ITA WACECE? BABI NA HU'DU 4

1.8K 135 2
                                    

❄🏵❄🏵❄🏵❄🏵

*ITA WACECE?*

🏵❄🏵❄🏵❄🏵❄

*Written*✍

*By*

*Nusaiba Ibrahim Usman Zango*

_*Star Nucee36O*_

*IDON MIKIYA WRITER'S ASSO*🦅

*DEDICATED TO KHADIJA CANDY*

*_Wattpad StarNucee360_*

*Babi na Hud'u*(4)

*CHIKAGO*

_Hilton Hotel_

'Kara lallatsa wayar yayi kuma ya kara a kunne bada jimawa ba ya fara magana

"Hello ina magana da Fu'ad ne pls".

9ja

*KADUNA*

_Kabala Doki_

"Na'am shine ke kan layi".

*CHIKAGO*

_Hilton Hotel_

"Koda yake nasan bazaka gane mai magana ba(is been long time) amma nasan ai kasan Alhaji Mahmud Isa Naira Zariya".

9ja

*KADUNA*

_Kabala Doki_

"Oh oh oh kaddai Mun'im d'a d'aya tilo ga Alhaji Mahmud Isa Naira da Hajiya Aisha Aliyu Naira d'an gata kuma shalele"

"Ashe zaka iya zumunci"

*CHIKAGO*

_Hilton Hotel_

"Ah haba kune dai ba zumun ci ina shama ko bakai bane shahada kawai nayi na kiraka"

9jaa

*KADUNA*

_Kabala Doki_

Hhhhh"amma ina kasamu lambana donni duk iya k'ok'ari na bansamu ba nasha zuwa gidan ku ba'a barina na shiga wai sai da sanin masu zuwa, wani mai gadin gidan ku ne mai kirki ya hito zaije masallaci muka gaisa nake tambayar sa labarin ka yace aishi tun zuwan sa gidan baima san suna da wani d'a ba don bai tab'a jin labarin sa ba ma sai yau nan mukayi sallama nace masa ni mak'ocin su ne na nuna masa gidan mu to kullum inna shiga Zariya mukan had'u mu gaisa kuma saina tambaye sa ko yaji labarin ka amma shiru.

*CHIKAGO*

_Hilton Hotel_

Murmushi Mun'im yayi yace"Allah sarki a Facebook naganka inasha ko bakai bane naga harda kid kardai naka ne.

9ja

*KADUNA*

_Kabala Doki_

"Oh Abokina"y'ay'an ka ne fa".

*CHIKAGO*

_Hilton Hotel_

"Woow aboki na yanzu harkayi aure harda kids masha Allah".

9ja

*KADUNA*

_Kabala Doki_

"Hahaha to kai yaushe zaka kiramu ne na fa k'osa naga ranar" ya k'arasa maganar cikin dariya.

*CHIKAGO*

_Hilton Hotel_

Hmmmm"Aure tukuna gaskiya donni y'ar k'asata nakeson aure gaskiya don haka bama zancen Aure yanzu har sai nadawo gida tukunna".

9ja

*KADUNA*

_Kabala Doki_

"Lallai bako rana kenan ".

*CHIKAGO*

_Hilton Hotel_

"Dashi mana amma ba yanzu ba"

Da haka suka cigaba da hirar su cikin raha sannan sukayi sallama.

9ja

*ZARIYA*

Kwance take ta rufu da zannuwa da yawa amma kamar bata rufu ba sai makyarkyatan sanyi take hakwaranta sai dukan junan suke, suna bada sauti mai d'an k'ara.

"Sufah! Sufah!! Sufah!!!"

Da k'arfi take Kiran ta dataji shiru sai ta tako zuwa bakin d'akin ta, tayaye labulen tana k'ara kwad'a mata kira, don tasan ta d'a nauyin barci,duk sahe kafin ta, tashi barci ta shirya zuwa makaranta sai anyi ta fama sannan amma yanzu sai taga sab'anin haka, kwance ta ganta ta rufu da zannuwa sai rawan d'ari take, da sauri Ammi ta k'ari sa shiga d'akin ta yaye zannuwan jikin Sufah da ta rufu ta d'aura hannun ta a wuyar ta, taji zafi sosai, da sauri ta hita taje ta d'ibo ruwa ta had'o da tsumma d'akin, ta dawo ymta cire wa Sufah riga sai shimin jikin ta, sannan ta d'auki tsaftataccen tsumman ta tsoma cikin ruwan ta matse tafara goge mata jiki da shi cikin yardan Allah zafin ya sauka, fita Ammi ta kumayi ta yo mata jik'e jik'en maganin gargajiya tazo ta bata da k'yar ta tashi ta kurbi maganin, daga nan ta koma ta kwanta barci mai nauyi ya d'auke ta.

*Bayan Kwana Biyu*

Suzana ce zaune d'akin Sufah, tazo dubata da jiki, tayi matuk'ar tausaya ma Sufah don tanajin jiki Suzana tace"Hammi wai baza ka kaita Hospital ba jikin ta yayi zafi sose"Ammi tace"to ta yaya zamu kaita kawai y'an jik'e jik'en mu na gida ya wadatar da ita" insha Allah zata samu sauk'i,"Suzana tashi tayi ta ce wa Ammi tana zuwa ta fice da saurin ta.

Sashin ma'aikata ta nufa da saurin ta d'akin Emanuel ta fad'a yana kwance suka gaisa sannan ta rok'e sa da ya zo ya duba Friend d'in ta da magiya ya yadda don shima tsoro yake ji kada Hajiya ta gan su amatsayin shi na likitan hajiyar kawai ya d'auki akwatin sa da dabara suka je sashin su Sufah ya duddu bata ya Daura mata Karin ruwa sannan ya yi mata allurai yace limoniya ke damun ta sai zazzabi ta guji yin wanka da ruwan sanyi ko yawan sha ko zama gun dake da sanyi sosai magunguna ya bata sannan sukai ma Ammi sallama suka fice tare da Suzana,Ammi sai godiya take masu da shi masu albar.

Kuyi hak'uri da wannan.

*GYARA DA SHAWARWARIN KU INA LALE MARHABUN DASU, KADA KU BARNI DA IYAWA TA.*

_vote_
_Share_
_Comment_
_And Follow_

*Muna Mugun Tare*🤝

*Taku Har Kullum*👱🏼‍♀

*Star Nucee36O*✨💫

ITA WACE CE? (Complete Book1)Where stories live. Discover now