*🍡🍡🍡NAFI K'ARFIN SHI🍡🍡🍡*
*NA MRS SADEEQ✍🏻*
*ummu Meenal*
*🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟*
*G.W.F*
*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we the best among*
*DEDICATED TO*
*ANTY MAIMOUNATH O.G**masoyana ina ganin saqonku harda masu kirana suna yimun fatan alkhairi duk ina godiya kuma nima ina yinku irin sosai ďin nan😍😘*
*Page 16-20*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
A zaune ya same ta tagama lallaba Abdullah yayi barci, akan 1sitar ya zauna fuskar shi A ďaure,
Kallonshi tayi tace " yanaga kamar ranka A b'ace meyake faruwa?",
"Matar yaya kema kinsan in raina ya baci kinsan daga gidansu khady nake"'Matar yaya ta kalleshi cikin tausayawa tace " Allah ya nuna maka ka aure ta kahuta da baqin cikin da take saka",
"Ai an kusa yanzu ma zuwa nayi kifaďam mun abubuwan da suka rage wanda ba'a siya ba gobe insha Allah zan siyo Dan munyi magana da mama jibi zasu kai lefen",
Matar yaya tace " wallahi ashraf kayi qoqari sosai A lefen nan abu uku suka rage wanda ba'a siya ba, daga pant sai braziya da fauda, itama braziya yayanka yabada kuďi a siyo to abunda yasa ban siyo ba saboda bansan side ďin ta ba Amma yanzu abunda za'ayi kakira ta saita faďa maka side ďin ta gobe sai A siyo",
Yaji daďi har cikin ranshi dayaji cewa yayi qoqari kuma bra kaďai ta rage Dan haka ya tashi yace " to bara inkirata duk yanda mukayi da ita zan faďa maki"
Bai jira abunda zatace ba yayi saurin barin ďakin ya shiga ďakin shi ya ďauko waya ya kira khady wanda ya rubuta my lvly wife,
A nata b'angaren tanaji wayar ta tana ringing Amma sanin shine yasa bata ďauka ba saida taji ya dame ta da waya sannan ta ďauka cikin tsiwa tace
"Wai lafiya kadameni da kira sai kace maye? "
"Lafiya Lau khady daman nakira ne inji side ďin breziyar ki da pant",Abun haushi ya bata da mamaki cikin ranta tace ko ya haukace, Amma a fili sai tace " wallahi bazan tab'a faďa maka side ďin breziya taba to waima idan nafaďa maka me zakayi? WALLAHI nafi qarfin infaďa maka side ďin breziya ta",
Maganar shi tayi masifar b'ata mashi rai Dan haka shima yace " laa khady kiyi haquri Dana tambayeki side ďin breziyar ki, ai na manta ďazu na tab'a kuma zan iya bada side ďin breziyar ki",
Ba qaramin haushin maganar shi taji ba , tarasa mezatayi Dan ya riga ya gama da ita kawai saita sa mashi kuka A waya,
Jin kukan tane sai yaji bai kamata ya faďa mata haka ba amma ai laifin ta ne, cikin rarrashi yace
"Haba khady daga na faďa maki haka saiki fara kuka to kiyi shiru wasa nake maki bazan tantance komai ba akan abunda ya faru ďazu kuma ina roqonki daki yafemun",
Cikin kuka tace "ni ka qyale ni kacuce ni bazan yafe maka ba", sai tayi saurin kashe wayar,
Ashraf kallon wayar yarinqayi yana tunani kala kala daga qarshe dai yaja bargonshi ya kwanta, asuba ta gari,
WASHE gari A gidansu khady sai shirye shiryen tarbar lefe sukeyi Sunyi abubuwa kala kala suna jiran masu kayan lefe,
A gidansu ashraf kuwa sunyi qoqari Dan set ďaya ashraf ya haďa akwai shidda kenan harda babko, atamfa kala goma sha biyar sai less kala takwas dogayen riguna kala kala biyar sai tarkace ,
Qarfe biyar na yamma ýan gidansu ashraf suka kawo lefe gidansu khady,
A gaskiya sunga tarba sosai kuma Sun anshi lefen lefen hannu bibbiyu kowa sai murna yake da fatar Allah ya nuna mana ranar aurensu,
ýan Ganin lefe duk wanda ya gani sai yasa albarka da fatar Allah yasa albarka,
Saida kowa ya watse sannan khady ta shigo gidan tareda nana daman bata gidan,
Kai tsaye ďakin da aka ajiye lefen suka shiga nana tana ganin lefen gabanta ya faďi Dan a zuciyar ta batayi tunanin lefen zai kai yawan haka ba,
Ita kuma khady lokacin da taga lefen a zuciyar ta itama tayi mamaki Dan itama bata zaci lefen yakai yawan haka ba, Amma A fili kuwa saita tab'e baki tayi kwanciyar ta kan doguwar kujera,
Nana ce ta bubbuďe komai sannan ta juyo tacema " A gaskiya wannan lefen ba kalarki bane kefa matar manya ce yakamata ace gidan Hutu zakije, kai ni nasan ashraf yasha baqar wahala sannan ya haďa kayan nan",
Tab'e baki tayi tana mamakin marar zuciya irin ashraf,
Nana ce ta katse ta da cewa " nasan yanzu idan kukayi aure ashraf zai rabani dake",Da sauri ta yunquro cikin fushi tace " wallahi ashraf bai isa ya rabani dake ba Waye shi ai bai isa ba kuma Kibari kigani",
Cikin zuciyar nana haushi ne fal A ranta haushin khady takeji sosai kuma A ranta tayi qudirin saita rabata da ashraf daga qarshe kuma ta aure shi tanaji tana gani,
Kwana biyu da kawo lefen khady akasa ranar aurensu da ashraf nan da sati uku masu zuwa kowa sai fatan yake Allah ya nuna mana ranar,
Ashraf kuwa murna sosai yakeji dan harya qosa ranar tazo daman harya buga invitation sannan ya kama gida A damb'a quarters babu laifi gidan yanada kyau,
Ita kam khady bata tabbatar da auren ta da ashraf ba sai wannan karon dataga ýan gidansu sunje duban ďaki kowa saisa albarka akeyi,
Yanzu haka an hana khady fita ko'ina daman suna hutun skull,
Mai gyaran mata aka ďauko musamman Dan ta gyara khady, ita kuma khady har a ranta batason wannan gyaran auren ma baso takeyi ba balle was gyaran jiki kuma wai Dan ashraf yagani,
Hankalin ta bai qara tashi ba saida taga an haďa mata tsumi ance daga yanzu shine ruwan shan ta, Sannan an haďa mata kazar amare kuma an tilasta ta dole saitaci,
Haka khady take din kazar tana kuka tana yima ashraf Allah ya isa A cewar ta shiyaja mata,
Haka kuma idan tace zata sha ruwa sai abata ruwan tsumi ace su zatasha ,babu yanda zatayi haka takesha,
Yanzu idan kaga khady sai kayi daqyar ka ganeta saboda wani irin kyau taqara daman ga dilka anayi mata kuma an hanata fita kullum tana ďaki tana aikin kuka,
A b'angaren ashraf kuwa abokananshi daga wani gari duk sunzo A hotel suka sauka , ashraf kuwa duk wanda yayanshi yasan yana cikin murna ,
Sai dai ya daďe baiga khady ba kuma idan ya kirata A waya bata ďauka,...............
*Ummu meenal ce ✍🏻*