ITA WACECE? BABI NA SHA BIYAR 15

1.2K 80 0
                                    

❄🏵❄🏵❄🏵❄🏵

*ITA WACECE?*

🏵❄🏵❄🏵❄🏵❄

*Written* ✍

*By*

*NUSAIBA IBRAHIM USMAN ZANGO*

_*Star Nucee36O*_


*IDON MIKIYA WRITER'S ASSO*🦅


*DEDICATED TO KHADIJA CANDY*

*_Wattpad StarNucee360_*

*Babi na Shabiyar(15)*

_Fabs Hotel G.R.A_

4:16

Sanyin Asubahi ne ya farkar dashi daga suman da yayi addu'a yake tayi yana nanatawa da kyar ya samu ya ja jikin sa zuwa bakin gado ya haura saman gadon ya kwanta yana maida numfashi, karatun alqur'ani mai girma ya kunna da kyar, ga kansa na masa wani azababben ciwo jikin sa duk ya mutu,wani baccin wahala ne ya kwashe sa bashi ya farka ba sai k'arfe goma da minti ashirin da takwas 10:28am ba laifi yaji dan k'arfin jikin da kyar ya tashi ya shiga makewayi ya watsa ruwa ya d'auro alwala ya fito da tawul d'aure a k'ugun sa gurin ajiye kayan sa ya nufa ya sanya farar jallabiya kal sannan ya shinfid'a sallaya ya fara sallah saida ya jero duk sallolin dake kansa ya jima yana addu'oi kafin ya tashi, shirin tafiya gun aiki ya fara,da sauri sauri briefcase d'in sa da rigar likitocin sa ya d'auka ya fito direba ya gani zaune yana jiran fitowar sa gaishe sa direban yayi sannan suka kama hanyar tafiya Dr Mun'im ya tambayi direban gun da zai tsaya ya karya kafin su k'arasa Asibitin don rabon sa da abinci tun wanda ya ci jiya da safe a Niger.

Suna zuwa Zango direba ya tsaya ya faka motar a inda aka tanada Dr Mun'im ya kalligun *Zariya Suya Sport* yana nanata sunan a zuciyar sa fitowa yayi ya kalli direban yace"ka tabbata sun iya abinci?"gyad'a kai direban yayi kamar wani jankai yace"sosai ma ranka shi dad'e likita ai indai abinci ne inkazo nan kankat kenan"Dr Mun'im yace ma direba"bismillah mu shiga ciki", sosa k'eya direba yayi yace ma Dr Mun'im"ranka shi d'ad'e likita aini iya hurumina kenan n... Dr Mun'im ya dakatar dashi yace"aini nace ba rok'o na kayiba muje banson musu"sum sum sum direba ya wuce suka kama hanyar shiga ciki, direba yana mamakin shi ba ruwansa da girman kai.

Korayen ganyen fulawoyine shar shar sukai ma gun k'awanya gunin ban sha'awa, da nishad'i ga fafaren k'arafunan da aka zagaye gun dashi ga fararen kujeru da tebura daga cen ciki kuma shima gun zamane da kujerun anyi gun kamar bukka saman an masa rufu da ciyawa gefe wasu adon duwatsu ne sunyi tsoro ga wani jan wuta dake haskasu suna haske mai jan hankalin mai kallon su gaskiya gun nan ya burgeni sosai.

Ciki suka shiga shida direban suka zauna bayan Dr Mun'im ya bada oden abincin daza suci,bada jimawa ba aka kawo masu suka fara ci, abincin gun yayi ma Dr Mun'im dad'i sosai bayan sun kammala ci Dr Mun'im ya biya suka bar gun, suka d'auki hanyar Asibiti.

_Shika Hospital_

Suna isa Dr Mun'im ya nufi inda sauran abokan aikin sa suke. Sunji dad'in ganin shi saidai yazo a makare don haka aikin sun

taru da yawa cikin gaggawa yasa marasa lafiyar suka fara shigowa yane duba su.

Wad'anda za'ayi masu aiki yana turasu inda ya kamata wad'anda kuma maganine kawai suke buk'ata suma yana turasu inda zasu karb'i magungunan, haka suka dinga duba marasa lafiya har zuwa k'arfe shida 6:00pm sannan suka tashi direban su ya d'auke su zuwa masaukin su dake *Fabs hotel G.R.A* suna sauka kowa yayi d'aki sa.

Dr Mun'im ya na shiga d'aki ya rage kayan jikin sa ya fad'a wanka yana fitowa ya yi addu'a a ruwa ya sha ya tofe jikin sa,bada jimawa ba akayi kiran sallar magrib alwala yayi ya fito ya nufi masallaci, bashi ya dawo ba sai da akayi sallar ishsha'i.

Bayan ya kammala cin abinci na'ura mai kwakwalwa ya janyo ya kunna ya fara danne danne ya kuma kunna Datar wayar sa sak'onni ne suka dinga shigowa rututu rututu sha kamar zuban ruwan sama.

Zab'an sakonnin ya keyi yana karantawa indai ya kula sakon yana da muhimmanci zai karanta, ahaka ya kammala dubawa, ya kashe Datar ya kulle na'ura mai kwakwalwar ya haye gado da addu'oi a baki sa.

_Washe Gari_

Bayan sun isa gun aiki Dr Mun'im tare da Dr Aminu yana masa bayanin rashin lafiyar da ke damun wata mara lafiyar sa mai suna Sufah ko itama zata samu shiga cikin tallafin nasu, don Dr Aminu ya lura suma masu neman taimako ne shiyasa yake masu k'ok'arin samun wannan tallafin, tunda Dr Aminu ya ambaci sunan Sufah gaban Dr Mun'im ya buga...

_vote_
_Share_
_Comment_
_And Follow_

*Muna Mugun Tare*🤝

*Taku Har Kullum*👱🏼‍♀

*Star Nucee36O*✨💫

ITA WACE CE? (Complete Book1)Where stories live. Discover now