💖AKWAI WANI ABU💖
By Sawwama A.
Page 2.
Kallom kallo suka yi lokaci d'aya kaman wacce ta tuno wani abu ta zabura ta nufoshi da sauri "oyoyo d'ana oyoyo zuwa ba sanarwa?" Tace tare da rik'o hannunshi kaman wacce take kokonton yanda zata tareshi.
Shi kuma ganin haka yasashi zagaye dogayen hannayensa a jikinta tare da fad'in "oyoyo hajiyata uwar maraya,ai naga yanzu kin daina yayina ne ba kya ji dani tunda kika samu 'yan samari a gidan nan."Dariyan da yafi kama da na yak'e tayi tace "wacce ni da mantawa da kai 'yan kannenka ai sai dai su lakato son da nake yi maka." Ta fad'a tana zare jikinta daga runguman da tayi mishi
"Well yanzu ka samu kaje ka huta ka cire gajiya sai ka shigo ayi dinner,ummm iya dan Allah a gyara d'akinshi a kuma kara girka wani abu na saukan babban dan gidan nan ko ba haka ba?" Ta fad'a tana b'abb'aka dariya.
Ajiyar zuciya ya sauke ganin ta koma hajiyarsa da ya sani.
Iya ma ajiyar zuciya ta sauke yanzu al'amarin hajiyan ya daina ba ta mamaki da al'ajabi domin kuwa hajiyar ta koma kaman hawainiya yau she is her normal self gobe kuma ta rikid'e.
Komawa bakin aikinta Iya tayi yayin da sharafudden da hajiya suka tafi d'aya k'aramin palon gidan.
"Ina alhaji yake ne? Banji motsinshi ba." Sharafudden ya tambayeta yayin da yake relaxing akan couch
"Alhaji ya fita zuwa gidan senator" ta fad'a tana gyara agogon gold dake d'aure a hannunta kallonta sharaffuden yayi yana mamakin yaushe ta koma sa flashy abu haka well ten years ia not like ten days.
"Sauran yaran gidan fa? I dunno my lil ones anki kawo min su...."
"Ko kai kaki zuwa ka duba mu ba, u only know them a hoto haba!"
Murmushi yayi yana kallon expression dinta yanda take nuna b'acin ranshi na kin zuwanshi na tsawon shekaru 10.Within few minutes iya ta dawo ta sanar musu an gyara part d'in sharafudden tashi yayi yana stretching yayin da y'ar budurwa da tazo tare da iya taja trolley dunshi shi kuma ya d'auki bag park d'inshi.
Hajiya ma mik'ewa tayi tace "da fita zan yi amma bari in bar fitan zuwa gobe tunda d'ana ya dawo.
Murmushi yayi mata yabi bayan yarinyan da ta d'au kayanshi zuwa part d'inshi dan bai sanKo akwai wani sauyi ba ga mamakinsa d'akinsa na tun tafiyan shi,shine dai dakinsa a halin yanzu.
Tura hannayensa yayi cikin aljuhun wandonsa na baya yana k'arewa d'akin kallo memories d'in yarintansa na dawo mishi bango guda na d'akin yake kallo wanda yake d'auke da hotunansa tun daga first birthday d'in da aka yi mishi zuwa graduation d'inshi daga primary school da na secondary sch,sai na lokutan da yake bachelor degree d'in shi a Malaysia dana graduation dinshi zuwa awards din da ya karb'a har zuwan shi US aviation dinshi wasu kuma yana tuk'a jirgi gasu nan dai barkatai kaman wani studio.
Ajiyan zuciya ya sauke he cant thank his parent enough sun yi mishi komi ya sani ba ko wani d'ane ya samu gatan da ya samu ba.
D'auke d'an k'wallan da ya taru mishi a ido yayi sannan ya wuce bathroom d'inshi komi fes kaman an san da zuwanshi.
Wanka yayi tare da d'auro alawla dan rama sallolin dake kanshi kammalawansa yayi dai dai da kiran sallahn magrib da aka yi hakan ya sashi mik'ewa dan zuwa masjid saboda k'wad'ayin ladan jam'i duk kuwa da irin gajiyan da yake tattare dashi.
Fitowanshi yayi dai dai da fitowan alhaji da sauri ya k'arasa wajenshi yana shirin durk'usawa ya gaisheshi alhajin ya taroshi tare da rungumeshi bakin nan har kunne "oyoyo my son is finally back,naji dadin dawowanka sosai,muje sallaah mu dawo."
Hannunsa kan kafad'anshi kaman wani abokinsa suka jera zuwa masjid din.
Sun dawo sun sami ilaharin iyalan gidan suna jiran dawowarsu a dining,wuri suka samu suka zauna yayin da yaran gidan kowa ya fara gaishe da sharafudden cike da murnan yau sun ga yayansu.
Fuskarsa d'auke da murmushi yake amsa gaisuwansu Al-ameen da Ahmad yayin da Ruqayya ta kasa magana sai murmushi take.
Kumatunta yaja yace "heyyyy emmatana an girma ba a iya gaisuwa ba" dariya tayi had'e da rufe fuskanta tace "kai yah duk murnan ganinka ne ya tafi min da magana,word can't express how happy i am kumaaa...."
"Ruqayyah! Manners! Ina d'abi'an cin abincinki yake zaki zauna kina zuba a wajen cin abinci kaman carbi ya tsinke?" Hajiya ta dakawa Ruqayya tsawa da sauri y'ar budurwan yarinyan ta gyara zama hade da sunkuyar da kanta tace "sorry mommy!" Tsaki alhaji yaja amma bai ce komi ba da alama abinda hajiyan tayi ya bata mishi rai.
Sakin baki sharafudden yayi yana kallon ikon Allah Ruqayya itace 'ya mafi soyuwa a wajen hajiyarsu then why the sudden change last he checked kowa yana magana a wajen amma Ruqayya na magana ta hayayyak'ota kan manners asalima ko abincin ba a serving ba balle akai ga ci.
Jikinsa ne yayi sanyi sai yana ganin kaman sabida shi tayi,she is protecting her daughter from him.........
_wai kam menene alak'an sharafudden da wannan zuriyan,i know is a lil bit twist buh i promise zaku fahimta a sannu ku biyoni a next page dan jin ya alakarsu take._
*zaku iya biyan kudin wannan littafin a wannan acct 4913066710 Hafsat Abbas Ecobank ko ku tuntubeni a wannan layin 09032871327
Sawwama Qawwama😘