Akwai wani abu page 1.

2.1K 76 6
                                    

💖AKWAI WANI ABU💖





By Sawwama A.





Page 1.





_Bismillahi rahmanir rahim_



Sak'ale yake da bag pack a kafad'arsa ta dama yayin da yake janye da trolley da d'ayan hannu.

Saukarsa kenan daga cikin cab din da ya d'aukosa d'aga kai yayi yana kallon katafaren gidan da yayi yarintarsa a ciki.

K'wank'wasa kofar gate d'in gidan yayi,daga ciki yaji muryan baba sule me gadin da ya kwashi shekaru yana gadin gidan "wanene wannan?" Ya tambaya daga ciki.

Murmushi yayi yace "baba sule nine *Sharafudden*" kit kat yaji an zare sakatan karamin gate din lokaci daya kuma aka wangale k'ofar.

"La'ila ha'illallahu sharafu kaine yau a k'asar,na shiga uku ji yanda ka yi wani irin girma,halan me ake baka a can turan kakr ci ka dawo kaman shanun gona?"

Dariya sharafudden yayi yace "kai baba sule ai ka bani hanya in wuce ai kafin muyi hiran,hala yau y'an hiran naka basu zo bane kana neman d'an tay?"

Bashi hanya baba sule yayi yana cewa "uhmmm kayya yaro kayyah da ne kakr ganin gidan nan da 'yan hira amma yanzu komi ya canza."

Dariya sharafudden yayi yana jin nishad'i yau gashi a gida janye trolley din shi daga hannun baba sule da yake kokarin amsa,gidan yake karewa kallo wanda baya rabuwa da ma'aikata suna hada hadarsu a tsakar gidan amma yau wayam sosai abin ya bashi mamaki.

Babban kofar glass din da zai sadaka da  babban palon gidan ya nufa door bell ya danna ba tare da b'ata lokaci ba iya babbar ma'aikaciyar gidan ta bud'e.

"Iyata!" Ya furta fuskarsa dauke da fad'ddan murmushi kallonshi tayi tana kokarin tuno fuskar zaro ido tayi lokacin da kwakwalwanta ta gane wanda yake tsaye a gabanta "ya subahanallah! Sharafu kaine ko kuwa idona ne ko me kama da kaine?" Dariya yayi ya rik'o hannunta yace "Ni d'in ne dai Iya."

Shiga cikin palon yayi idanunsa na k'arewa palon kallo gidan nayi mishi kaman ba gidan da ya girma a ciki ba wannan gidan is looking dull anya? *akwai wani abu* something is definitely wrong yana shirin bud'e baki yayi magana ya jiyo masifan Hajiya

"Ladi so nawa zance miki bani so bani so ko kad'an ayi abinci kasa da uku a gidan nan iyyeh,ba ana biyanki kudin salary dan ki dinga bijirewa dokokina bane?"

Mamakine ya kashe  sharafudden hajiya ke kiran iyah ladi da sunanta gatsau me ke faru haka sannan tana yi mata ihu treating her like the maid she is.

Tana shirin bud'e baki ta kuma wani rashin mutunci idonta ya hasko mata sharafudden baki ta bud'e ta fara dibi dibi amma kalma daya ya kasa fitowa, sai kallon kallo da suke yiwa juna shi da ita..........



*akwai wani abu! Akwai wani abu! Akwai wani abu...... Kar Ku sake a baku labari ku kara biyo ni a cikin wannan littafin dan warware kullin dake cikin wannan labari*

*Labarine da yazo da sabon salo me cike da rikitarwa domin kuwa _akwai wani abu_ zaku samu labarin a sawwama paid group a #200 kacal ta hanyar transfer a wannan  acct number 4913066710 Hafsat Abbas Gambo Ecobank or contact me ta wannan layin 09032871327.


_Thank you_

AKWAI WANI ABUWhere stories live. Discover now