka ga ni ba fad'a nazo ba  goro na kawo maka don nasan dae bara ka iya saya da kud'inka ba."

MATAR ABDALLAH..Onde histórias criam vida. Descubra agora