ITA WACECE? BABI NA ASHIRIN DA BIYAR 25

1K 63 0
                                    

❄🏵❄🏵❄🏵❄🏵
*ITA WACECE?*
🏵❄🏵❄🏵❄🏵❄

*Written* ✍

*By*

*NUSAIBA IBRAHIM USMAN ZANGO*
_*Star Nucee36O*_

*IDON MIKIYA WRITER'S ASSO*🦅

*DEDICATED TO KHADIJA CANDY*

*_Wattpad StarNucee360_*

*Gaisuwa ta Musamman Gareku, Members na group d'in ITA WACECE Kad'an daga cikin ku*

_Naimat Hashim_
_Nana Bilqeesu(Ashezi)_
_Ameena_
_Mai.gado..jinari_
_Fateema _
_Nahnah_
_Rukayyat Abubakar_
_Sauda Namadi_
_Nafisa Gada_
_Jidda_
_Ummiey_
_Mommmy Aneesah( meenat)_
Mom Ameer_
_Maryam m kashim_
_Fatymah Gimba_
_Zaynababu9_🤷‍♀
_Fateema Usman_😘
_islah khair_
_Hajara_
_Miss~meerah_
_Rashida Bello Maman_ _Salim_
_Sfata_
_Maman Ramlat_
_Bishra Al-Ameen_
_Safiyya Ibrahim_
_Sadyn mamee_

*Babi na Ashirin Da Biyar(25)*

Tirka tirka akayi sosai agun tsakanin Alhaji Mahmoud Isa Naira da y'an sandar gurin fafir yak'i yarda da k'udirin y'an sandar cen dai da su Fu'ad sukaga abun yaki yuwuwa dole suka matso kusa suka shiga maganar, suka fara ba Mahaifin Dr Mun'im baki nan ma tsofaffin gurin wasun su suka sanya baki amma ina kamar ma k'ara tinzirashi suke, yanata masifa yana bambami ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba yana cewa

"nifa bazan yarda a tonemin d'a naba daga makwancin sa bayan Allah yayi masa sutura, wannan ma ai tozarci ne ni kukeson ku tozarta in banda haka kowa yasan d'annan rasuwa yayi, to don haka ku shafa ma kanku lafiya kubar gurinnan tunkafin raina ya kara b'aci in ba haka ba saina kaiku k'ara kotun k'oli mu fafata shari'a, har sai infa k'arfina ya k'are"

Dr Fu'ad ne yayi k'arfin halin cewa"Alhaji kayi hak'uri ka barsu suyi aikin su tunda su turo su akayi asibiti kawai za'a da gawar ayi bincike kuma ma ai za'aiya yin komai a gaban ka ka gani, da an kammala bincike za'a dawo dashi akuma yi masa sutura"

Kallon uku saura kwata Alhaji yayi masa,Fu'ad dayaga haka sai ya matsa kusa da takwarar sa Dr yace

"Alhaji kayi hak'uri kabasu shi ni zan bisu duk wani abu da ake ciki ni zan dinga sanar da kai kuma insha Allah zanyi k'ok'arin insun kammala binciken su adawo da shi makwancin sa

Kowa agun shiru yayi suna kallon Alhajin yanda ya tak'ark'are yana masifa kamar ba jimamin mutuwa ake ba, da dai y'an sandar sukaga wankin hula zaikai su gayin dare, sai kawai suka kasu gida biyu, kashi d'aya suka tare Alhaji kashi d'aya kuma suka isa gurin kabarin suka fara tone sa cikin k'ank'anin lokaci suka tono sa suka wuce dashi cikin mota, y'an sandan da suka tare Alhaji suka barshi suka nufi gun motar su suka tada suka bar mak'abartar.

Alhaji Mahmoud Isa Naira kamar zai ari baki don fad'an da yake yi,jama'ar gurin sai ba Alhaji hak'uri sukeyi.

Gashi yanason yakira lauya yashigar da k'ara amma kuma yana tsoron *Allura ya tono garma* garin bincike-bincike abinciko masa *b'oyayyiyar sirrin sa* amma don kada y'an gurin su gane burga yakeyi, sai ciro wayar sa daga Aljihu yayi kamar ya danna kira ya kara a kunne ya fara magana cikin d'aga murya

"Barista duk inda kake kayi maza kazo Zaria ka sameni, akwai wani case babba da zakayimin aiki akansa, kabiyo jirgi ne ba ta mota ba saida yayi jimm sanna ya zare wayar daga kunnen sa ya zira aljihu shida tawagar sa suka tafi.

Sannu ahankali jama'ar gurin suma suka watse, su Dr Fu'ad dama tuni sukabi motar y'an sandar zuwa asibiti tunda burin su yacika.

_A.B.U Teaching Hospital Shika_

Suna isa asibitin kai tsaye d'akin bincike aka nufa dashi, bayan sun cire likafanin, likitoci sama da goma ne a kansa kowa da fannin dayake bincika akai, bayan kowannen su ya kammala nasa binciken sai yaxo ya sanar da Dr Fu'ad sakamakon amma duk ciki ba wanda ya nuna alamar doguwar suma ne, tun karfe 8:56am suka shiga dakin binciken basu suka fito ba sai k'arfe 5:49pm.

Cikin Sauri Fu'ad ya tari gaban Dr Fu'ad yana tambayar sa ko ansamo sa amma yanayin fuskan sa kawai ya sanar dashi babu nasara cikin sanyin jiki ya kallesa yace,

"muje mu daukesa mu maida shi, asamu yau a maidashi makwancin sa ba sai ya kara kwana a doran k'asa ba"

Dafa kafadar sa Dr Fu'ad yayi

"Sai hak'uri haka Allah ya so, mutuwa riga ga kowa, muma ita muke jira kuma duk soyayyar mu da shi baikai wanda iyayen Sa suke masa ba, da shikansa wanda ya halicce mu yanzu babu abun da yake buk'ata agare mu sai addu'ar mu shine kadai zamu nuna masa irin soyayyar da muke masa.

_Gida_

Bayan an dawo da shi gida wanka aka kumayi masa akayi masa Sallah sannan aka kuma daukansa zuwa mak'abarta.

_MaKaBaRtA_

Gyara kabarin aka kumayi kafin masu kawo gawan su k'araso bada jimawaba sai gasu sun iso da gawar ijeshi bakin kabarin sukayi sannan akafara yin jawabi game da rayuwar sa data gabata fa kyawawan ayyukan Sa sannan limamin yace kowa ya Kalli gabas yayi masa addu'a dai-dai gwargwadon iyawar Sa, duk sun kalli gabas suna addu'a sai Alhaji Mahmoud Isa Naira yaga kamar makara ya motsa murza ido yayi sosai ya kuma tsura ma makaran ido ya jima ahaka bai kuma ganin ta motsa ba tsaki ya saki acikin zuciyar sa yace

"abunma harda kizo yakemin"

har aka kammala addu'ar akazo aka d'aukesa aka sanyasa cikin kabarin aka fara mai da k'asa ana rufewa sai ganin....

_vote_
_Share_
_Comment_
_And Follow_

*Muna Mugun Tare*🤝

*Taku Har Kullum*👱🏼‍♀

*_Star Nucee36O_*✨💫

ITA WACE CE? (Complete Book1)Where stories live. Discover now