ITA WACE CE? BABI NA SITTIN 60

572 49 6
                                    

❄🏵❄🏵❄🏵❄🏵

         *ITA WACECE*

🏵❄🏵❄🏵❄🏵❄

*Written* ✍

*By*

*NUSAIBA IBRAHIM USMAN ZANGO*
_*Star Nucee36O*_

*DEDICATED TO KHADIJA CANDY*

*_Wattpad StarNucee360_*

*Babi Na Sittin (60)*

_Don't mind the errors plsss_

_Don Allah Readers  kuci gaba da hak'uri danii love you all fisabilillah_

_*Bismillahirrahmanilrahim*_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

  _*Kwanci tashi asarar mai rai*_

Sufah tana ta shirin fara jarabawar makaranta, ga kuma shirin tarbar Aminiya Nusaiba zasu dawo murnar tayi mata yawa, amma abun dayake damunta shine bata da mai kaita airport don tarban Aminiyar ta

Shiyasa tasamu guri ta rakub’e tai shiruu, gashi bata son ta b’ata farincikin ta da wannnan tunanin.

Wani nannauyar bacci ne ya d’auke ta batare da ta shirya ba, cikin baccin sai tafarayin mafarkin

_[Tana cikin tafiya sai taga wani k’orama mai kyaun gaske ya bata sha’awa sai kawai ta yanke hanya ta gangara, ga rairayin k’asa agurin gashi kana ganin komai nacikin k’oramar ,ga garai-garai d’in ruwar sai kaiwa da komowa yake, ga ranar da ake k'wallawa ita ta taimaka gurin k’ara taimaka wa k’oramar gurin ganin komai dake cikin ruwar_

_Jitai kawai ta kwad’aitu dason yin wanka a k’oramar, batai wata-wata ba ta rage kayan jikin ta, ta nufi ruwan_

_K’afarta guda tafara sanyawa a cikin ruwan sannan ta kuma sanya d‘ayar, ruwan da d’umin sa tafiya takeyi cikin ruwan tana watsa ma jikinta ruwa tana dariya da tayi nisa da tafiya lokacin ruwan ya kai mata har wuya sai ta dakata daganan ta sami dutse ta taka ta hau saman sa ta zauna tanata murmushi abin ta, tana sanya hannu tana d’ibar ruwan tana wanke jikin ta dashi_

_Iska yafara kad’awa da d’an k’arfi sosai har ya razana Sufah, iskar takai kamar mintuna uku sai kuma ta lafa, amma yanayin iskar gurin ya k’aru_

_D’aga kanta keda wuya sai tayi arba da wani kyakykyawan saurayi shima yana zaune bisa dutse  acikin ruwan kamar yadda take zaune, sai dai shi ya bata baya, ta tsura masa idanu tana tunanin inda tasan shi amma ta kasa tuna inda ta sansa_ 

_Sauka tayi tafara k’ok’arin fita daga cikin ruwan don tagama wasa da ruwan, tazo dab da bakin ruwan zata fice sai taji tsantsi na maidata baya tayi hakan yafi a k’irga amma fitan yaki yuwuwa, sai cen kuma taji kamar ana janta, tunawa tayi da tafaga mutum d’azun, sai tafara kwalla masa kira don yakawo mata agaji_

_“Bawan Allah kazo ka taimakeni don Allah kaj... ”_

_Bata k’arasa mai zatace ba taji an janyeta cikin ruwan fanjam! _fanjam!  tafarayi naganin ta ceci kanta amma ina k’asa take tayi cen sai taga wani farin haske dogo kamar maciji yazo yana k'ok'arin ratsawa ta k'asan ta ya shiga jikin ta nan tafara mammatse k'afafu amma ina yana zuwa ya ratsa ta ya shiga cikin cikinta ta k'asa, sai kuma taga tafara tasowa sama har tazo bakin gab’a a sukwane ta tashi da gudu tabar gurin]_

ITA WACE CE? (Complete Book1)Where stories live. Discover now