ITA WACECE? BABI NA D'AYA 1

7.8K 307 27
                                    

❄🏵❄🏵❄🏵❄
*ITA WACECE?*
🏵❄🏵❄🏵❄🏵❄

*Written* ✍
*By*
*NUSAIBA IBRAHIM USMAN ZANGO*

*Star Nucee36O*

ITA WACECE?

i

*GODIYA*
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai masanin kowa da komai. Ina k'ara godiya ha Allah subhanahu wata'ala daya bani ikon rubuta wannan littafi Allah ka k'ara bamu kaifin basira da ilimi mai albarka Ameen.

ii

*SADAUKARWA*
Nasadaukar da wannan littafi ga KHADIJA CANDY kin cancanci haka harma kinwuce Ubangiji Allah ya bar zumunci ya kuma k'ara daukaka Ameen.

iii

*GABATARWA*
Wannan littafin mai suna *ITA WACECE?*.Nayi shine don nishad'antarwa fad'akarwa da kuma wa'azantarwa

*GODIYA TA MUSAMMAN*
Bazan manta da kuba k'awayen arziki.
Xeebnab yakasai Queen
Suwaiba U Adam's Subie
Nafeesat Yusuf Feenah baby
Ayusher Musa Iliasu Queen

*IDON MIKIYA WRITER'S ASSO*🦅

*DEDICATED TO KHADIJA CANDY*

*_Wattpad StarNucee360_*

*Babi na d'aya (1)*

Tsaye take tabama k'aton filin tsakar gidan baya hannun ta rik'e da tiyo tana bayin wa filawoyin(flowers)da sukai wa gidan k'awanya ruwa, tanayi tana wasa da ruwan da gani kasan tana cikin nishad'i duk ta jik'e jikin ta.
Y'arinyar da batawuci shekaru goma sha shida(16) ba.cabko mata hannu taji anyi arazane tayi unk'urin guduwa wacce ta rik'eta bata saketa ba sai kawai ta nemi afkawa filawoyin(flowers) da sauri ta fisgo ta,ta fad'o jikin ta cikin gurb'atacciyar Hausarta tace"Khadija kina soro fa sosai"sai yanzu dataji muryar mai maganar sannan hankalin ta ya d'an fara dawowa jikin ta ta d'ago kai ta kalle ta idon ta cike da tsoro har yanzu,cikin kayan kuku matar take,ta kuma daurawa da cewa"kajika kanka jeka cire kazo nan"Khadija da tunda matar tafara magana bata ce uffan ba ta gyad'a mata kai ta wuce zuwa sashin su da gudu tana tsalle tsalle, izuwa yanzu tsoron ya sake ta sashen su ta nufa da y'ar sallamar ta tashi ga Ammi ta tadda zaune tana tankad'e"ta amsa mata sallamar sannan tace"Ammi Suzana ce tace nazo na canza kaya na naje tana jirana" Ammi bata ce k'ala ba, ta wuce ciki ta canza kayan ta fiddo wad'anda suka jik'e ta baza su kan bishiyar da suke shanya ta dawo gun Ammi tace Ammi natahi Khadija har takai bakin k'ofa ta tsinkayo muryan Ammi na cewa"sufa _haka suke kiranta don b'oye sunan mahaifiyar mijin ta_ kinsan dai baso nake inaganin ki kina rab'ar cikin gidan nan tunda Hajiya da Alhaji ba so suke ba tunda ma munsamu har sun bamu nan muna rab'awa ai sai mu rik'e talaucin mu amma ke naga kina son zuwa kina rab'ar su amma duk sanda Hajiya ta kamaki a cikin gidan ta ba ruwa na komai zata maki ta maki ba ruwa na"jikin Khadija duk yayi sanyi tace "to Ammi insha Allah bazata kama ni ba taya suzana aikin girki fa nake"Ammi rik'e baki tayi Sufa girki kuma kinsan kuwa sabo da kyamar talakawa yasa Hajiya d'auko y'an aiki a k'asar waje wallahi ki shiga taitayin ki, ki kuma rufa mana asiri"Ammi kimin addu'a insha Allah ba komai""hmm toh Allah tsare"Amin sufa ta ce" sannan ta k'arasa fita.

Inda ta bar Suzana nan ta taddata ta rik'a mata hannu suka wuce cikin gidan kai tsaye kitchen suka nufa suka kama aikin had'a abincin kamar kullum, Suzana na kwada ma Sufa yadda ake girki.

Babban gida ne wanda yakusan rabin wani unguwar, Security's ne ta ko ina da gurin zaman su. Da farko in ka wuto gate din farko da securitys ne ke gadin gate din sai gate na biyu kuma wanda Malam fillo ke kula da alhakin bud'ewa da kullewa, in kayi gaba kuma harabar gidanne tafkeke flowers sun masu k'awanya, tafka tafkan gidaje ne guda uku masu hawa uku, uku a d'aya gefen dama, gefen hagu sai d'aya kuma yana kallon mai shigowa gidan, ko wanna k'ofar shiga sashen akwai k'ofa da akayi na flowers ya zagaye k'ofar har sama, koraye shar da fure fari da ja ajiki. Ta bayan gefen hagu nan ne d'akunan ma'aikatan gidan wanda babu abunda aka rage su da shi, ta gefen dama kuma flat ne madaidaici nan Malam fullo yake zama da iyalan sa.
Sashen da ke kallon mai shigowa ta baya lambu ne da shuke shuke iri daban da ban da kujerun zama ga rumfar ciyawa flowers duk sun zagaye su.

K'urr! k'urrr!! k'urrr!!! k'arar waya ce ta gauraye hadaddan palon da yasha kayan alatu iri da ban da ban. Na'urori ne kawai ke aiki sai kuma k'arar wayar da ke tashi tun d'azu kyakkawar matashiyar mata ce take saukowa daga matattakala kamar mai tausayin kasa cikin nutsuwa tai gurin wayar ta d'aukq tana murmushi ta kara a kunnen ta"Hello".

Daga cen k'asar CHIKAGO a wannan katafaren babban otel d'in HILTOL HOTEL kwance yake bisa katafaren gadon sa na alfarma da waya kare a kunnen sa na hagu"Mommo i really miss u all ina papa kozaki had'amu mu gaisa.

9ja
*Zariya*
_"Ba damuwa 1mint", zare wayar tayi daga kunnen ta tayi y'an danne dannen ta sannan ta maida wayar a kunnen ta"Son papan ka na kan layi"._

*CHIKAGO*
_Hilton Hotel_
"Ok Hello papa ya aiki".

9ja

*FCT ABUJA*
"Hii Son ya karatu"

*CHIKAGO*
_Hilton Hotel_
"lahiya papa ya aiki"

9ja
*FCT ABUJA*
"Lahiya Alhamdulillah, ya karatu"

*CHIKAGO*
_Hilton Hotel_
"Mun kammala duk na k'osa na dawo na ganku"

9ja
*ZARIYA*
"Son mai zai kawoka nan 9ja yanzu kawai kayi zaman ka nan komai kake so baka da matsala".

9ja
*FCT ABUJA*
"Gaskiya Mommon ka ta fad'a kayi zaman ka kawai ka fara aikin ka anan in kana son ganin mu sai ka gaya mana muzo hakan yafi Son, bana so kazo gida kafara wahala babu komai a 9ja sai wahala shiyasa tun kana karami muka fitar da kai don kasamu ingan tacciyar rayuwa da jin dad'in ka,come on son kadaina tunanin zuwa 9ja".

"Inma kasamu mata kayi Auren ka nan kaji dad'in rayuwar ka".

*ZARIYA*
"A'a aure anan zan sama maka mata ko cikin y'ay'an k'awaye nane sai ayi auren mu turo maka matar nan, amma ban y'ar da da auren turawannan ba".

*FCT ABUJA*
"Kaji abun da Mommon ka ta fad'a so kabar zancen zuwa gidan 9ja pls"

*CHIKAGO*
_Hilton Hotel_
"Mommo, papa mai yasa bakwa k'aunar nayi maku maganar zuwa ta gida 9ja ne sai kuyi ta bani Uzurin da haryau baikai ya hanani zuwa gida ba. Batun kuma yin aure bana buk'ata ni da kaina zan zab'a wa kaina mata".

"Aiki kuma a k'asata ta gado nakeson nayi Nima na bada gudun mawa wa k'asa ta bawai nayi karatu ba na b'ige da taimaka ma wata k'asar ba tawaba kamar yadda da dama wasu y'an 9ja sukeyi, so wannan time d'in gida nakeson zuwa shekara ashirin da tara(29) ina wata k'asar".

9ja
*ZARIYA*
"Son na gaya maka kada naga k'afar ka a k'asar nan".

*FCT ABUJA*
"Son pls kada kazo ka gaya mana komai kake buk'ata mu masu yi maka ne".

*CHIKAGO*
_Hilton Hotel_
"Gida nake son zuwa papa bansan maiyasa kuke rejecting d'ina, na zuwa gida ba saikace kuna boyemin wani abu nafayi girman da zan iya kula da kaina".

9ja
*FCT ABUJA*
"Damm gaban Alhaji Hahmud isa Naira ya buga sai zufa yafara karyo masa kitt ya katse wayar don ya daburce.

*ZARIYA*
Mtswww taja tsaki itama kitt ta katse wayar.

*CHIKAGO*
_Hilton Hotel_
Shima cire wayar tasa yayi daga kunnen sa ya zabga tagumi yana tunani wad'annan iyayen nasa da basason ya koma gida 9ja.Nifa na dad'e da fuskan tar suna boye min wani abu but miye? tambayoyi ya farayi ma kansa.
Maiyasa basa so naje gida?basa so nane? In kuma basa sona ai baza su haifeni ba? Ko wani abu suke b'oyemin basa so na sani?, wa zai bani amsar tambayoyi na?

Yanzu aka fara

_vote_
_Share_
_Comment_
_And Follow_

*Muna Mugun Tare*🤝
*Taku Har Kullum*👱🏼‍♀
*Star Nucee36O*✨💫

ITA WACE CE? (Complete Book1)Where stories live. Discover now