*🍡🍡🍡NAFI K'ARFIN SHI🍡🍡🍡*
*NA MRS SADEEQ✍🏻*
*ummu Meenal*
*🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟*
*G.W.F*
*Home of gorgeous, intelligent and expert writers we the best among*
https://www.Facebook.com
*DEDICATED*
*ANTY MAIMUNATH O. G**Anty mamee 🧕🏻ustaziyya ko 'yar duniya🤷♀ writer ina farin cikin dawowar ki akan cigaba da yimana typing, gaba dai gaba Anty mamee, kinayi munajin daďi kina bari muna jin haushi*
*Sis Rukyn mama ramin mugunta writer ,Abunda kika yimun ban isa na Maida maki makamancin shi ba, lallai ke haske ce A gare ni, kina 'ko'karin fahimtar dani abunda ban fahimta ba Alkhairin da kika yimun bazai bayyanu ba dan zai cinye page ďin duka 🤝🏻*
*Ko na'ki kona so dole inyi maku typing Masoya na A duk inda suke ina Alfahari dasu Allah yabarmu tare 🤝🏻*
*Wannan page ďin nakune ma'kiya na A duk inda suke toga page nabaku shi kyauta kuyi yanda kukaga dama dashi 🤣, ina Alfahari daku ma'kiya na Ana mugun tare🤝🏻*
*page 66-70*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
" Budurwa tace kuma ita nake in aura nan bada daďewa ba ",
Nan take khady ta hasala wani 'kololon ba'kin ciki ya tsaya mata a wuya ko miyau takasa haďuwa,
Da sauri ta 'karasa gabanshi hankalinta A tashe ta cakumi wuyan rigararshi tana kuka tace " Ashraf daman kasan da cewa nana tana Sonka shine baka faďamun ba ? To wallahi daga kai har ita Baku isa ba " ta'karasa maganar tana matsanancin kuka,
Ashraf yace" ban gane bamu isa ba, ke har kin isa ki hanani auren nana , to bara kiji ko kinaso ko bakiso saina aure ta saboda ita take sona , kefa kikace kinfi 'karfi na ",
Khady cikin kuka tace " wallahi baka isa ba bazaka aure nana ba indai har ina raye, nana Ashe daman macuciya ce ban sani ba , shine kai kuma kabata haďin kai dan kuci amana ta ",
Ashraf yayi dariya ya 'Kwace jikinshi ya nuna ta da ďan yatsa (manuni) yace " khady baki sona , yakamata Kibari in aure wacce take sona ", ya faďa yana fita daga ďakin,
Saida ya kusa fita bedroom ďin sannan ya juyo yace " Ni kinga yanzu ma wajen fira( taďi ) zanje "
Khady jin tayi idanunta Sun rufe batasan lokacin da tayi saurin shiga gabanshi tasama 'kofa key ba,
Kallonshi tayi tana hawaye tace" Ashraf Ashe daman ba sona kakeyi ba ? Yanzu har zaka iya cin Amana ta kenan? Ban ta6a tunanin hakan daga gareka ba ",
Tabashi tausayi sai yaji kamar ya rungume ta ya lallashi ta,
Baice mata komai ba ya juya zuwa cikin bedroom ďin,
Kan gado ya kwanta fuskar shi tana kallon P.O.P yana tunanin Ashe daman Khady tana sonshi shine take mashi yawo da hankali, to shima saiya nuna mata ya fita rainin hankali,Khady tana ganin ya shiga bedroom itama tabishi bayan ta cire key ďin ta 6oye ,
Ganin Ashraf kwance kan gado da alama yana tunani hakan ya bata damar zuwa inda yake sai taga kamar baimasan tazo ba,
Kan jikinshi ta hau tana kuka fuskar shi tana kallon nata fuskar ,
Shikam Ashraf gaba ďaya ya ruďe jin khady A jikinshi hankalinshi ba 'karamin tashi yayi ba,Yaso ya 6an6are khady daga jikinshi Amma bazai iya ba,
Hannunwan shi yasa A bayanta ya 'kara rungeme ta tsammm kamar wani zai 'Kwace mashi ita,