*🍡🍡🍡NAFI K'ARFIN SHI🍡🍡🍡*
*NA MRS SADEEQ✍🏻*
*ummu Meenal*
*🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟*
*G.W.F*
*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we the best among*
Https://www.facebook.com
*wannan shafin nakune 'yan gorgeous writer's forum nabakushi kyauta ko kuma ince daman nakune kuyi yanda kukaga dama dashi 😍 fatana Allah yabar 'kauna A tsakaninmu kuma Allah ya ninnika mana basira✍🏻*
*Nafi k'arfin shi fans, kuna goyon bayan khady Dan kunga tanada kyau ko ? To babu ruwa na saina haďaku da ashraf😍*
*masoyan wannan littafin gashinan read more 10 nayi maku😂*
*DEDICATED TO*
*AUNTY MAIMOUNATH O.G**Page 6-10*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Haka Ashraf ya kwana yana mafarkin khady iri-iri, saida asuba ya tashi yayi alwala yaje masjid yayi nafilanshi daga baya sukayi sallah asuba,
Mafi yawan addu'ar shi itace idan aurensu da khady alkhairi ne Allah ya tabbatar,
Ita kuma tana tashi bayan tayi sallar asuba ta shirya cikin atamfa tayi kyau abunta idan kaganta kamar ka sace ta ka gudu,
Bayan Sun gama break bada jimawa ba saiga k'awar ta nana ta shigo saboda idan zasuje skull ita take biyo mata saisu wuce skull,
Bata b'ata lokaci ba saboda daman ta shirya, ďakin baba ta shiga ta sameshi zaune kan dadduma da alama sallah walha yayi, duk'awa tayi ta gaishe shi,
Amsa mata yayi cikin fara'a ya kalleta yace," uwa ta har zaku fita makaranta ne?",
" Eh baba "," to daman inason zan faďa maki wata magana,"
Shiru yayi kamar mai tunani sannan yaci gaba da cewa, " daman akan maganar yaron nan ne ashraf, "Gabanta taji ya faďi Amma ta daure taci gaba da sauraron shi,
" ashraf dai jiya yazo ya sameni da kanshi akan maganar auren ku, yace yana neman alfarma a dawo da auren ku kusa kamar wata ďaya haka ko wata biyu,"
Saurin kallon baba tayi zuciyar ta tana suya nan take hawaye suka cicciko mata cikin muryan kuka tace," baba karatu fa nakeyi kuma had nakai level 2 ",
Baba yayi murmushin manya yace, " to ke uwata in banda abunki auren ai shi yafi zaman maki alkhairi kinga bayan auren idan ya yarda sai ki cigaba da karatun ai abu ne mai sauk'I",
Banida bakin magana domin bazan iya ja da maganar baba ba, Amma cikin zuciya ta kamar an zubamun garwashi anan take tsanar ashraf ta k'ara shiga ta,
Wato yana son ya rabani da freands ďina kuma yanason ya rabani da makaranta ta, shin wai da yake son ayi auren mu kusa uwar me ya tanada wallahi zaiga rashin mutunci na,
Da haka nagama sak'e sak'e çikin raina A zuciyata ina tunanin rashin Mutuncin da zanyima ashraf bayan auren mu,
Fitowa nayi Naga har yanzu k'awata tana nan tana jirana A raina nace Allah sarki k'awar arzik'i ,
Ina zuwa wajen ta cikin ýan sakonni ta gane akwai damuwa tareda ni,
Nana kallo na tayi itama ta nuna Tata damuwar A fili tace, " wai khady meyake damunki Naga daga shiga ďakin baba kin fito da damuwa meyake damunki?",
Hawayen da suke mak'ale cikin idanuwa na ne suka fito kamar an kunna fanfo,
K'awa ta nana hankalinta ya k'ara tashi anan take itama ta fara nata hawayen tana tambaya ta meyake faruwa?,
Cikin kuka nabawa nana labarin abunda baba yace mun na tsakanina da auren ashraf bazai wuce wata biyu ko ďaya ba ,
Gaban nana ne ya faďi dataji abunda khady tace mata , Anan take itama tafara kuka wiwi wai a cewar ta ashraf ya cuci khady,
Ni kuma danaga tana kuka nima na k'ara fashewa Danawa kukan,
Nana ce ta tsaida nata kukan tana cewa, " lallai ashraf ya cuceki daman so yake ya wargaza maki rayuwa, abunda nakeso dake yanzu muje wajen shi kici mashi mutunci son ranki mayb yayi zuciya ya faďa auren naki",
Sosai nayarda da shawarar ta haka mukaje inda nasan yake zama Amma Bamu sameshi ba, Ana muka tambayi wani ko yasan inda ashraf yake sai yace mana yanzu yaga ya shiga cikin gidansu,
Juyowa nayi na kalli nana nace tunda ya shiga gidansu bai kamata mu shiga cikin gidansu ba saboda mutanen gidansu sunada kirki ,
Nana tayi saurin cewa, " albishirinki ai mutanen gidan basu nan ai kinsan Aysha ta haihu Sun tafi suna Babansu kuma yana shinkafi yara kuma sunje makaranta Dan haka shi kaďai ne gidan",
Hakan danaji nana tace sai nace, " Eh haka ne to muje kirakani ",
Fir nana tak'I zuwa ta rakani incima ashraf mutunci ,sai cewa tayi ai ni kaďai yakamata in tafi saboda idan yaganta zaice ita take zugani,Nayarda da maganar ta saboda daman nasan ashraf ya tsani nana ďan haka nayi saurin shiga cikin gidansu,
Ko sallama banyi ba na shiga dayake daman gidan ba bak'o na bane nasan ko'ina Dan haka na shiga ďakin shi batareda fargaba ba, kasancewar bantab'a ganin namiji haka ba,
Kamar zan juya in koma waje sai wata zuciyar tace karki fita kifaďa mashi abunda kikazo ki faďa mashi,
Tsaye nayi a k'okar ďakin anan nafara cewa," nazo ne domin in faďa maka ka gaggauta janye maganar auren dayake tsakanina dakai,"
Kallo na yatsaya yanayi ni kuma naci gaba da cewa, " sak'onka ya iso gareni na cewa kanason ayi auren da wuri to wai kai inbanda k'ururbuciya datake damunka katanadi kayan auren nawa da har zakace ayi Auren da wuri?",
Ban k'arasa maganar ba naji ya damk'I hannu na ya Jawoni na k'arasa shiga ďakin anan take ya haďa jikina da nashi, ni kuma tsoro ya kamani you tsiwata tajamun,
(Ina ýan mata masu zuwa ďakin samari to idan dai har kinason kanki da mutunci to karki kuskura kije ďakin saurayi kidaina ganin saurayinki ba ďan iska bane komai malantar shi karki kuskura kije saboda idan an keb 'e tsakanin namiji da mace to na ukun su shaiďan ne,)
Jikina ne yarink'a rawa kamar mazari tsoro duk yagama kamani, gashi ni kuma girman kaina bazai barni in bashi haquri ba,
Ganin nayi ya k'ara matseni jikinshi har rawa yakeyi yana neman yakai hannunshi cikin breast ďina anan na k'ara firgita na fara rik'e hannunshi iya k'arfina ina cewa kasakeni ni ba ýar iska bace,
Muryanshi kamar ďan maye yace, "yau zan nuna maki cewa bakifi k'arfina ba kuma banida k'urciya",
Hankalina ya k'ara tashi lokacin da naji abar tafiya tana gugan Mara na kuma najita A tsaye abar da ko A novel ban tab'a jin an misalta ta ba,
Kuka nakeyi sosai ina bashi haquri ina cewa wallahi kafi k'arfi na kayi haquri nima nana ce taturoni tace inzo inyi maka rashin Mutunci",
Daman ashraf yasan za'ayi haka yasan duk abunda khady takeyi harda zugin nana Amma yasama ranshi sai yayi maganin khady ďin Dan harda laifin ta ita da take yarda da abunda zatace mata,
Da k'yar ashraf yayi control ďin kanshi ya k'yale khady amma ba kaďan yakejin sha'awar ta ba dan har wata zuciyar tace kawai ya aikata yayi sex da ita,
Da yake ba mutumen banza bane sai bai biye ma zuciyar shi ba ya saketa ,
Ni kam yana sakina na kwasa da gudu ko hijabina ban tsaya ďauka ba nayi saurin barin gidan daman k'awata na waje anan na sameta,......
*Ummu meenal ce ✍🏻*