*🍡🍡🍡NAFI K'ARFIN SHI🍡🍡🍡*
*NA MRS SADEEQ✍🏻*
*ummu Meenal*
*🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟*
*G.W.F*
*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we the best among*
*DEDICATED*
*ANTY MAIMOUNATH O. G**Page 11-15*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Ni kam yana Sakina na kwasa da gudu ko hijabina ban tsaya ďauka ba nayi saurin barin gidan daman k'awa ta tana tana jira na,
Ganin tayi nafito a hargitse hankali na baya jiki na duk na daburce cikin sauri take tambaya ta lafiya,
Magana ta tana rawa nace" Dan Allah kiyi sauri kishiga ki ďauko mun hijabi na yana ďakin shi ashe ďan iska ne ban sani ba",
Gaban nana ya faďi tayi saurin tambayar khady meya yimata?
Anan na kwashe duk yanda mukayi da ashraf na faďa mata daga qarshe nace bazan qara zuwa gidan su ba daman me kika turo no,
Wani irin kishi ne ya mamaye zuciyar nana jin cewa harda rungumeta yayi, Anan take taji zuciyar ta kamar garwashi sai taji dama itace yakema wannan son,
Kallo na tayi tace" kitsaya anan bara naje na ďauko maki hijabin ",
Kai kawai na gyaďa mata , ita kuma nana tayi saurin shiga gidan kai tsaye ďakin ashraf ta shiga ta sameshi har yasa jallabiya yana zaune yana jujjuya hijabin khady yanajin qamshin hijabin kamar khady ce gabanshi lumshe idonshi yayi ya rungume hijabin,
Sallamar nana yaji ya juyo yana kallon ta,
Nana shiga ďakin tayi tana mai addu'ar Allah yasa itama ya rungume ta,Cikin kisisina take tafiya harta kai gabanshi tana yanga, jitake kamar ta rungume shi Amma kuma bataga fuskar yin hakan ba,
Cikin in in nah tace " wai khady tace kabata hijabin ta",
Wani irin kallo ya watsa mata mai cike da harara da tsana yace " inason daman inyi maki kashedi akan matata, nasan duk abunda takeyi ke kike zugata to nayanke qawance ku ",
Kallonshi tayi kamar zatayi kuka jin ya kira khady a matsayin matar shi, ita A zaton ta itama zai rungumeta kamar yanda ya rungume khady Amma sai taga ita kallon tsana yake mata ,
Batace mashi komai ba saboda tana ganin qwarjinishi Dan ji takeyi inama ace ita yakema wannan son da yakema khady,
Ashraf yace" kice tazo ta anshi hijabin da kanta",
Ranta ne ya qara b'aci ganin ko kulata baiyi ba cikin rashin qarfin jiki ta juya harta kai qofar fita sai ashraf ya kirata,
Sanin khady yayi bazata qara shigowa ba dan haka ya wurga mata hijabin batareda yayi magana ba,
ďaukar hijabin tayi ta fita cikin ďakin , kamar tayi kuka haka tabar gidan ta iske khady daga can gefe gaba da gidan kaďan,
Khady tana ganin ta tayi sauri zuwa wajen ta tace " yauwa na gode maki da kika ansomun hijabi na gurin wannan ďan iskan ni yau aiya firgita ni",
Nana tace "ai kece kike mashi abu kamar kina tsoron shi ni wallahi da nice ke idan nayi mashi wani abun sai yace ya fasa auren ",
"Mezan mashi ? Kinsan shi da naci irin wulaqancin da nake mashi da yanada zuciya ai da yanzu ya fasa aurena",
Nana tace "ai yau zaizo ko ?"
"Mayb",
"To idan yazo ki qara shuka mashi rashin M muagani zaiyi zuciya koko bazaiyi ba",Khady tace "ke mudaiyi sauri muje skull gashi har munyi late "
Haka suka kama hanyar zuwa skull nana tana ta bata shawara akan yanda zatayi idan ashraf yaxo anjima,"
Shi kam ashraf yau yayi abunda bai tab'a yi ba wato rungumar ýa mace wadda ba muharramar shi ba, tun lokacin da abun ya shiga tsakaninsu yaji ya qara son khady,
Ji yake da yanada hali da next week za'ayi bikin a kawo mashi khady ďinshi Dan Shi dai yanada buqatar ta a kusa dashi,
Da haka yayi ta tunani inda tunaninshi ya tsaya akan cewa anjima zaije ya samu matar yaya daman wajen ta yake Tara kayan lefen shi to zaije yaga abunda A babu saiya siyo,
Duk wanda yake zaune A zamfara yasan cewa kafin Asa ranar aure to sai an fara kawo lefe sannan Asa ranar aure, to Dan haka yau ashraf ya qosa yakai lefe asa mashi ranar aure kusa,
A skull kuwa khady takasa sakin jikinta babu abunda take tunani sai abunda ya faru ďazu tsakaninta da ashraf, idan ta tuna sai taji kamar tayi kuka A cewar ta ashraf ya cuce ta tunda harya tab'a bress ďinta,
Da wannan tunanin ne suka tashi zuwa gida Amma duk da haka khady takasa sakin jikinta sai nana ce take bata haquri tana cewa yau kiyi maganin ďan iska,
Misalin qarfe takwas na dare ashraf ya kira khady A waya cewa yana falon baqi inda suka Saba zama kenan,
Daman kiranshi take jira saboda tanason yau tayi mashi rashin M Dan haka bata b'ata lokaci ba ta iskeshi ďakin baqi zaune ,
Tana shiga gabanta ya faďi saboda ta tuna ďazu kenan , ji tayi kamar zai maimaita abun ďazu Dan haka ta tsaya ďan nesa dashi kuma saita kasa cewa komai,
Ashraf yana ganin ta sai yaji ta qara shiga zuciyar shi yanajin kamar ya sace ya gudu Dan haka yayi saurin gaishe ta,
Ko kallonshi batayi ba balle ta ansa mashi, hakan yabashi damar cigaba da cewa,
"Insha Allah jibi inason A kawo lefen nan kinga sai asa rana ayi auren a huta,
Saurin kallonshi tayi Dan tasan gidansu shi kaďai ake jira ga maganar da babanta ya faďa mata ďazu, cikin tsiwa da nuna isa tace
"Kana nufin harka Tara kayan lefen nawa ko kuma cika baki ne da gaggawa irin taka",
"Eh to idan ankawo zaki gani koma menene zaki gane",
Jin tayi kamar ta ďauke shi da Mari ganin ya fara raina mata wayo anace kawai mai gaggawar tsiya ,
Cikin fushi tace "wallahi bakada abunda zaka aure ni dashi komai yawanshi saboda nafi qarfin ka kuma inason kasawa ranka cewa nafi qarfin ka marar zuciya kawai",
Kalamanta ba qaramin b'ata mashi rai sukayi ba baice mata komai ba ita kuma taci gaba da cewa " wallahi nafi qarfin ka kuma banason lefen ka riqe tsummanka ni kaga tafiya ta",
Tana kaiwa nan ta juya tayi shigewar ta cikin gida,
Anan tabarshi ranshi a b'ace zuciyarshi kamar garwashin wuta , A haka ya daddafa yakai gidansu kasancewar babu nisa tsakaninsu,
Yana shiga gidansu ďakin matar yaya ya shiga dan yaji me yakamata a qara cikin lefen...........
*kuyi haquri da wannan banida lafiya ne*
*taku Ummu meenal ce ✍🏻*